Ta Fara Tsami tsakanin Gwamna da Ministan Tsaro, APC Ta Fusata kan Lamarin
- Jam’iyyar APC ta gargaɗi mambobinta su guji tayar da fitintinu, musamman masu goyon bayan tsohon gwamna, Mohammed Badaru Abubakar
- An gargadi yaran da ake kira “Badaru Boys” da haddasa rikice-rikice a wuraren taruka da zaben cike gurbi
- Har ila yau, ana zargin yaran suna kuma ɓata sunan Gwamna Umar Namadi wanda hakan rashin ladabi ne
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - Jam’iyyar APC a Jigawa ta yi gargaɗi ga wasu mambobinta kan kokarin jawo hatsaniya a jihar.
Jam'iyyar ta bukaci mambobinta su guji rashin ɗa’a da halaye marasa kyau da za su iya kawo rabuwar kai.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar, Muhammad Dikuma Umar ya sa hannu wanda Aminiya ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin matsala tsakanin Badaru da Gwamna Namadi
Hakan ya biyo bayan zargin akwai matsala tsakanin Gwamna Umar Namadi da tsohon gwamnan jihar, Mohammed Badaru Abubakar.
A yanzu haka, Badaru shi ne babban ministan tsaro a Najeriya bayan Bola Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023.
Kamar yadda yake faruwa a wasu jihohi, an ce akwai alamun baraka ta barke a jam'iyyar APC da ke jihar Jigawa.
Wasu rahotanni sun ce alaka ta fara tsami tsakanin tsohon gwamnan jihar, Badaru Abubakar da Gwamna Umar Namadi.
Sai dai gwamnan jihar ya yi magana kan lamarin inda ya ce babu wata baraka musamman a jam'iyyar APC amma ya tabbatar wasu na kitsa ta.
APC ta fusata kan halayen yaran Badaru
Jam'iyyar ta ce wasu magoya bayan tsohon gwamna Mohammed Badaru Abubakar da ake kira “Badaru Boys” suna tayar da hankali.
An zargi “Badaru Boys” da rikice-rikice a Majiya da ke Gumel da zaben Babura/Garki, tare da cin fuska ga gwamnati a taron Kafin Hausa.

Source: Facebook
APC ta kare Gwamna Namadi a Jigawa
Jam’iyyar ta ce, duk da rashin ladabi, Gwamna Namadi ya yi haƙuri, amma ta koka da yadda tsohon gwamna bai tsawatar da magoya bayansa ba.
“Fitinar ‘Badaru Boys’ ta yi yawa, Wannan ɗabi’a… ta sabawa sashe na 21 na kundin tsarin mulkin APC."
- Cewar sanarwar
APC ta yi barazanar amfani da kundin mulki don ladabtarwa, ta kuma kira jami’an tsaro su dauki mataki don hana ɓarkewar rikicin siyasa.
Wasu na ganin wannan baraka na iya jawo matsala ga jam'iyyar a zaben 2027 da ake tunkara wanda yake da matukar tasiri.
Sai dai gaggawar daukar mataki da jan kunne zai iya kawo karshen matsalar da ke tunkarar APC a jihar.
Gwamna Namadi ya kwarara yabo ga Tinubu
Mun ba ku labarin cewa gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya ƙwarara yabo ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Umar Namadi ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya nuna jarumtaka wajen ɗaukar matakan da waɗanda suka gabace shi suka kasa ɗauka.
Ya nuna cewa matakan da Tinubu ya ɗauka sun taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya wanda ya kama hanyar durƙushewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

