Dr. Isa Ali Pantami ya yi martani kan rubutun da aka yi akansa na hannu a Boko Haram

Dr. Isa Ali Pantami ya yi martani kan rubutun da aka yi akansa na hannu a Boko Haram

- Dr Isa Ali Pantami ya mai da martani kan rubutun wata jarida na cewa yana da hannu a Boko Haram

- Ya yi ishara ga karatuttukansa na sama da shekaru 15 in da yake yakar munanan akidu irin na Boko Haram

- Ya kuma shaida wa jaridun cewa, lallai za su hadu da lauyoyinsa a gaban kotu nan gaba kadan

A safiyar yau ne NewsWireNGR ta buga cewa, gwamnatin kasar Amurka ta sanya sunan Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami cikin jerin masu hannu cikin tashin tashina na Boko Haram.

Bayan da jaridar ta lashe amanta biyo bayan cece-kuce, ta bayyana janye labarin da ta fitar, amma Dr Isa Ali Pantami ya mai da martani kan rubutun da jaridar ta wallafa.

Ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa:

"@NewsWireNGR Janye rubutunku ta hanyar binciken ka mai zaman kansa, na lura dashi. Ko da yake, aikin jarida na bincike yana bukatar bincike kafin a buga shi, ba bayan an buga ba.

KU KARANTA: Karya kika yi, Amurka bata zargin Pantami da daukar nauyin ta’addanci – Hadimin Buhari ga kafar yada labara

Dr. Isa Ali Pantami ya yi martani kan zargin da aka yi masa na hannu a Boko Haram
Dr. Isa Ali Pantami ya yi martani kan zargin da aka yi masa na hannu a Boko Haram Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

"Bugu da kari, manyan masu buga labarin za su hadu da lauyoyi na a kotu kan wannan bata suna.

"Akwai karatuttukana a kan sukar koyarwarsu da duk wasu mugayen mutane sama da shekaru 15, gami da muhawarorin da suka jefa rayuwata cikin hadari kan masu aikata laifi da yawa a Najeriya.
"Idan ba ku iya fahimtar Hausa, ku samu kwararren mai magana da yaren ya fassara muku da idon basira.
"Dangane da batun Tabbatar da NIN da SIM don yaki da rashin tsaro, babu gudu babu ja da baya.
"Babban manufarmu a matsayin GWAMNATI bisa dogaro da tsarin mulkinmu na 1999 (wanda aka yiwa kwaskwarima) Sashe na 14 (2) b shine TSARO, ba tattalin arziki kadai ba. Tabbas, babu ja da baya kwata-kwata. Masu tallafawa su ci gaba.
"FYI duka, da ikon Mai Duka, babu wani yawan matsi da zai hana @IsaPantami aiwatar da kyawawan manufofin Shugaba Muhammadu Buhari, GCFR kan tsaro.
"A KARSHE: Idan har yanzu baku lika SIM dinku da NIN ba, ku tabbata kun yi shi da wuri, kafin aikinmu na gaba. 'Yan ta'adda na jin zafin aikin.

KU KARANTA: Wike ga 'yan siyasa: Talakawa sun gaji, ku daina yi musu alkawuran karya

A wani labarin, Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad, ya mayar da martani game da rahotannin da ke cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Isa Pantami yana cikin jerin mutanen da kasar Amurka ke zargi.

A daya daga cikin sakonninta, NewWireNGR ta yi zargin cewa Pantami yana karkashin kulawar Amurka saboda zargin alakarsa da mayakan Boko Haram, Abu Quatada al Falasimi, da sauran shugabannin kungiyar Al-Qaeda.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel