Akwai Damuwa: An Yi Hasashen Tinubu Zai Iya Neman Hanyar Dauwama a Mulki
- Fasto Seun Adeoye ya yi gargadi ga yan Najeriya da su dage da addu'o'i musamman game da mulkin Bola Ahmed Tinubu
- Adeoye ya ce Shugaba Bola Tinubu na iya neman zama shugaban ƙasa na har abada, yana cewa alamun sun wuce siyasar 2027
- Limamin ya ce ana murƙushe adawa, yayin da bangaren shari’a, majalisa da manyan hukumomi ke fuskantar matsin lamba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Malamin addinin Kirista a Najeriya, Seun Adeoye ya yi magana game da shugabancin Bola Tinubu a kasar.
Faston ya bayyana damuwa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya neman zama shugaban ƙasa na har abada a Najeriya.

Source: Facebook
Fasto ya ba 'yan Najeriya shawara kan Tinubu
Hakan na cikin wata sanarwa a Leadership wanda ya fitar a Osogbo ranar Talata 17 ga watan Disambar shekarar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabaran Adeoye, wanda shi ne wanda ya kafa cocin 'Sufficient Grace and Truth International Ministries', ya bukaci Kiristoci a fadin kasar nan su gudanar da bikin Kirsimeti cikin natsuwa da tunani.
Ya bukaci mabiya addinin Kirista su tuna da dubban mutanen da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda suka hallaka, tare da nuna goyon baya ga wadanda har yanzu ke hannu.
Makircin da Fasto ya zargi Tinubu da yi
Da yake magana kan yanayin siyasar Najeriya, Fasto Adeoye ya ce yana da yakinin cewa ana shirin sauya tsarin siyasa domin bai wa Shugaba Tinubu damar zama shugaban kasa har abada.
Ya ce:
“Abin da ake yi a yanzu ya wuce dabarun siyasar 2027. Yunkuri ne na sauya dokoki domin mutum guda ya mallaki mulki har abada.
"Wannan ba batun wa’adi na biyu ba ne, shiri ne na boyayyen buri na rayuwa.”

Source: Twitter
Yadda ake zargin Tinubu ya raunana adawa

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023
Limamin ya kara da cewa adawa ta raunana, yayin da bangaren siyasa da shari’a ke fuskantar matsin lamba.
Ya ce manyan hukumomi kamar sojoji, ‘yan sanda da hukumar zabe suna karkashin tsauraran matakai.
Adeoye ya kuma soki abin da ya kira shiru da rashin fitowar masu fafutuka, yana cewa masu yada farfaganda za su fara kwatanta Najeriya da kasashen China da Rasha, inda shugabanni ke dadewa kan mulki.
Ya ce za a yi amfani da bokaye da masu kiran kansu masu ruhi wajen yaudarar jama’a cewa mutum guda ne kawai aka zaba har abada.
Limamin ya yi gargadin cewa masu goyon bayan wannan tsari za su rika lakaba wa masu adawa suna da makiyan kasa, tare da tilasta kowa ya bi sahu.
'Yan adawa sun taso Tinubu a gaba
Mun ba ku labarin cewa ‘yan adawa sun gargadi Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu kan barazanar mayar da kasar karkashin jam’iyya ɗaya.
Wadanda suka bayyana takaicinsu sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisa, Sanata David Mark.
Sun zargi gwamnati da amfani da hukumomin tsaro da yaki da cin hanci don tsoratar da 'yan adawa gabanin babban zaben shekarar 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

