"Babu Wani Makirci": Kwankwaso Ya Yi Magana kan Tazarcen Tinubu a 2027

"Babu Wani Makirci": Kwankwaso Ya Yi Magana kan Tazarcen Tinubu a 2027

  • An samu hargitsi a cikin 'yan kwanakin nan a wajen wasu tarurruka da 'yan adawa suka jagoranta
  • Wani jigo a jam'iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa akwai makircin da ake kokarin kullawa Shugaba Bola Tinubu
  • Sai dai, ya nuna cewa duk wasu 'yan kulle-kullen da ake yi, ba za su bata sunan mai girma Bola Tinubu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Jigo a jam'iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi magana kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa babu wani nau’in batanci ko makirce-makircen siyasa, da zai hana Shugaba Tinubu yin tazarce.

Kwankwaso ya tabo batun tazarcen Tinubu
Hotunan Musa Iliyasu Kwankwaso da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Musa Iliyasu Kwankwaso, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan yayin da yake martani kan rigingimun siyasa da aka samu a cikin 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

APC ta kare salon mulkin Tinubu yayin da shugabannin siyasa a Arewa ke koka wa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An farmaki tarurrukan 'yan adawa

A ranar Litinin, 'yan daba sun kai hari kan jerin motocin tsohon ministan shari'a kuma jigo a jam'iyyar ADC, Abubakar Malami, inda suka lalata motoci guda 10.

Hakazalika, a ranar Lahadi, ‘yan daba sun tarwatsa wani taro na shugabannin jam’iyyar ADC a jihar Kaduna.

Me Musa Kwankwaso ya ce kan Tinubu?

Sai dai a martaninsa, Kwankwaso ya ce lamarin na da nasaba da siyasa, kuma an yi shi ne da nufin bata sunan Shugaba Tinubu tare da rage masa damar samun nasarar sake zama shugaban kasa, rahoton jaridar The Nation ya ruwaito.

"An yi shugabannin kasa daga Arewacin Najeriya da dama kafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Kwanan nan Buhari ya yi shekara takwas, amma yanzu mutane sun fara maganar an yi watsi da Arewa."
"Dukkanmu mun san abin da ya faru a lokacin Buhari. Ana samun ci gaba da fuskar tsaro a mulkin Tinubu. Yanzu hanyar Kaduna zuwa Abuja tana da aminci. Ana fatattakar 'yan bindiga a jihohin Arewa maso Yamma."

Kara karanta wannan

Siyasa ta fara tsami: An farmaki ministan Buhari a Kebbi, APC ta ɗauki zafi kan lamarin

"Ayyukan Boko Haram sun ragu a Arewa maso Gabas. Godiya ga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, wanda baya gajiyawa."
“Wadannan zarge-zargen kai hare-hare ga shugabannin adawa da ake dorawa kan APC, makircin siyasa ne da aka kulla domin batawa shugaban kasa suna kafin zaɓen 2027."
“Amma ayyukan Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su ci gaba da yin magana a madadinsa. Akwai ayyukan ci gaba masu yawa da ake yi a sassa daban-daban na Arewacin kasar nan."
"Yan Arewa sun samu manyan mukamai. Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, duk 'yan Arewa ne."

- Musa Iliyasu Kwankwaso

Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi magana kan Tinubu
Hoton jigon a jam'iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso Hoto: Musa Iliyasu Kwankwaso
Source: Facebook

Musa Kwankwaso ya soki Naja'atu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ragargaji 'yar gwagwarmaya, Hajiya Naja'atu Muhammad.

Musa Kwankwaso ya bayyana Naja'atu a matsayin yar hassada wadda ta ke mutuncin manyan mutane a Najeriya.

Jigon na APC ya zarge ta da zagin tsofaffin shugabannin kasa, Goodluck Jonathan da Olusegun Obasanjo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng