An Zo Wajen: Wike Ya Fadi Lokacin da Gwamna Fubara Zai Dawo kan Mulki a Rivers

An Zo Wajen: Wike Ya Fadi Lokacin da Gwamna Fubara Zai Dawo kan Mulki a Rivers

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya kada kuri'arsa a zaben kananan hukumomin jihar Rivers
  • Nyesom Wike ya yaba kan yadda zaben yake gudana cikin kwanciyar hankali da lumana a sassa daban-daban na jihar
  • Ministan ya kuma nuna cewa akwai yiwuwar Gwamna Siminalayi Fubara da 'yan majalisar dokokin jihar su koma kan kujerunsu a watan Satumba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan lokacin dawowar Gwamna Siminalayi Fubara kan mukaminsa.

Nyesom Wike ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara tare da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma bakin aikinsu ranar 18 ga watan Satumban 2025, lokacin da dokar ta-baci a Rivers za ta kare.

Wike ya yabi zaben kananan hukumomin Rivers
Hotunan ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara Hoto: @GovWike, @SimFubaraKSC
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Wike ya faɗi haka ne a ranar Asabar, jim kaɗan bayan ya kada kuri’arsa a zaɓen kananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Ministan Tinubu ya fadi lokacin kawo karshen matsalar rashin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya kada kuri'a a zaben Rivers

Ministan ya kada kuri’a a rumfar zaɓe ta bakwai, mazaba ta tara a kauyen Rumuepirikom, karamar hukumar Obio-Akpor.

Bayan ya kada kuri’a, Wike ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan rashin fitowar jama’a da kuma rashin amfani da na’urar tantance masu kada ƙuri’a (BVAS) a zaɓen.

"Ina matukar farin ciki. Wannan yana nuna cewa jama’a sun amince da zaɓen. Ba ku ji labarin tashin hankali ba, ba ku ji labarin ɗaukar akwatin kada kuri’a ba."
"Kamar yadda ku ke gani, kayan zaɓe sun iso, mutane suna nan suna kada ƙuri’a. A ganina wannan zaɓe yana gudana cikin lumana.”

- Nyesom Wike

Dangane da rashin amfani da BVAS, Wike ya ce hakan bai rage ingancin zaɓen ba, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar da wannan.

"Tabbas, mun damu da karancin fitowar jama’a, amma mutane suna ci gaba da fitowa. Kafin zaɓe ya ƙare, za ku ga adadin masu kada ƙuri’a ya ƙaru. Don haka muna farin ciki ƙwarai da yadda wannan zaɓe ya gudana cikin nasara da lumana."

Kara karanta wannan

Harin masallaci: Gwamna Radda ya ziyarci kauyen Mantau, ya dauki alkawura

- Nyesom Wike

Yaushe gwamna Fubara zai dawo kan mulki?

Ministan ya danganta nasarar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da yiwuwar janye dokar ta-baci da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana a jihar a farkon shekarar nan.

Wike ya kada kuri'a a zaben kananan hukumomin Rivers
Hoton Nyesom Wike yana kada kuri'a a zaben kananan hukumomin Rivers Hoto: @OlayinkaLere
Source: Twitter

Ya ce idan ba a gudanar da zaɓen kananan hukumomi karkashin dokar ta-baci ba, hakan zai sanya ba za a samu shugabanci ba a matakin kasa bayan janye dokar.

"Ma’anar wannan zaɓe shi ne ku sani cewa daga ranar 18 ga Satumba, dokar ta-baci za ta kare, gwamna da ’yan majalisar dokokin jiha za su koma bakin aikinsu."
"Kuma ku tuna cewa Kotun Koli ta soke zaɓen da ya gabata. Idan aka kasa gudanar da wannan zaɓe, hakan zai nuna babu mulki a matakin kananan hukumomi.”

- Nyesom Wike

Hadimin Wike ya caccaki jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai magana da yawun bakin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

2027: Amaechi ya sha sabon alwashi kan takarar shugaban kasa karkashin ADC

Lere Olayinka ya soki PDP ne kan matakin da ta dauka na kai tikitin shugaban kasa zuwa yankin Kudu a zaben 2027.

Ya bayyana cewa jam'iyyar ta makara domin tun a zaben 2027 ya kamata ta yi hakan, lokacin da Wike ya ba ta shawara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng