El Rufai Ya Tsokano Ministan Abuja bayan Ya Yi Hasashen Makomar Tinubu a Zaben 2027

El Rufai Ya Tsokano Ministan Abuja bayan Ya Yi Hasashen Makomar Tinubu a Zaben 2027

  • Ga dukkan alamu kalaman tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ba su yiwa ministan Abuja, Nyesom Wike dadi ba
  • El-Rufai ya ce a lissafin da ya buga, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba zai samu nasara a zaben 2027 ba, amma zai zo na uku
  • Wike ya soki wannan hasashe na El-Rufai, yana mai cewa ya kamata tsohon gwamnan ya bayyana na daya da na biyu domin cika lissafi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kalubalanci tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, kan hasashen da ya yi game da zaben 2027.

Mista Wike ya yi fatali da kalaman El-Rufa'i, wanda ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai zo na uku a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Ku daina": El Rufai ya shawarci Amaechi da Peter Obi kan takarar shugaban kasa

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Hoton ministan Abuja, Nyesom Wike yayin da yake jawabi a wurin taro Hoto: @GovWike
Source: Facebook

The Cable ta rahoto cewa Wike ya yi martani ga tsohon gwamnan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a Abuja ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane hasashe El-Rufai ya yi kan zaben 2027

Tun farko, tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai, a wata hira da Channels TV, ya yi hasashen cewa jam’iyyar APC za ta yi rauni a zaben 2027.

A cewar Malam El-Rufai, a lissafin da ya yi babu ta yadda shugaban kasa zai samu damar yin tazarce.

“Tinubu zai zo na uku a zaben 2027. Na yi lissafina kuma zan iya tabbatar maku cewa babu wata hanya da zai samu nasara.
"Ina tunanin ma babu wanda zai samu nasara a zaben da za a yi a zagayen farko.

Wannan furuci na El-Rufai ya jawo cece-kuce a cikin APC da wajen ta, inda wasu ke kallon sa a matsayin gargadi, yayin da wasu ke ganin ya yi gaggawa.

Kara karanta wannan

'Ban taba abokantaka da Uba ba,' El Rufa'i ya fadi alakarsa da gwamnan Kaduna

Ministan Abuja ya maida martani ga El-Rufai

A martanin da ya mayar, Wike ya bayyana cewa El-Rufai bai yi cikakken hasashe ba, saboda ya ce Tinubu zai zo na uku amma bai bayyana wanda zai zo na ɗaya da na biyu ba.

“El-Rufai abokina ne, amma a wannan lissafin ya yi kuskure. Idan ya san Tinubu zai zo na uku, to ya kamata ya fada mana wanda zai zo na daya da na biyu,” in ji Wike.
Ministan Abuja, Nyesom Wike da El-Rufai.
Hoton ministan Abuja, Nyesom Wike da na tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @Govwike, @elrufai
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa ko da yake ya yarda da gaskiyar El-Rufai wajen bayyana ra’ayinsa, akwai bukatar ya tabbata cewa duk lokacin da yake magana yana dogaro da sahihin bayani.

“A wannan batun zan yi fariya, ina da yakinin cewa Shugaba Tinubu ne zai ci zaben 2027, ban sani ba ko zai yarda da ni," in ji Wike.

Ministan Abuja ya caccaki hasashen El-Rufai

A wani labarin, kun ji cewa Nyesom Wike ya bayyana cewa ganganci ne babba PDP ta dawo da tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: El Rufai ya fallasa abin da gwamnatin Tinubu ke yi wa 'yan bindiga

Ministan harkokin Abuja ya ce dawowar Obi PDP babbar matsala ce da ka iya karasa ruguza jam'iyyar gaba daya.

Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas, ya sake jaddada cewa PDP ba ta koyi darasi daga kuskuren da ya jawo mata rashin nasara a zaben 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262