Yayin da Kwankwaso ke Taro a Kano, Barau Ya Janye 'Yan NNPP zuwa APC
- Wani rukuni na matasan NNPP da Kwankwasiyya daga yankin Danbatta a Kano sun shiga jam’iyyar APC a birnin Abuja
- Matasan sun ce sun gaji da yadda ake mu'amala da su a jam'iyyar NNPP, shi ya sa suka yi watsi da jar hular Kwankwasiyya
- Hakan na zuwa ne yayin da Rabiu Kwankwaso ya jagoranci taron shugabannin NNPP tare da karɓar masu sauya sheka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Siyasar jihar Kano ta dauki sabon salo yayin da matasa daga ƙaramar hukumar Danbatta suka bar jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya suka koma APC.
Wannan ya biyo bayan ziyarar da suka kai wa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin a ofishinsa da ke majalisar tarayya a Abuja.

Source: Facebook
Barau ya wallafa a Facebook cewa matasan da suka fito daga cikin masu ruwa da tsaki na NNPP a Danbatta, sun bayyana cewa sun gaji da zama a NNPP da Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan
Ana batun zaben 2027, Majalisar Dinkin Duniya ta aiko sako ga jam'iyyu da 'yan siyasar Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A daidai wannan lokaci kuma, a Kano, jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gudanar da taron shugabannin jam’iyyar a gidansa.
Matasan NNPP sun koma APC a Kano
Matasan da suka bar NNPP tare da watsi da alamar tafiyar Kwankwasiyya ta jar hula, sun samu rakiyar shugaban APC a Danbatta, Mohammed Liman, da kuma Alhaji Ado Rabiu Danbayero.
A yayin ganawar da aka yi a Abuja, matasan sun bayyana cewa sun shiga APC ne bayan matsalar da suka fuskanta a NNPP, musamman yadda suka rasa samun kulawa.
An shaida cewa sun yi watsi da hular Kwankwasiyya a bainar jama’a a matsayin alamar rabuwa daga tsohuwar tafiyarsu.
“NNPP ta kusa rushewa,” Barau Jibrin
Sanata Barau da ya karɓi matasan ya bayyana cewa matakin sauya sheƙar nasu alama ce ta yadda NNPP ke ƙara dusashewa a siyasar Najeriya.
Ya ce jam’iyyar APC ce babbar jam’iyya a yammacin Afirka, wadda ke da tsarin da zai tallafa wa matasa wajen ciyar da ƙasa gaba.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji
A cewarsa, NNPP tana kan hanyar rushewa, kuma lokaci ne kaɗan ya rage ta ɓace baki ɗaya daga doron siyasar Najeriya.

Source: Facebook
Kwankwaso ya gana da 'yan NNPP
A gefe guda, jagoran NNPP kuma tsohon ministan tsaro, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya shirya taron shugabannin jam’iyyar NNPP a gidansa da ke Miller Road, Kano.
Taron ya samu halartar manyan kusoshin jam’iyyar daga fadin jihar, inda aka tattauna kan makomar tafiyar kuma ya karbi wasu 'yan siyasa zuwa NNPP.
Hadimin Sanata Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a X cewa mutanen da suka sauya sheka sun fito ne daga APC.
'Yan CPC za su fara adawa da APC
A wani rahoton, kun ji cewa wasu shugabannin tsohuwar jam'iyyar CPC ta margayi Muhammadu Buhari sun gana da Atiku Abubakar.
Shugabannin sun bayyana goyon bayan su ga sabuwar tafiyar ADC domin kafa gwamnati a Najeriya a zaben 2027.
Sun koka da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta kauce daga manufar da aka kafa APC a kai domin tallafawa talakawan Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng