Sarki Ya Sacewa Atiku, El Rufai Guiwa kan Lamarin Siyasa, Ya ba Su Hakuri

Sarki Ya Sacewa Atiku, El Rufai Guiwa kan Lamarin Siyasa, Ya ba Su Hakuri

  • Sabon Sarkin Ibadan a jihar Oyo, Oba Rashidi Ladoja ya karbi bakuncin manyan yan siyasa a fadarsa
  • Sarkin ya gana da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai bayan nada shi a sarauta
  • Ladoja ya ce ya daina siyasa bayan nadinsa inda ya tuna alakarsa da Atiku da sauran yan siyasa a baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai sun ziyarci sabon Sarkin Ibadan.

Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja ya tarbe su cikin aminci da kuma mutuntawa a fadarsa da ke birnin Ibadan.

Atiku, El-Rufai sun ziyarci sabon Sarkin Ibadan
Atiku, El-Rufai da manyan yan siyasa yayin ziyartar Sarkin Ibadan. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Atiku, El-Rufai sun ziyarci sabon Sarkin Ibadan

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku ya tabbatar da kai ziyarar a yau Talata 30 ga watan Satumbar 2025 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Abuja ta zama abin tsaro, Tinubu ya ba da umarni bayan yi wa yar jarida kisan gilla

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin rubutun da ya yi, Atiku ya wallafa bidiyon jawabinsa a yayin ganawarsu da sauran manyan yan siyasa da suka halarci taron.

Rahoton Legit Hausa ya ce an nada sabon Sarkin ne a ranar Juma'a 26 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki.

Sarkin ya bayyana cewa ya rabu da siyasa bayan zama Olubadan, yayin karɓar manyan baƙi.

Sarkin Ibadan ya karbi bakuncin Atiku da El-Rufai
Ziyarar Atiku da El-Rufai a fadar sabon Sarkin Ibadan. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Abin da Atiku ya fadawa sabon Sarkin

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tare da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da sauran manya sun kai masa ziyara domin taya shi murna.

Oba Ladoja ya amsa da cewa ba dan siyasa ba ne yanzu, yana mai jaddada cewa zai yi hidima ga jama’ar Ibadan da Najeriya baki ɗaya.

Ya tuna irin dangantakarsa da Atiku a jam’iyyu daban-daban, yana cewa yanzu manufarsa ita ce tabbatar da adalci, da zaman lafiya ga al’ummarsa.

A cikin rubutunsa, Atiku ya ce:

"Da safiyar yau na jagoranci tawagar abokai da ’yan siyasa zuwa birnin tarihi na Ibadan, domin ziyarar taya murna ga Oba Rashidi Adewolu Ladoja Arusa I, Olubadan na 44 na Ibadan.

Kara karanta wannan

Girma ya fadi: Basarake ya rasa sarauta kan zargin satar tiransifoma 2

"A cikin tawagar akwai tsohon shugaban PDP, Sanata Iyorchia Ayu, tsohon gwamnan Jihar Cross River, Mista Liyel Imoke, tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, Malam Adamu Maina Waziri, tsohon Ministan Harkokin ’Yan sanda, da kuma Malam Kashim Imam.
"Na yi farin ciki matuka ganin yadda Olubadan ya kira kowanne daga cikinmu da sunanmu, yana tuna lokutan da muka yi tafiya tare wajen hidimar kasa.

Ya ce hakika, su da mai martaba sun shafe shekaru muna hidimar wannan kasa mai daraja domin kawo mata ci gaba.

Atiku ya bayyana rashin halartar nadin saboda batun tsari, yana cewa:

“Ba da gangan ba ne, muna ba da hakuri, kuma muna taya ka murna.”

Atiku, El-Rufai sun mutunta Rotimi Amaechi

Mun ba ku labarin cewa an daura auren dan tsohon ministan Sufuri a Najeriya, Rotimi Amaechi a cikin wani coci da ke Abuja.

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tare da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai sun samu damar halartar bikin.

Har ila yau, Gwamna Alex Otti na Abia da ministoci da kuma sanatoci ciki har da Sanata Simon Lalong da sauran manya na daga cikin mahalarta taron.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.