Takarar Gwamna: Lokuta 3 da Pantami Ya Fuskanci Sukar Jama'a bayan Shiga Siyasa
Gombe - Duk da cewa bai fito fili ya bayyana aniyarsa ba, masu sharhi kan siyasa na ganin cewa Sheikh Isa Ali Pantami yana zawarcin kujerar Gwamna Inuwa Yahaya.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A siyasar Najeriya, fitattun mutane sukan ɓoye kudurinsu na ɗan lokaci domin kauce wa harin abokan hamayya, su bar matasa su jagoranci yakin neman zaben ta karkashin kasa.

Source: Twitter
Wannan dabarar tana ba ɗan takara damar gina farin jini a tsakanin talakawa kafin ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta takara a hukumance, a cewar rahoton jaridar Premium Times.
Sai dai, fitaccen malamin Musuluncin, Sheikh Isa Pantami ya fuskanci sukar jama'a a baya, waɗanda ake ganin za su iya shafar yadda jama'a ke kallonsa a matsayin jagoran da zai riƙe jihar Gombe.
Wannan rahoton zai yi nazari kan lokuta uku da Pantami ya jawo ce-ce-ku-ce, kama daga takaddamar matsayin Farfesa, kalaman addini na baya, da kuma rigimar shiga siyasa a yanzu.
1. Takaddamar matsayin Farfesa a FUTO
A watan Satumba, 2021, Legit Hausa ta ruwaito cewa jami'ar FUTO dake Owerri ta sanar da karrama Pantami da matsayin Farfesa a fannin tsaron yanar gizo.
Wannan karramawar ta zo ne a lokacin da yake riƙe da muƙamin ministan sadarwa, wanda hakan ya janyo ayoyin tambaya kan sahihancin matsayin.
Ƙungiyar ASUU ta ƙasa ta yi watsi da wannan matsayi, tana mai bayyana shi a matsayin "haramtacce" kuma wanda ya saɓa wa ƙa'idodin jami'a.
ASUU ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa ba a bi ƙa'idojin da aka saba bi ba wajen naɗa Farfesa a tsarin Najeriya.
Shugaban ASUU na lokacin, Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa Pantami bai cancanta da matsayin ba duba da cewa ba malamin jami'a ba ne na dindindin.
Duk da haka, jami'ar FUTO ta ci gaba da kare kanta, tana mai cewa ta bi dukkan ƙa'idodin da suka dace wajen ba shi wannan muƙami.
Har ma ta kai ga cewa jami'ar da ke Owerri, jihar Imo ta fito ta ce ta maka ASUU a kotu bayan kungiyar ta yi barazanar sanya mata takunkumi kan ba Pantami matsayin Farfesa.
Wannan takaddama ta bar tabo a tarihin ilimi na Pantami, domin har yanzu akwai waɗanda ba sa kallonsa da matsayin "Farfesa" saboda wannan dalili.
Abokan hamayyarsa na siyasa na iya amfani da wannan batu wajen nuna cewa Pantami yana amfani da muƙami domin samun abin da bai cancanta ba.
2. Tsaurin ra'ayin addini na baya

Source: Facebook
Mafi girman ƙalubalen da Pantami ke fuskanta shine kalaman da ya yi a shekarun 1990 da farkon 2000 lokacin yana matashin malamin addini.
Pantami ya shahara sosai a matsayin babban malami a Arewacin Najeriya, musamman a garinsu na Gombe, inda yake da dubban magoya baya.
Sai dai, a shekarar 2021 wasu faifan bidiyo da muryoyi sun sake bayyana a yanar gizo waɗanda suka nuna irin tsauraran ra'ayoyinsa na baya.
A cikin wani faifan bidiyo, an ji Pantami yana nuna goyon baya ga ƙungiyoyin tada kayar baya na ƙasashen waje irin su al-Qaeda da Taliban.

Kara karanta wannan
Jerin manyan malaman Musulunci 3 da suka tsaya ko nuna sha'awar takarar gwamna a Najeriya
Har ila yau, wasu rahotanni sun nuna cewa ya taɓa nuna goyon baya ga Osama bin Laden, wanda duniya ke kallo a matsayin babban ɗan ta'adda.
Rahoton da BBC ta fitar a ranar 23 ga Afrilun 2021, ya bayyana cewa an samu wasu takardu daga taron JNI na 2010 da Pantami ya halarta inda aka tattauna batun hana gina coci-coci a wasu garuruwa.
Haka kuma, an samu faifan muryar malamin yana kuka yayin da yake kiran ƴan ƙungiyar Boko Haram da "ƴan uwanmu musulmi" waɗanda ake zalunta.
Pantami ya mayar da martani, inda ya ce ya yi waɗannan kalaman ne lokacin yana matashi ɗan shekara 20 zuwa kusa da 30.
Ya bayyana cewa a lokacin ba shi da cikakkiyar fahimtar siyasar duniya, kuma tuni ya sauya ra'ayinsa wanda ya yi daidai da tafiyar zamanin da ake ciki.
Sai dai masu fashin baƙi sun ce waɗannan kalaman na iya sanya tsoro a zukatan Kiristocin dake Jihar Gombe da kuma masu zuba jari na ƙasashen waje.
3. Matsayar siyasar Pantani a 2006 da 2026

