Ana Zargin Alaka Ta Yi Tsami Tsakanin Namadi da Badaru, Gwamna Ya Magantu

Ana Zargin Alaka Ta Yi Tsami Tsakanin Namadi da Badaru, Gwamna Ya Magantu

  • Kamar yadda yake faruwa a wasu jihohi, akwai alamun baraka ta barke a jam'iyyar APC da ke jihar Jigawa
  • Wasu rahotanni sun ce an alaka ta fara tsami tsakanin tsohon gwamnan jihar, Badaru Abubakar da Gwamna Umar Namadi
  • Sai dai gwamnan jihar ya yi magana kan lamarin inda ya ce babu wata baraka musamman a jam'iyyar APC amma ya tabbatar wasu na kitsa ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Jigawa - Wasu rahotanni sun fara bullowa a jihar Jigawa kan zargin rigima tsakanin tsohon gwamna, Badaru Abubakar da Umar Namadi.

Akwai abubuwa da ke faruwa da ake ganin sune silar rigimar musamman daga bangaren gwamnan da mai gidansa.

Ana zargin rigima tsakanin Badaru da Gwamna Namadi
Wasu na hasashen alaka ta fara tsami tsakanin Gwamna Umar Namadi da Badaru Abubakar. Hoto: Umar Namadi, Ministry of Defence.
Asali: Facebook

Abubuwa da ake zargin sanadin rigimar Namadi, Badaru

Wani rahoton Vanguard ya ce lamarin ya faro ne tun lokacin kaddamar da yan Majalisa a jihar da zaben kakakinta a watan Yunin 2023.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba da umarnin rufe makarantu saboda mutuwar Sanata, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin wata ganawa, an amince za a zabi Idris Garba kakakin Majalisar wanda daga bisani gwamnan ya sauya ra'ayi inda ya goyi bayan Haruna Dangyatin wanda bai yiwa masoyan Badaru dadi ba.

Daga bisani an yi kokarin tsige kakakin Majalisar wanda ya sha da kyar, a kokarin daukar fansa a wancan lokaci inda Dangyatin ya dakatar da wasu ciyamomi da ake ganin yaran Badaru ne kan zargin badakala.

Jaje kan fashewar tankar mai a Jigawa

Bayan fashewar tankar mai da ta yi ajalin mutane da dama a karamar hukumar Taura, Badaru ya tura tawaga inda ya ba da gudunmawar N20m ba tare da kula gwamnatin jihar ba kamar yadda wasu suka yi.

Hakan ya batawa na kusa da gwamnan rai da suke ganin Badaru na kokarin kaskantar da mai gidansu, cewar Premium Times.

Wata kungiyar APC Vanguard ta zargi Badaru da mu'amala da wasu yan adawa inda ta ce hakan babbar barazana ce ga jam'iyyar a kowane mataki.

Kara karanta wannan

'Tinubu bai san ya aka yi ba': Ganduje ya fadi yadda suka yi nasara a zaben Ondo

Shugaban Kungiyar, Salisu Yakubu ya bukaci Bola Tinubu ya taka masa birki ka da abin da ya faru da Goodluck Jonathan a 2015 ya maimaita kansa.

Gwamna Namadi ya magantu kan rikicin APC

Gwamna Namadi ya magana kan zargin matsala a APC bayan dawowa daga hutun makwanni uku inda ya ce babu matsala a jam'iyyar.

Ya tabbatar da cewa bayan ba shi nan abubuwa da dama sun faru inda ya koka kan yadda wasu ke kokarin kawo rigima tsakanin yan jam'iyyar.

An mika rahoton iftila'in gobara a Jigawa

Kun ji cewa Gwamnatin Jigawa ta karbi rahoton kwamitin da ta kafa domin binciken matsalar faduwar tankar fetur a jihar.

Hakan ya biyo bayan iftila'in fashewar tankar mai wanda ya yi sanadin al'umma da dama a karamar hukumar Taura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.