'Ba a Sarki 2,' Tsohon Kwamishina Ya Fadi Dalilin Batawar Abba da Kwankwaso a Kano

'Ba a Sarki 2,' Tsohon Kwamishina Ya Fadi Dalilin Batawar Abba da Kwankwaso a Kano

  • Dr. Yusuf Bello Danbatta ya bayyana cewa sauya shekarar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC tarihi ne ya maimaita kansa
  • Ya ce kowane gwamna yana so ya samu cikakken ikon gudanar da mulkinsa domin ba a taba sarki biyu a gari daya a dukkan fadin duniya
  • Danbatta ya bayyana yadda ya hango batawar Abba da Kwankwaso tun da dadewa saboda tsarin samun gwamnan gudanarwa da na siyasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Tsohon kwamishinan tsare-tsaren tattalin arziki na Kano, Dr. Yusuf Bello Danbatta, ya yi fashin baƙi kan halin da siyasar jihar ke ciki.

Dr. Yusuf Danbatta wanda yana daga cikin wadanda suka assasa tafiyar Kwankwasiyya a Kano ya tabo batun batawar Gwamna Abba Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Sunan malami ya fito: An shawarci Kwankwaso kan 'yan takarar da za su kifar da Abba

Dr. Yusuf Bello Danbatta ya yi bayani na dalilin batawar Gwamna Abba Yusuf da Sanata Rabiu Kwankwaso.
Gwamna Abba Yusuf ya na yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bayani a wani taro. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

A wata tattaunawa ta musamman da jaridar The Sun, Danbatta ya bayyana cewa sauya shekarar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC ba ta zo masa a ba-zata ba.

A matsayinsa na tsohon jigon Kwankwasiyya, ya nuna cewa abin da ke faruwa a Kano yanzu ba baƙon abu ba ne, face tarihi da ke maimaita kansa.

Kano: Fadan gwamnoni da iyayen gidansu

Dr. Danbatta ya bayyana cewa wannan rikici tsakanin gwamna da wanda ya ba shi takara ya jima yana faruwa a dukkan jerin zaɓukan jihar Kano.

Ya fara da tuna wa duniya rigimar 1979 zuwa 1983, inda Malam Aminu Kano da Abubakar Rimi suka raba gari a lokacin mulkin Jamhuriyya ta biyu.

Haka kuma a 1999, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kansa ya raba gari da iyayen gidansa kamar su Musa Gwadabe da Abubakar Rimi kafin 2003.

Haka abin ya faru tsakanin Ibrahim Shekarau da jiga-jigan da suka kafa shi a 2003, irin su Sule Yahaya Hamma da Naja’atu Bala Muhammad.

Kara karanta wannan

Bayan Abba, Kwankwaso ya shiga tattaunawa da APC kan sauya sheka? Gaskiya ta fito

"Ko a shekarar 2011 ma, an samu saɓani tsakanin Shekarau da mataimakinsa Abdullahi T. Gwarzo saboda gwamnan ya zabi Mallam Sagir Takai a matsayin magajinsa. Wannan rigimar ce ta sake dawo da mu kan mulki, kuma Kwankwaso ya dawo ya yi wa'adinsa na biyu.
"Rikici mafi muni da aka gani shine tsakanin Kwankwaso da tsohon mataimakinsa Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya girgiza siyasar jihar kusan shekaru takwas."

- Dr. Yusuf Danbatta.

Falsafar "ba a sarki 2 a gari 1"

Babban dalilin da ya sa Abba Kabir Yusuf ya bar Kwankwaso a cewar Danbatta shine rashin yiwuwar samun shugabanni biyu a mulki.

Ya bayyana cewa kowane gwamna dake kan kujera yana da iko mai girma, wanda hakan ke sa ya zama wahala wani ya riƙa juya shi.

Dr. Danbatta ya ce ko da mutum ya naɗa ɗan cikinsa a matsayin gwamna, hikima ita ce ya yi ritaya ya bar shi ya yi mulkinsa.

A cewarsa, sarki idan ya yi murabus yana barin gari gaba ɗaya domin ya bai wa sabon sarki damar gudanar da mulki ba tare da tsoma baki ba.

Dr. Danbatta ya ce Abba ya koma APC ne domin samun cikakken iko na gudanar da mulkin Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: @KwankwasoRM, @Kyusufabba
Source: Twitter

Batawar Abba da Kwankwaso a Kano

Danbatta ya bayyana cewa ya jima da sanin cewa tabbas Gwamna Abba Kabir Yusuf zai raba gari da jagoran tafiyar Kwankwasiyya saboda matsin lamba.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado: Gwamna Abba ya bayyana wanda zai ci gaba da zama Sarkin Kano

Ya ce duk tsarin da ya samar da "gwamnan gudanarwa" da kuma "gwamnan siyasa" a lokaci guda, to lallai wannan tsarin ba zai taɓa dorewa ba.

Akwai iƙirarin cewa wasu na ƙoƙarin sarrafa gwamna daga waje, wanda Danbatta ya ce babban kuskure ne duba da girman ikon kujerar gwamna.

Yanzu da Gwamna Abba ya koma APC, Dr. Danbatta yana kallon hakan a matsayin yunƙurin gwamnan na tabbatar da ƴancin kansa a matsayin jagora.

Matar Ganduje ta aika sako ga Kwankwaso

A wani labari, mun ruwaito cewa, Farfesa Hafsat Ganduje, ta bukaci Rabiu Musa Kwankwaso ya ajiye rigingimun siyasa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Uwargidan tsohon gwamnan Kano ta ce Abba Kabir Yusuf ya shafe kusan shekaru 40 yana aiki karkashin Kwankwaso, don haka ya dace a amince da zabinsa.

Ta ce ya kamata Kwankwaso ya bar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gudanar da mulkinsa cikin kwanciyar hankali domin amfanin al’ummar jihar Kano baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com