Source: Facebook
Wata takaddama kuma ita ce yadda Pantami yake iƙirarin daɗewa a siyasa, alhalin ya taɓa cewa shi ba dan siyasa ba ne, ba dan wata jam'iyya ba ne, kuma ba zai taɓa shiga siyasa ba.
A wani faifan bidiyo na shekarar 2006, an ji Pantami yana bayyana cewa shi malami ne kawai kuma ba ya shiga harkokin siyasa ko kaɗan.
A cikin bidiyon, ya nuna cewa malaman dake shiga siyasa suna ɓata mutuncin addini ne, kuma shi ba zai taɓa zama ɗaya daga cikinsu ba.
Faifan bidiyon wanda wani Imran U. Wakili ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna malamin a kan mumbarin masallaci yana cewa:
"Ni ban cika yin magana a kan siyasa ba, sai abin da ya zama ba makawa, ni ba dan siyasa ba ne, ban san siyasa ba, ban taba yi siyasa ba, ban taba zuwa taron siyasa ba.
"Don haka ba na daga cikin malaman da suka rike shugaban jam'iyya, ko sakataren jam'iyya, ban taba shiga taron siyasa ba, mu abin da muke shiga, taron sunnar Manzon Allah (S.A.W).
Sai dai a yanzu, yayin da ya sake sabunta rajistar jam'iyyar APC a Gombe, ya bayyana cewa ya jima yana siyasa tun shekarar 2001.
A cikin bidiyon, malamin ya ce:
"A tarihi, da yawa sun dauka wai yanzu ne muka shiga siyasa, ba yanzu muka shiga ba. Ana harkar siyasa da ni tun 2001."
Kalli bidiyon a kasa:
Martanin 'yan Najeriya kan siyasar Pantami
Wannan ya janyo saƙonni daga masu sharhi a kafafen sada zumunta irin su Imran U. Wakili, wanda ya yi tambaya ko a wane wa'azin ne za a ce Pantami ya yi ƙarya?
Wakili ya ce idan a 2006 Pantami ya ce ba ya siyasa, sannan a 2026 ya ce yana siyasa tun 2001, to akwai ƙarya a cikin ɗaya daga cikin maganganun.
Jarida Jaafar Jaafar ya soki wannan buri nasa sosai, inda ya ce Pantami ba zai iya sanya rigar malanta da ta siyasa a lokaci guda ba.
Fitaccen dan jaridar, ya yi bayanin cewa siyasa fage ne na yaudara da wasan cabali da zai iya bata mutum, wanda bai dace da mutumin dake iƙirarin jagorancin addini ba.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Jaafar ya ce: "Ba a gudu ana susar duwawu," karin maganar da ke nuna cewa dole Pantami ya ajiye malanta idan har yana son zama gwamna.
A zantawar Legit Hausa da da Salihu Ahmad, wani matashi a jihar Gombe, ya ce Sheikh Pantami yana da farin jinin jama'a, musamman ma matasa.
Salihu Ahmad ya ce:
"Malam yana da tarin jama'a, musamman saboda kasacewarsa malami. Ina da yakinin zai samu karbuwa idan ya fito takarar gwamna.
"To amma kasan halin siyasa, 'yar yarfi ce. Ba ruwanta da malami ko fasto, sai kaga jahili ya zo ya ci mutuncin malami, wannan ne ya sa wasu da dama ke zulumin shigar malamai siyasa.
"Da ace siyasar Najeriya tana da tsarki, to da babu ko shakka malamai za su fi cancantar shiga cikinta, ko ba komai, za su rika kiyaye hakkokin Allah a kan shugaba, za a samu adalci da shugabanci nagari."
Wata Rahama Kumo, ta shaidawa Legit Hausa cewa ita tana tare da Malam a duk matakin da zai dauka na siyasarsa.
"Ya yi namijin kokari wallahi. Ya toshe kunnensa daga ce-ce-ku-cen da za a yi. Ni na san kafin ya yanke hukunci, zai duba abin da ya fi dacewa garesa, addininsa da al'ummarsa. Ina tare da shi dari bisa dari."

Source: Twitter
Makomar Pantami a jihar Gombe
Idan har Pantami ya yi nasarar zama gwamnan Gombe, zai zama malami na biyu dake mulkar jiha a yankin Arewa maso Gabas tun 1999.
Na farko shine Jolly Nyame na Jihar Taraba wanda limamin coci ne, sannan Hyacinth Alia na Jihar Benue dake mulki a halin yanzu.
Magoya bayan Pantami suna kallonsa a matsayin mutumin da zai kawo ilimin zamani da na fasaha zuwa Jihar Gombe duba da gogewarsa a lokacin minista.
Suna ganin cewa kwarewarsa a fannin tattalin arzikin yanar gizo za ta taimaka wajen samar wa matasan jihar ayyukan yi na zamani.
Sai dai kuma, abokan hamayyarsa suna ganin cewa halayensa tun na dauri na iya janyo rarrabuwar kai a tsakanin mazauna jihar daban-daban.
Dole ne Pantami ya fito da dabarun da zai wanke kansa daga waɗannan zarge-zarge idan har yana son samun goyon bayan kowa da kowa.
"Kowa haushinka yake ji" - Bakas ga Pantami
A wani labari, mun ruwaito cewa, wani sakataren tsare-tsaren APC a Gombe, Ibrahim Musa Bakas, ya fadawa Sheikh Isa Ali Pantami gaskiya game da yadda jagororin jam'iyyar ke kallonsa.
Ibrahim Musa Bakas ya shaidawa Pantami cewa dukkan shugabannin APC suna jin haushinsa a jihar, saboda ya guje su a lokacin da ya samu mukamin minista.
Sakataren tsare-tsaren ya furta wannan magana ne a yanayi na fushi-fushi, game da batun rashin ziyartar ofishin jam'iyya da tsohon ministan yake yi.
Asali: Legit.ng






