Gwamna Mutfwang Ya Bi Sahun Gwamnonin PDP Masu Sauya Sheka zuwa APC

Gwamna Mutfwang Ya Bi Sahun Gwamnonin PDP Masu Sauya Sheka zuwa APC

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta kara yawan gwamnonin da take da su a cikin jihohi 36 na tarayyar Najeriya
  • Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya watsar da jam'iyyarsa ta PDP inda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sanar da sauya shekar Gwamna Mutfwang a wajen wani taro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Jam’iyyar APC ce ta sanar da sauya shekar Gwamna Caleb Mutfwang, daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Gwamna Mutfwang ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Gwamna Mutfwang ya koma APC daga PDP

Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yelwata, wanda shima ɗan jihar Plateau ne, ya sanar da ficewar gwamnan daga PDP.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya ba da tabbaci kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Nentawe Yilwatda ya sanar da hakan yayin wani taron APC da aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa, da ke binin Abuja.

APC ta kara yawan gwamnoni a Najeriya

Yelwata ya ce da sauya shekar Gwamna Mutfwang, yanzu dukkan yankin Arewa ta Tsakiya yana karkashin mulkin jam’iyyar APC, jaridar The Punch ta dauko labarin.

Gwamna Mutfwang, wanda aka zaɓe shi a ƙarƙashin PDP a zaɓen gama-gari na 2023, ya zama sabon babban ɗan siyasa da ya fice daga babbar jam’iyyar adawa.

An tabo batun rajistar mambobin APC

A taron, shugaban APC ya sanya wa’adin 30 ga watan Janairu, 2026 ga dukkan mambobin jam’iyyar su kammala rajista ta hanyar na'ura don zama mamba.

Ya ce fara aiki da tsarin rajistar na’ura, wanda tuni ya fara, zai kara gaskiya, ingancin bayanai da kuma dimokuraɗiyyar cikin gida a jam’iyyar.

“Mun yi horo a matakin jihohi, mun yi a matakin shiyyoyi, mun kuma yi a kananan hukumomi a yawancin jihohi. Ina kira ga masu ruwa da tsaki da su goyi bayan aiwatar da wannan muhimmin aiki a faɗin ƙasa."

Kara karanta wannan

PDP ta sake birkicewa, sanata ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

“Mu yi amfani da wannan dama mu tabbatar wa sababbin mambobi cewa suna da cikakken ’yanci da hakkoki a cikin jam’iyyar, tare da karfafasu su yi amfani da rajistar mambobi ta ƙasa domin su yi wa magoya bayansu rajista."
"Don haka tsofaffi da sababbin mambobi duka su shiga wurin rajista su yi rajistar dukkan mambobinsu."
“Muna sa ran a kammala wannan aiki daga yanzu zuwa karshen Janairu, wato 30 ga watan Janairun 2023"
"Dole ne dukkan mambobi su yi rajista tare da shiryawa tarurrukan jam’iyya da ke tafe."

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Shugaban APC na so mambobi su yi rajista
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Gwamna Mutfwang ya gana da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sa labule da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Caleb Mutfwang ya gana da Mai girma Bola Tinubu ne a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

A yayin ganawar ta su, Shugaba Tinubu ya amince da shirin sauya shekar gwamnan zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng