Tarihin rayuwa da siyasar 'Jagoran Talakawa' Aminu Kano

Tarihin rayuwa da siyasar 'Jagoran Talakawa' Aminu Kano

A makon nan ne Malam Aminu Kano ya cika shekara 35 da barin Duniya. Da dama sai dai kurum sunan su ke ji don ba su san wanenen Malam Aminu Kano ba. Dalilin haka ne mu ka tsakuro kadan daga tarihin sa.

Malam Aminu Kano yayi fada da Mala’u da Sarakuna da kuma Turawan mulkin mallaka inda ya rika fafutukar karbowa Talakawa ‘yancin su. Ya rasu ne a 1983 a lokacin mulkin Shehu Shagari yana mai shekara 62 a Duniya.

Tarihin rayuwa da siyasar 'Jagoran Talakawa' Aminu Kano
Marigayi 'Jagoran Talakawa' watau Malam Aminu Kano

1. Kuruciya da karatu da karantarwa

An haifi Malam Aminu Kano ne a gidan Malamai a shekarar 1920. Ya kuma yi karatu a Kwalejin nan ta Katsina kafin ya tafi Landan karo ilmi. A wajen karatu ya hadu da irin su Firayim Minista (daga baya) Sir Abubakar Tafawa-Balewa. Bayan ya dawo ne ya fara karantarwa a Arewacin Najeriya.

KU KARANTA:

2. Siyasar Malam Aminu Kano

Da farko Malam Aminu Kano yana tare da Jam’iyyar NPC kafin ya balle da jama’ar sa zuwa NEPU. Malam da mutanen sa sun gamu da tsangwama daga manyan NPC a NEPU. A 1954 yayi takarar kujerar Majalisa ya sha kasa hannun Maitama Sule. Daga baya Aminu Kano samu zuwa Majalisar.

3. Mukaman da ya rike

Malam Aminu Kano yana cikin manya a Majalisa a shekarar 1959. Bayan an kifar da Gwamnatin su Sardauna kuma Malam ya rike Ministan lafiya na tsawon lokaci a Gwamnatin Sojan Gowon. A 1978 Aminu Kano yayi takarar Shugaban kasa amma Jam’iyyar sa ta PRP ba ta kai labari ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng