Tinubu Ya Fadi Gwamnoni 2 da Suka San Wahalar da Ya Sha kafin Nasara a 2023
- Shugaba Bola Tinubu ya ce ya sha matsananciyar wahala da kalubale da dama kafin samun nasara a zaben 2023
- Tinubu ya bayyana cewa sauya fasalin Naira da dogon layi a gidajen mai sun jefa jama’a cikin kunci
- Ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da tsayawa tsayin daka kan dimokuradiyya tare da godewa Allah duk da wahalhalun da aka sha
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da zaben shekarar 2023 da ta ba shi nasara zuwa kujerar shugaban kasa.
Tinubu ya tuno irin kalubalen da ya fuskanta duk domin zaben wanda a karshe jam'iyyar APC ta yi nasara da rinjaye.

Source: Twitter
Hakan na wani faifan bidiyo da Imranmuhdz ya wallafa a X yayin jawabin Tinubu a taron jiga-jigan jam'iyyar APC da aka gudanar a Abuja.
Tinubu ya tuna kalubalen da ya fuskanta
Yayin jawabinsa, Tinubu ya ce ya sha bakar wahala da tsallake tarkuna kafin samun nasara a zaben 2023 da ta gabata da marigayi Muhammadu Buhari ya mika masa mulki.
Tinubu ya ce gwamnoni biyu sun san irin wahalar da ya sha kama daga sauya fasalin Naira har zuwa dogon layi a gidajen mai.
Shugaban ya kira sunan gwamnoni biyu da suka hada na Yobe, Mai Mala Buni da kuma na Kaduna, Uba Sani a matsayin wadanda za su shaida hakan.
Ya ce:
"Gwamnan Yobe da sauran yan uwansa sun san wahalar da na sha a kan hanyar zama shugaban kasa.
"Gwamna Uba Sani ma zai shaida haka, an samu ruguntsumi daga sauya fasalin kudi zuwa dogon layi a gidajen mai."

Source: Facebook
Tarnaki da Tinubu ya fuskanta a zaben 2023
Tinubu ya koka kan yadda aka sha wahala a wancan lokaci musamman kuncin da aka shiga na rashin kudi, cewar Punch.
Ya ce mutane da dama sun mutu saboda rashin kudi musamman bayan sauya fasalin Naira wanda ya kawo karancin kudi a kasa.
"Mutane da dama sun mutu saboda ba su da abincin da za su ci a rana saboda rashin kudi kan zabe daya kacal.
"Idan kun yi imani da ikon Allah, sai mu godewa Allah, dole mu kara tsayawa tsayin daka kan wannan dimukradiyya domin ta tabbata."
- Bola Tinubu
Bola Tinubu ya ce ikon Allah ne ya kawo shi kan kujerar mulkin Najeriya inda ya ce ba tare da ikon Allah ba, da ba su kawo war haka ba kuma a kan mulki.
Alkawarin da Tinubu ya yi ga Amurka
An ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa dole ne a tabbatar da kafa 'yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaro da ƙarfafa mulki a ƙasa.
Tinubu ya bayyana cewa ya ba Amurka da abokan hulɗar Najeriya a Turai tabbacin cewa Najeriya za ta aiwatar da tsarin ’yan sandan jihohi.
Shugaban ya kuma matsa lamba kan ’yancin ƙananan hukumomi tare da kira ga gwamnonin jihohi su daina riƙe kuɗinsu a yayin taron jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng

