An Bazo Wa Minista Wuta, Hadimin Atiku Ya Bukaci Shugaba Tinubu Ya Tsige Shi Nan Take
- Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Paul Ibe ya ce bai kamata Uche Nnaji ya ci gaba da zama a kujerar Ministan Kimiyya da Fasaha ba
- Mai magana da yawun Atiku ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke Ministan kuma ya mika shi domin a gurfanar da shi a kotu
- Wannan dai na zuwa ne bayan bincike ya bankado cewa takardun Uche Nnaji na kammala digiri da bautar kasa watau NYSC duk na bogi ne
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Zargin amfani da takardun bogi da ake yi wa Ministan Kimiyya da Fasaha, Cif Uche Nnaji na kara tayar da kura a Najeriya.
Paul Ibe, Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce kamata ya yi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsige ministan daga mukaminsa nan take.

Source: Twitter
Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku ya bayyana haka ne a wani gajeren sako da ya wallafa shafinsa na Facebook yau Litinin, 6 ga watan Oktoba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bazo wa Ministan Tinubu wuta
Wannan dai na zuwa ne bayan bincike ya bankado cewa ministan ya gabatar da satifiket din kammala digiri na bigi ga Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Dattawa yayin tantancewa.
Binciken, wanda jaridar Premium Times ta wallafa ranar Asabar da ta gabata ya nuna cewa takardar digiri da takardar NYSC da Ministan ke amfani da su duk na bogi ne.
An fara zargin Uche Nnaji da amfani da takardun bogi tun a watan Yuli 2023, lokacin da Shugaba Tinubu ya sa sunan Nnaji a cikin jerin ministoci 28 na farko da aka tura majalisar dattawa.
Bayan bayyanar wannan bincike a karshen makon jiya, yan adawa a Najeriya suka fara kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke Nnaji daga kujerar minista.
Hadimin Atiku ya nemi a kori Uche Nnaji
Da yake martani kan lamarin, hadimim Atiku, Paul Ibe ya ce bai kamata Shugaba Tinubu ya bar ministan a kan kujerarsa ba.
A cewarsa, ya dace Shugaban Kasa ya tsige ministan daga mukaminsa, sannan ya mika shi ga hukumomi domin a gurfanar da shi a gaban kuliya.
"Tun da Jami’ar Najeriya ta Nsukka (UNN) ta tabbatar da cewa Minista, Uche Nnaji na amfani da takardar shaidar digiri ta bogi, wacce ita ya gabatar lokacin da aka nada shi minista, bai kamata ya ci gaba da zama ba.
"Mu na tsammanin cewa Shugaba Bola Tinubu zai tsige shi daga mukaminsa tare da mika shi ga hukuma domin gurfanar da shi a gaban kotu."

Source: Twitter
Ministan Tinubu zai fito ya kare kansa
A wani rahoton, kun ji cewa Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji ya yanke shawarar fitowa ya kare kansa kan zargin da ake masa na amfani da takardun bogi.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ministan Tinubu zai fito bainar jama'a kan zargin amfani da digirin bogi
Bayanai sun nuna cewa Nnaji zai yi magana kan lamarin a taron manema labarai da ya kira a ranar Litinin, 6 ga watan Oktoba, 2025 a Abuja.
Hakan ma zuwa ne bayan an yiwa Ministan ca kan batun takardun bogi, lamarin da aka fara zarginsa da shi tun nada shi a mataayin Minista.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
