APC Ta Ware Matsayin da Za Ta ba Kwankwaso idan Ya Sauya Sheka tare da Gwamna Abba

APC Ta Ware Matsayin da Za Ta ba Kwankwaso idan Ya Sauya Sheka tare da Gwamna Abba

  • APC reshen jihar Kano ta ce a shirye take ta karbi jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso idan ya amince zai shiga jam'iyyar
  • Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa za a mutunta Kwankwaso idan ya sauka sheka, amma ba shi zai jagoranci APC a Kano ba
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da siyasar jihar Kano ke daukar hankali bayan ganawar Gwamna Abba Kabir Yusuf da shugaban kasa Tinubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa suna maraba da jagoran NNPP na kasa, sanata Rabiu Musa Kwankwaso idan ya amince ya dawo jam'iyyarsu.

Abbas ya ce za su karbi Rabiu Kwankwaso idan ya sauya sheka tare da mai girma gwamna Abba, Kabir Yusuf, kuma zai shiga cikin iyayen jam'iyya a jihar Kano.

Kara karanta wannan

APC ta fayyace wanda zai zama jagora a Kano tsakanin Gwamna Abba da Ganduje

Gwamna Abba da Kwankwaso.
Jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabur Yusuf Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Shugaban APC ya bayyana haka ne a wata hira da Freedom Radio ta Kano ta yi da shi kan shirye-shiryen fara rijistar mambobin jam'iyya ta na'ura.

Gwamna Abba zai karbi katin jam'iyyar APC

Abdullahi Abbas, wanda ya halarci wurin bai wa ma'aikatan wucin gadi sama da 1,500 horo, ya ce watakila Gwamna Abba ne zai kaddamar da fara aikin a hukumance.

Ya ce duk da har yanzu gwamnan bai sanar da shiga APC a hukumance ba, amma su na sa ran zai yanki katin zama cikakken dan jam'iyya idan ya koma Kano daga Abuja.

Da aka tambaye shi matsayin da za su ba Kwankwaso, wanda ya jagoranci kafa gwamnatin Abba, idan ya shiga APC, Abdullahi Abbas ya ce zai shiga cikin iyayen jam'iyya.

Wane matsayi za a ba Kwankwaso?

A cewarsa, idan Kwankwaso ya amince ya sauya sheka zuwa APC, zai shiga cikin shugabanni, wadanda za su rika jagorantar tafiyar da harkokin jam'iyya.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: NNPP ta hango makomarta a Kano bayan ficewar Gwamna Abba

"Idan (Kwankwaso) ya shigo APC, zai shiga cikin shugabanni amma ba shi ne jagoran tafiya ba, yana nan a cikin shugabanni ko iyayen jam'iyya, shi ma zai zama kamar uban jam'iyya.
"Mu a ka'idar mu gwamna shi ne jagoran jam'iyya, shi kuma zai zama uba a cikin jam'iyya, sai ya zama yana cikin iyayen APC a Kano."

- Abdullahi Abbas.

Kwankwaso da Ganduje.
Jagoran NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso da tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje Hoto: @SaifullahiHON, Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Twitter

Me yasa Kwankwaso ba zai jagoranci APC ba?

Da aka kara tambayarsa kan ko za su ba Kwankwaso jagorancin APC ganin yada ya taimaki Ganduje da Abba suka samu mulki, Abdullahi Abbas ya ce hakan ba za ta yiwu ba.

Ya ce ba su suka kirkiro tsarin da ya ba gwamna jagorancin jam'iyya a jiha ba, kundin tsarin mulkin APC ne ya tanadi hakan, don haka ba za su saba masa ba, cewar Vanguard.

"Ba tsarin mu ba ne, kundin tsarin mulkin jam'iyya ko ka'idarta ne haka, gwamna shi ne jagora, saboda haka ba mai iya canzawa, duk girman mutum ba yadda za a ba shi jagoranci," in ji shi.

Tinubu ya share wa Gwamnan Kano hanya

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu damar da yake bukata don komawa APC bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, an ji lokacin da Gwamna Abba zai zama 'dan APC a Kano

Wasu majiyoyi aun ce Shugaba Tinubu ya sharewa Gwamna Abba fagen shiga APC a hukumance nan da yan kwanaki kadan.

A cewar majiyoyin, gwamnan ya 'dan jinkirta ne saboda rashin tabbas kan makomar siyasarsa a APC, musamman batun takara a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262