Tazarce 2027: Tsohon Gwamna Zai Jagoranci Yakin Neman Zaben Tinubu a Jihohi 6

Tazarce 2027: Tsohon Gwamna Zai Jagoranci Yakin Neman Zaben Tinubu a Jihohi 6

  • Tsohon Gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode, ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
  • Ambode ya ce Shugaba Tinubu ya cancanci ya koma mulki ya yi wa'adi na biyu, domin ya karasa ginin da ya riga ya dora harsashinsa
  • Tsohon gwamnan ya ce zai jagoranci yakin neman zaben Tinubu a jihohi 6, kuma shi kansa zai sake tsayawa takarar gwamnan Legas

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Tsohon Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya bayyana goyon bayansa ga shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaben 2027.

Ambode ya bayyana hakan ne a Badagry, da ke Legas, yayin wani shiri na wayar da kan jama’a kan rajistar katin zabe (PVC).

Tsohon gwamna, Akinwunmi Ambode ya ce zai goyi bayan tazarcen shugaba Tinubu a 2027
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya na tsaye a zauren majalisar FEC, yayin da ake shirin fara taron majalisar a Abuja. Hoto: @DOlusegu
Source: Twitter

An wayar da kan jama'a kan katin zabe

A wajen taron, tsohon gwamnan ya bukaci mazauna yankin Badagry da su yi rajista, domin mallakar katin kada kuri'a a 2027, kamar yadda The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin baiwa jihar Legas fifiko wajen ayyukan raya kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ta bakin daraktan kungiyar goyon bayan Tinubu-Ambode, Dr. Seyi Bamigbade, tsohon gwamnan ya ce shugaba Tinubu ya cancaci tazarce.

Ambode ya ce Tinubu ya samar da aza harsashe mai karfi na gina al'umma kuma ya cancanci wa’adi na biyu don karasa ginin da ya riga ya fara.

Ambode ya roki ‘yan Najeriya su zabi Tinubu

Ya kuma yi kira ga mazauna Legas da ‘yan Najeriya baki daya da su tabbatar sun sake zabar Tinubu a 2027, "domin mu duka mu ci gaba da amfana da nasarorin mulkinsa."

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa:

“Ina kira ga mazauna Legas da ‘yan Najeriya baki daya da su tabbatar ya samu wa’adi na biyu a 2027 domin mu duka mu ci gaba da cin gajiyar shugabancinsa.
"Dangane da jihar Legas kuwa, zan sake amsa kiran jama'a na yin takara, wannan zai ba ni damar dasawa daga nasarorin da aka samu a baya tare da magance matsalolin da ake fuskanta yanzu."

Kara karanta wannan

'Ko a jiki na': Tinubu ya yi martani mai zafi kan harajin Trump ga Najeriya, ya samo mafita

Tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode ya ce zai jagorancin yakin neman zaben Tinubu a Kudu maso Yamma a 2027
Tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode tare da Shugaba Bola Tinubu a wajen wani taro. Hoto: @AkinwunmiAmbode
Source: UGC

Ambode zai jagoranci yakin zaben Tinubu

Tsohon gwamnan ya kuma ce zai ci gaba da wayar da kan jama'a game da yin rajistar katin zabe, a wani bangare ne na kokarin nemawa Tinubu kuri'u a Kudu maso Yamma.

Jaridar Vangaurd ta rahoto Ambode ya yi alkawarin cewa zai jagoranci yakin nemawa Tinubu kuri'u a jihohin shiyyar shida, domin ganin ya samu tazarce a 2027.

A wajen taron, Dr. Seyi Bamigbade, ya ce:

“Mun yi imanin cewa Shugaba Tinubu da Mista Ambode su ne ke fafutukar ganin ci gaban jama'a, kuma za su yi shugabanci da zai amfani mutane."

Taron ya samu halartar shugabannin al'umma, kungiyoyin matasa, da masu ruwa da tsaki wadanda suka yi alkawarin ba da goyon baya ga Shugaba Tinubu da Ambode a zabukan da ke tafe.

Ambode ya magantu kan komawa ADC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode, ya kawo karshen jita-jitar da ake yadawa cewa zai bar APC zuwa ADC.

Kara karanta wannan

'Ba Jonathan ba ne,' Malami ya ce mutane 3 ne za su iya kayar da Tinubu a 2027

Ambode ya ce rahotannin da ake yada wa cewa zai watsar da tafiyar Shugaba Bola Tinubu, ya shiga hadakar 'yan adawa karkashin ADC, ba gaskiya ba ne.

Tsohon gwamnan jihar na Legas ya ce har gobe yana tare da Tinubu, kuma zai goyi bayan tazarcen shugaban kasar a zaben 2027 mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com