Tinubu na Fuskantar Barazana, An Mika wa INEC Bukatar Kafa Sabuwar Jam'iyyar Adawa

Tinubu na Fuskantar Barazana, An Mika wa INEC Bukatar Kafa Sabuwar Jam'iyyar Adawa

  • Shugaba Bola Tinubu na fuskantar sabon kalubale yayin da Dakta Aliyu Audu ya mika bukatar kafa sabuwar jam’iyya a INEC
  • Dakta Aliyu Audu ya bayyana cewa ARC za ta kasance kwale-kwalen ceto Najeriya daga rashawa da shugabannni marasa nagarta
  • Audu wanda tsohon hadimin Tinubu ya yi alkawari cewa jam'iyyar ARC za ta yi shugabanci bisa gaskiya, hangen nesa, da bin doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Bayan ADC, PDP da sauransu, Shugaba Bola Tinubu na fuskantar sabuwar barazana yayin da ake shirin kafa sabuwar jam'iyyar adawa.

Yayin da zabukan 2027 ke gabatowa, Dakta Aliyu Audu, tsohon mai ba Tinubu shawara kan harkokin jama'a, ya gabatar da bukatar kafa jam'iyyar ARC.

Tsohon hadimin Tinubu, Dakta Aliyu Audu ya aika wa INEC bukatar kirkirar sabuwar jam'iyyar siyasa, ARC.
Wasikar da Dakta Aliyu Audu ya aika wa shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ta bukatar rajistar jam'iyyar ARC. Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Ana shirin kafa sabuwar jam'iyyar siyasa

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa tuni Dakta Aliyu Audu ya mika wa hukumar INEC takardar bukatar rajistar jam'iyar ARC, watau African Renaissance Congress.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kadu da Allah ya yiwa tsohon gwamna kuma jigon APC rasuwa a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon hadimin Tinubu ya aika wasikar bukatar rajistar sabuwar jam'iyyar ga shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar 22 ga Agusta, 2025.

Dakta Aliyu Audu, wanda shi ne shugaban kungiyar ARM, ya bayyana jam'iyyar ARC a matsayin dandalin da za a ceto 'yan Najeriya da kasar baki daya.

A madadin wadanda suka kafa ARM da kwamitin amintattunta, Dakta Audu ya ce sun kirkiri jam'iyyar ARC bayan nazarin jirgin Annabi Nuhu, da ya ceci mutane lokacin Dufana.

Dalilin son kafa sabuwar jam'iyyar ARC

Ya bayyana cewa Najeriya, wacce ya ce ita ce ruhin Afrika, na kan kwale-kwalen da ke tangal tangal zai nutse a teku saboda rashawa da gurbatattun shugabani.

A cewarsa, kamar yadda jirgin Annabi Nuhu ya ceci mutane da dabbobi a lokacin ruwan Dufana, haka ARC take da burin ceto Najeriya ta fuskar tattali, siyasa da ci gaban jama'a.

Shugaban ARM ya ce jam'iyyar ARC na da burin ceto Najeriya a 2027 ta sabon salon shugabanci mai cike da kwarewa, hangen nesa, kyankyasar shugabanni masu adalci, samar da ci gaba na dogon karni, da sauransu.

Kara karanta wannan

Kungiyar APC ta gargadi Tinubu kan sauya Shettima, ta fadi barazanar da ke tafe

Dakta Aliyu Audu ya kara da cewa, ARC na neman ba ’yan Najeriya sabuwar jam'iyyar siyasa da aka gina ba kan son rai ba, sai dai kan ƙa’idoji, hangen nesa da kuma tasirin da za a iya tabbatarwa.

Dakta Aliyu Audu ya ce sabuwar jam'iyyar ARC za ta kasance kwale-kwalen ceto 'yan Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da tsohon hadiminsa, Dakta Aliyu Abdu. Hoto: @MrOgbuanu
Source: Twitter

Sabuwar jam'iyyar ARC za ta kiyaye doka

Jaridar Daily Post ta rahoto shugaban ARM ya na cewa:

“ARC na ƙoƙarin tabbatar da juyin-juya-halin matasa ta fuskar tunani da ɗabi’u, ta gyara yadda ake mulki, ta inganta kirkire-kirkire, da kuma kiyaye tsarin Allah mafi girma.”

Daga nan ya yi alkawari cewa ARC ta shirya yin aiki bisa cikakken bin Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima."

Sannan ARC za ta kiyaye Dokar Zaɓe ta 2022, ta kasance mai riko da gaskiya da amana da ake buƙata daga kowace jam'iyyar siyasa ƙarƙashin kulawar INEC.

Ana son kafa jam'iyyar TNN

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar siyasa ta TNN ta fara shirye-shiryen zama jam'iyya a Najeriya yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

A wata sanarwa da mai magana da yawun TNN, Mohammed Adah Shaibu, ya fitar a Kaduna, ya ce sun miƙa bukatar zama jam'iyya ga INEC.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa, watau INEC ta bayyana cewa ta samu sakon kungiyoyi 91 da ke son zama jam'iyyun siyasa a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com