Tinubu, Gwamnoni, Sun Hallara a Fadar Aso Rock, APC Ta Shirya Muhimmin Taro

Tinubu, Gwamnoni, Sun Hallara a Fadar Aso Rock, APC Ta Shirya Muhimmin Taro

  • APC ta gudanar da taron kusoshin jam'iyyar na kasa, karon farko karkashin sabon shugabanta, Nentawe Yilwatda, a fadar Aso Rock
  • Gwamnoni shida da suka fice daga PDP zuwa APC sun halarci taron tare da shugabannin majalisar tarayya da dattawan jam’iyyar
  • APC ta ce yanzu tana da rinjayen kujeru a majalisar dattawa da ta wakilai, tare da kaddamar da tsarin rijistar mambobi ta yanar gizo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam’iyyar APC ta gudanar da babban taron kusoshinta na kasa a dakin taro na Banquet Hall da ke cikin fadar shugaban kasa a Abuja.

Wannan shi ne taron kusoshin APC na farko da Nentawe Yilwatda, sabon shugaban jam’iyyar na kasa, ya jagoranta tun bayan hawansa kan kujerar shugabanci.

APC ta shirya babban taron kusoshin jam'iyyar na kasa, wanda Tinubu ya halarta.
Tinubu, Shettima, sun halarci taron kusoshin jam'iyyar APC a Abuja. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Tinubu, 'yan majalisa sun hallara a Abuja

Kara karanta wannan

Jakadun da Tinubu ya zaba sun san matsayarsu bayan tantancesu a majalisa

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya isa dakin taron da misalin karfe 7:38 na yammacin ranar Alhamis, inda aka fara zaman, kamar yadda The Cable ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya samu rakiyar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da mataimakin kakaki, Benjamin Kalu.

Gwamnonin da suka sauya-sheka sun je taron APC

Daga cikin manyan abubuwan da suka dauki hankali a taron akwai halartar gwamnonin da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Wadannan sun hada da Peter Mbah (Enugu), Siminalayi Fubara (Rivers), Sheriff Oborevwori (Delta), Umo Eno (Akwa Ibom), Agbu Kefas (Taraba) da Douye Diri (Bayelsa).

Wannan ne karon farko da wadannan gwamnonin suka halarci taron manyan kusoshin APC bayan sauya jam’iyya.

Gwamnonin jihohin APC sun halarci taron

Sauran gwamnonin APC da suka halarci taron sun hada da Monday Okpebholo (Edo), Inuwa Yahaya (Gombe), Lucky Aiyedatiwa (Ondo) da Usman Ododo (Kogi).

Kara karanta wannan

Akpabio: Bayan yada jita jita, an ji gaskiyar batun rashin lafiyar shugaban majalisar dattawa

Sauran sun hada da Biodun Oyebanji (Ekiti), Francis Nwifuru (Ebonyi), Ahmed Aliyu (Sokoto), Mai Mala Buni (Yobe), Hyacinth Alia (Benue), Bassey Otu (Cross River) da AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara).

Har ila yau ragowar sun hada da Abdullahi Sule (Nasarawa), Dapo Abiodun (Ogun), Uba Sani (Kaduna) da Dikko Radda (Katsina), kamar yadda Punch ta rahoto.

Dattawa da tsofaffin shugabanni a taron APC

Taron ya samu halartar dattawan jam’iyyar APC da dama, ciki har da Bisi Akande, tsohon shugaban APC na farko, Segun Osoba, tsohon gwamnan Ogun, Adegboyega Oyetola, tsohon gwamnan Osun.

Har ila yau akwai Ben Ayade, tsohon gwamnan Cross River, Jolly Nyame, tsohon gwamnan Taraba, da Ifeanyi Okowa, tsohon gwamnan Delta.

Haka kuma, tsofaffin shugabannin majalisar dattawa Ken Nnamani da Anyim Pius Anyim, da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Ovie Omo-Agege sun halarta.

Sauran sun hada da Buba Marwa, shugaban NDLEA, Isa Yuguda, Yahaya Bello, Adams Oshiomhole, Abubakar Bello, Ibikunle Amosun, Niyi Adebayo, Abdulaziz Yari da Ahmed Sani Yerima.

Kara karanta wannan

Kakakin Majalisa na neman haddasa rigima a jam'iyyar APC kan tikitin zaben 2027

APC ta ce ita ce mai rinjaye a majalisar tarayya yayin da ta gudanar da taron kusoshin jam'iyyar.
Shugaba Bola Tinubu ya halarci taron kusoshin jam'iyyar APC a Abuja. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

APC ta ce tana da gagarumin rinjinaye a majalisa

Da yake jawabi ga mahalarta taron, Nentawe Yilwatda ya ce yawan sauya shekar da ake samu, musamman daga gwamnonin jihohi da ’yan majalisa, na nuna yadda jam’iyyar APC ke kara karfi a fadin kasa.

Ya ce APC yanzu tana da rinjayen kujeru a majalisar dattawa da majalisar wakilai yayin da ya ce jam'iyyar ta kaddamar da tsarin rajistar mambobi ta yanar gizo.

Ya bukaci shugabanni da mambobi da su ba da hadin kai domin tabbatar da nasarar shirin kafin gudanar da manyan tarukan jam’iyya na gaba.

An zabi sabon shugaban APC na kasa

Tun da fari, mun ruwaito cewa, APC ta gudanar da taron kwamitin NEC, inda aka zabi Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyya na kasa.

Zaben Farfesa Yilwatda ya zo ne bayan saukar tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar, wanda ya yi mulkin jam’iyyar kafin lokacin.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta shiga dambarwar Dangote da shugaban NMDPRA

Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda kwararren masanin kimiyya ne daga jihar Filato kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com