BoT: PDP Ta Dare Gida 2, Tsagin Abdulrahman Ya Kafa Sabon Kwamiti a Gidan Wike

BoT: PDP Ta Dare Gida 2, Tsagin Abdulrahman Ya Kafa Sabon Kwamiti a Gidan Wike

  • Wani tsagin PDP ya kaddamar da sabon kwamitin amintattu karkashin jagorancin Mao Ohabunwa a gidan ministan Abuja
  • Abdulrahman Mohammed, wanda ke jagorantar wannan tsagin ya ce sabon kwamitin zai dawo da PDP kan turbar gaskiya
  • Rikicin shugabanci tsakanin tsagi biyu na PDP dai ya kara zafi, inda Umar Damagum ya gargadi shugabannin jihohi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Tsagin PDP, da ke karkashin mukaddashin jam'iyyar na kasa, Abdulrahman Mohammed ta zabi sababbin shugabannin kwamitin amintattu (BoT).

Jam'iyyar PDP ta Abdulrahman ta zabi tsohon sanata Mao Ohabunwa a matsayin shugaban sabon kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT).

Tsagin jam'iyyar PDP da ke karkashin Abdulrahman Mohammed ya nada sababbin shugabannin kwamitin amintattu.
Hoton shugabannin PDP suna gudanar da taro a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

PDP ta zabi shugabannin kwamitin amintattu

Channels TV ta rahoto cewa an gudanar da zaben ne a gidan Ministan Abuja, Nyesom Wike, inda Isah Dansidi ya fito a matsayin sakataren kwamitin.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Shugabananni a jihohi 36 sun raba gardama tsakanin Damagum da tsagin Wike

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukaddashin shugaban jam’iyyar, Abdulrahman Mohammed, ya bayyana cewa wannan sabon mataki ne na farfado da jam’iyyar daga rikice-rikicen cikin gida.

Abdulrahman Mohammed ya ce:

"Ba kaddamar da sabon kwamiti muke yi a yau ba, har ma da sake tabbatar da gina sabon tubalin farfado da martabar jam’iyyarmu, cikin adalci, gaskiya da bin doka.”

Abdulrahman ya ce PDP za ta sake zama jam’iyyar da ke kare muradun jama’a kuma za ta gina tsarin mulki mai gaskiya da bin doka.

A cewarsa, sabon kwamitin zai zama ginshikin gyaran jam’iyyar da zai tabbatar da gudanar da babban taron kasa da zabukan shugabanni cikin gaskiya da tsari.

PDP: Dalilan sauya shugabannin BoT

Mukaddashin shugaban na PDP ya ce tsohon kwamitin amintattu karkashin Sanata Adolphus Wabara ya gaza gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa.

Ya ce:

“Rikicin PDP ya samo asali ne tun kafin zaben 2015 lokacin da aka yi watsi da tsarin rabon mukamai. Wannan ya lalata martabar jam’iyyar.”

Kara karanta wannan

Gwamna ya dakatar da sarkin da ake zargi yana daukar nauyin ta'addanci a Akwa Ibom

A cewarsa, sabon kwamitin amintattun zai tabbatar da cewa jam’iyyar ba za ta sake zama 'karamar danga mai saukin tsallakewa' ga wasu manyan ‘yan siyasa ba.

Abdulrahman ya yi kira ga mambobin jam’iyyar su hada kai domin dawo da PDP kan turbar gaskiya da mutunci.

Shugaban PDP na kasa, Umar Damagun ya gargadi shugabannin jam'iyyar na jihohi kan cin amana.
Shugaban PDP na kasa, Umar Damagun yayin da ya jagoranci taron shugabannin jam'iyyar a Abuja. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Facebook

PDP: Damagum ya gargadi shugabannin jihohi

A wani bangare kuma, shugaban PDP na kasa, Umar Damagum, ya gargadi shugabannin jam’iyyar a jihohi da su guji cin amanar jam’iyya.

Ya ce rashin biyayya da kuma yi wa jam’iyyun adawa aiki ta karkashin kasa zai jawo hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da laifi.

A kwanakin baya, kwamitin NWC da ke karkashin Damagum ya dakatar da wasu manyan jami’an jam’iyyar bisa zargin cin amanar jam’iyya, kamar yadda muka ruwaito.

Wadanda abin ya shafa sun hada da Samuel Anyanwu, Kamaldeen Ajibade, da wasu mutum biyu da ke cikin kwamitin shugabancin kasa.

Zanga-zanga ta barke a sakatariyar PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, zanga zanga ta barke a sakatariyar PDP da ke Abuja kan rikicin shugabanci da ya mamaye jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Damagum: Shugaban PDP ya fadi dalilin kin hukunta masu kawo cikas a jam'iyyar

Magoya bayan sabon mukaddashin shugaban PDP da bangaren Wike ya nada, Abdulrahman Mohammed sun barke da zanga-zanga a sakatariyar.

Sun bukaci Ambasada Umar Damagum da duk mambobin NWC da ke goyon bayansa, su bar sakatariyar jam'iyyar PDP nan take don Abdulrahman ya kama aiki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com