2019: Abinda ya sa Tinubu ya juyawa Ambode baya

2019: Abinda ya sa Tinubu ya juyawa Ambode baya

- Bayan an dade ana rade-radin akwai rashin jituwa tsakanin jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, yanzu abubuwa sun fara fitowa fili

- Shugaban jam’iyyar APC a jihar Legas, James Odumbaku, da tsohon kwamishinan noma, Kaoli Olusanya, sun shawarci Ambode ya mayar da fam dinsa na takara ko a tsige shi

- A satin da ya gabata ne aka fara yada jita-jitar cewar Ambode na shirin fita daga APC, kafin daga bisani ya musanta hakan

A satin da ya gabata ne kafafen yada labarai suka wallafa rahoton cewar gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, na duba yiwuwar ficewarsa daga APC saboda sabanin da ya shiga tsakaninsa da jagoran jam’iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya juyawa gwamna Ambode baya ne saboda canja wasu dokoki da ya yi bayan ya hau mulki a 2015, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

2019: Abinda ya sa Tinubu ya juyawa Ambode baya
Tinubu da Ambode
Asali: UGC

Rashin jituwar dake tsakanin Tinubu da Ambode ta kara fitowa fili ne bayan wasu jiga-jigan ‘yan APC a jihar Legas da suka hada da mataimakin jam’iyyar APC na Legas, Cardinal James Odumbaku, da tsohon kwamishinan noma, Kaoli Olusanya, sun umarci Ambode ya mayar da fam din takarar da ya saya ko kuma a tsige shi daga kujerar gwamna. Odumbaku da Olusanya sun fadawa Ambode hakan ne ranar Litinin da daddare a wurin taron da suka yi a Otal din Watercress dake Ikeja.

DUBA WANNAN: 2019: Manyan 'yan siyasa a Kano sun yi mubaya'a ga Kwankwaso

Rahotanni sun bayyana cewar yayin taron, dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar Legas 20 da na hukumomin raya jihar 37 (LCDAS), sun saka hannun goyon bayan dan takarar da Tinubu ke so, Mista Babajide Sanwo-Olu.

Jagorororin jam’iyyar APC a jihar Legas sun ce ba zasu goyi duk dan takarar da bashi da goyon bayan tsohon gwamna Tinubu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng