Nesa Ta Matso Kusa: Hukumar INEC Ta Kammala Tsara Jadawalin Babban Zaɓen 2027

Nesa Ta Matso Kusa: Hukumar INEC Ta Kammala Tsara Jadawalin Babban Zaɓen 2027

  • INEC ta kammala tsara jadawalin babban zaben shekarar 2027 duk da cewa majalisar tarayya ba ta kammala gyaran dokar zabe ba
  • Tuni dai hukumar ta miƙa dukkan buƙatunta ga majalisar domin tantancewa da kuma tabbatar da su kafin lokacin zaɓen ya gabato
  • Duk da haka, INEC ta bayyana cewa za ta ci gaba da amfani da tsohuwar dokar zabe domin tabbatar da cewa shirye-shirye ba su tsaya ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ba da tabbacin cewa shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 suna tafiya yadda ya kamata.

Hukumar ta sanar da cewa tuni ta kammala tsara jadawalin ayyukan zaɓen duk da jinkirin da aka samu na sauya dokar zaɓe.

Hukumar INEC ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen babban zaben 2027.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan da ya yi magana kan shirin zaben 2027. Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairu, 2026, yayin wani taro a Abuja, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban NIMASA a mulkin Buhari ya shiga hannun ICPC

Shirin hukumar INEC kan zaben 2027

Farfesa Amupitan ya gana da ƙungiyoyin fararen hula (CSOs) domin yi musu bayanin irin nasarorin da aka samu zuwa yanzu kan zaɓen.

Shugaban ya bayyana cewa hukumar ta riga ta kammala duk wasu tsare-tsare na lokutan da za a gudanar da kowane fanni na zaɓen.

Ya amince da cewa wasu sassa na jadawalin za su iya canzawa idan majalisar ƙasa ta amince da sababbin sauye-sauyen dokar zaɓe.

A halin yanzu, INEC ba ta da wani zaɓi illa ta ci gaba da amfani da tsohuwar dokar zaɓe dake aiki yanzu.

Hukumar ta ce ba za ta zauna jiran majalisa ba, domin hakan na iya janyo cikas ga babban zaɓen da ƙasar ke tunkara.

Tasirin kungiyoyi a lokutan zabe

Farfesa Amupitan ya jaddada muhimmancin ƙungiyoyin fafaren hula wajen tabbatar da gaskiya da amana a lokacin gudanar da harkokin zaɓe a Najeriya.

Hukumar ta miƙa dukkan buƙatunta ga majalisar dokoki ta ƙasa domin tantancewa da kuma tabbatar da su kafin lokacin zaɓen ya gabato.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, Gwamnatin Tinubu ta rufe bakin matasan N Power

A cewar shugaban, babban burinsu shi ne su kasance a shirye a kowane lokaci domin kauce wa kura-kuran da aka yi a baya.

INEC ta ce za t ci gaba da amfani da tsohuwar dokar zabe kafin majalisa ta kammala sabuwar.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan yana jawabi a wanin wayar da kai kan zabe. Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

INEC ta ba 'yan Najeriya tabbaci

Farfesa Amupitan ya ba wa ƴan Najeriya tabbacin cewa za a gudanar da zaɓe mai inganci wanda kowa zai gamsu da sakamakonsa.

Wani rahoto na Punch ya ruwaito cewa hukumar INEC za ta ci gaba da wayar da kan jama'a kan muhimmancin katin zaɓe da kuma rajistar masu zaɓe da za a fara nan gaba.

A halin yanzu, ƴan siyasa da jam'iyyu sun fara sanya ido kan wannan sabon jadawali domin tsara yadda za su fuskanci yakin neman zabe.

Ana sa ran za a fitar da cikakken bayani kan ranakun zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni a cikin watanni masu zuwa.

INEC ta dawo rajistar masu zabe

A wani labarin, mun ruwaito cewa, INEC ta ce ta dawo da aikin rajistar masu jefa ƙuri’a a faɗin Najeriya bayan kammala zagaye na farko da aka rufe a watan Disamban 2025.

Hukumar ta bayyana cewa miliyoyin ’yan ƙasa sun yi rajistar ta yanar gizo da ta zahiri a zagaye na farko, lamarin da ya nuna sha’awar harkar zaɓe.

Sai dai hukumar INEC ta ce a yanzu an dakatar da rajistar a Anambra da Babban Birnin Tarayya saboda wasu muhimman ayyukan zaɓe da ke gudana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com