Minista Ya ba Mutanen Kudu maso Gabas Dalilan Sake Zaben Tinubu a 2027

Minista Ya ba Mutanen Kudu maso Gabas Dalilan Sake Zaben Tinubu a 2027

  • Ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya bayyana yadda Shugaban Kasa Bola Tinubu ya jawo cigaban shiyyarsa ta Kudu maso Gabas
  • Ya ce shugabancin haɗin-kai da manyan ayyuka Tinubu ke aiwatarwa sun sa ƴan yankin jin kansu kamar cikakkun yan Najeriya
  • Umahi ya bayyana cewa yankin zai mara wa Tinubu baya a zaɓen 2027, yana mai cewa korafe-korafen wariya ba su da tushe a halin yanzu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce tsarin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bai wa kowa dama ba tare da fifita wasu yankunan a kan sauran ba.

Umahi ya ce kudin Tinubu ke zubawa a manyan ayyukan more rayuwa a yankin Kudu-maso-Gabas za su sa yankin ya mara masa baya a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"A bayyane yake": An hango abin da Tinubu zai yi wa Shettima a zaben 2027

David Umahi ya yi magana kan salon mulkin Tinubu
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu tare da David Umahi, Ministan ayyuka Hoto: David Umahi
Source: Twitter

The Cable ta wallafa cewa Umahi ya faɗi haka ne a wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja, inda ya jaddada yadda gwamnatin Tinubu ta mutunta yankinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umahi ya magantu kan mulkin Tinubu

Jaridar Daily Post ta ruwaito Umahi ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta kawo ƙarshen dogon lokaci na ware yankin daga manyan tsare-tsaren ci gaban ƙasa.

A cewarsa, shugabancin Tinubu ya haɗa Kudu-maso-Gabas a cikin tsare-tsaren ci gaban tarayya, don haka zargin wariya ba shi da tushe a yau.

A kalamansa:

"Shugaba Bola Tinubu ya yi wa kudu-maso-gabas abin a yaba, kuma za mu jefa masa ƙuri’a a 2027.

Ya ce wasu shugabannin yankin na tada maganar cewa lokaci ya yi da Kudu-maso-Gabas za ta samar da Shugaban Kasa, amma ya ce ya dace a bar Tinubu ya kammala wa’adinsa na shekaru takwas.

'An shigar da yankinmu a mulki' - Umahi

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Shugaba Tinubu ya fayyace gaskiya kan matsalolin Najeriya

David Umahi ya ce shigar da yankinsa cikin harkokin mulki da ake yi a yanzu hanya ce ta magance tsofaffin korafe-korafe, yana mai ƙara da cewa sauran yankuna, ciki har da Kudu-maso-Gabas, su ma sun amfana.

Ya kuma buƙaci shugabannin Kudu-maso-Gabas su tashi tsaye su yi magana kan ƙarya da kuma suka marar tushe a kan gwamnatin Bola Tinubu.

David Umahi ya nemi a sake zaben Tinubu a zaben 2027
Ministan ayyuka, David Umahi Hoto: David Umahi
Source: Getty Images

Ministan ya kuma mayar da martani kan kalaman Sanata Enyinnaya Abaribe na Abia ta Kudu, wanda ya yi shakku kan aikin gwamnatin tarayya a yankin.

Umahi ya ce kalaman ba daidai ba ne, yana mai cewa dukkanin gwamnonin Kudu-maso-Gabas na goyon bayan Shugaban Ƙasa saboda tsarin mulkin haɗin-kai da ya kawo.

Ya lissafo kafa cibiyar horas da sojoji a Ebonyi domin magance rashin tsaro, fara aiki da tashar wutar lantarki ta Enyimba, da kuma nadin manyan jami’an tsaro daga yankin a matsayin hujjoji.

Shugaba Tinubu ya yi wa talakawa albishir

A baya, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kwantar wa ’yan Najeriya da hankula kan sabon tsarin dokokin haraji da gwamnatinsa ta tsara da zai fara aiki a shekarar.

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da tabbaacin da cewa sauye-sauyen za su amfanar da talakawa, masu ƙaramin albashi da kuma ƙananan ’yan kasuwa ba wai muzguna masu ba.

Tinubu ya bayar da wannan tabbaci ne ta bakin Shugaban Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS), Dr. Zacheus Adedeji, wanda ya wakilce shi a wajen Taron Ajimobi Roundtable na 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng