Mataimakin Gwamnan Kano Ya Dawo, Ya Nuna Wanda Zai Bi tsakanin Abba da Kwankwaso

Mataimakin Gwamnan Kano Ya Dawo, Ya Nuna Wanda Zai Bi tsakanin Abba da Kwankwaso

  • An ga mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a gidan jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Kwankwaso
  • Wannan ziyara da Aminu Gwarzo ya kai na zuwa a lokacin da ake rade-radin alaka ta yi tsami tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba
  • Ana ganin ziyarar alama ce da ke nuna mataimakin gwamnan na nan tare da Kwankwaso, ba zai bi masu shirin tafiya APC ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya fara nuna bangaren da ya dauka tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Injiniya Rabiu Kwankwaso.

An ga Kwamared Aminu Gwarzo ya ziyarci jagoran NNPP kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, lamarin da ke nuna inda akalar siyasarsa ta karkata.

Kwankwaso da Gwarzo.
Jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo Hoto: Ibrahim Ayuba Gwarzo
Source: Twitter

Mataimakin gwamnan Kano ya bi Kwankwaso?

Kara karanta wannan

An zo wajen: Kwankwaso ya kafa sharadin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Leadership ta tattaro cewa bayyanar mataimakin gwamnan a gidan jagoran jam’iyyar NNPP na kasa a yau ranar Laraba, na iya zama wata alama dake nuna mubaya'arsa ga Kwankwaso.

Wannan taro ya gudana ne a gidan Kwankwaso da ke titin Miller a Kano, inda jagoran na Kwankwasiyya ke ci gaba karbar bakuncin shugabannin jam’iyyar NNPP da magoya da daban-daban.

An ce an ga Aminu Gwarzo ne lokacin da Kwankwaso ya gana da shugabannin NNPP da masoyansa daga kananan hukumomin Rano da Dawakin Tofa, gami da wasu kungiyoyin Kwankwasiyya.

Aminu Gwarzo ya hadu da Kwankwaso

A lokacin zaman, an hango Kwamared Aminu Abdussalam zaune daram a gefen Kwankwaso, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun fassara wannan zama a matsayin babban sako da ke nuna cewa mataimakin gwamnan na goyon bayan Kwankwaso har yanzu.

Gwarzo ya nuna alamun bangaren da ya dauka ne a daidai lokacin da rade-radin ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC ke dada karfi.

Mataimakin gwamna ya dawo daga Saudiyya

Duk kusan takaddama da musayar yawun siyasa da suka auku Kano, mataimakin gwamnan yana kasar Saudiyya domin gudanar da Umrah.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: An wanke Gwamna Abba, ba ya bukatar izinin Kwankwaso kafin komawa APC

Mutane da dama sun zura idon ganin ko Aminu Abdussalam zai canza sheka tare da Abba ko kuma zai sauya salon siyasarsa idan ya dawo kasar.

Kwankwaso.
Jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwanwakso yayin da ya karbar bakuncin mabiyansa a Kano Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Sai dai, bayyanarsa a taron ranar Laraba ya nuna cewa har yanzu yana nan daram a cikin tafiyar Kwankwasiyya, karkashin jagorancin Sanata Kwankwaso.

Aminu Gwarzo dai na daya daga cikin manyan na kusa da Kwankwaso, wadanda ake hasashen za su iya ci gaba da zama a NNPP maimakon tafiya APC tare da Abba.

Tsagin NNPP ya waiwayi Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa tsagin NNPP ya soki tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso kan batun sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

A cewar tsagin jam'iyyar NNPP, Gwamna Abba na da 'yancin yafiya APC ba tare da ya nemi amincewar ubangidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.

NNPP ta ce ba ta da wata matsala da kowace jam'iyya ciki har da APC, don haka ba za ta tursasa wa gwamna zama ba idan ya riga ya yanke shawarar tafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262