Attahiru Jega da wasu manyan Najeriya sun kirkiri sabuwar jam'iyyar ceto Najeriya

Attahiru Jega da wasu manyan Najeriya sun kirkiri sabuwar jam'iyyar ceto Najeriya

  • Wasu jiga-jigai a Najeriya sun kirkiri sabuwar jam'iyya a Najeriya don ceto 'yan kasa baki daya
  • Attahiru Jega, tsohon shugaban INEC na daya daga cikin wadanda suka kirkiri sabuwar jam'iyyar
  • Jam'iyyar a cewarsu za ta zama runduna ta uku wajen ceto 'yan Najeriya daga wahalhalu

Gabanin babban zaben shekarar 2023, wasu fitattun ‘yan Najeriya sun kafa runduna ta uku mai suna Rescue Nigeria Project (RNP).

Wadanda suka kafa RNP sun ce sun kaddamar da sabon tsarin siyasa ne domin baiwa 'yan Najeriya madadin jam'iyyar APC, da babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wadanda suka kafa RNP sun hada da tsohon gwamnan jihar Kwara; Ahmed Abdulfatai, tsohon dan takarar shugaban kasa, Farfesa Pat Utomi, tsohon ministan ilimi; Farfesa Tunde Adeniran da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023

Attahiru Jega da wasu manyan Najeriya sun kirkiri sabuwar jam'iyya
Farfesa Attahiru Jega | Hoto: dailytust.com
Asali: UGC

Sauran sun hada da tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta; Farfesa Attahiru Jega, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi; Yomi Awoniyi, Sanata Lee Maeba, Dr Usman Bugaje, Ambasada Nkoyo Toyo, Yomi Awoniyi, Dr Rose Idi Danladi, da sauran su.

Sai dai a bangare guda, Hon. Wale Oshun, shugaban Afenifere Renewal Group (ARG) ya bayyana cewa fatan samun runduna ta Uku a matsayin madadin manyan jam’iyyun siyasa biyu ba zai yi wani tasiri ba.

Rochas: Aikin sanata ya fi karfin albashin N13m duk wata, muna bukatar kari

Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya ce kusan Naira miliyan 13 da kowanne sanata ke samu a matsayin albashi da alawus-alawus bai kai wahalar aikin da 'yan majalisar ta dattawa ke yi ba.

Rochas wanda shi ma dan majalisar dattawa ne ya yi magana ne a wani taron manema labarai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba a Abuja, in ji rahoton The News.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon mataimakin gwamnan CBN da ya rasu

Tsohon gwamnan na Imo wanda ke gardama kan ya kamata a rage yawan sanatoci da aka zaba daga kowace jiha zuwa uku ya ce albashin sanata ya kai kimanin naira miliyan biyu tare da alawus na gida na naira miliyan uku da sauran alawus na kusan miliyan 11.

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

A wani labarin, Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kaca-kaca da shirin gwamnatin tarayya na ciyo sabon bashi na kasashen waje, kuma ci gaba da tara bashin ta'addanci ne, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce gwamnatin Buhari na tara basussuka ne ga masu zuwa a bayanta, yana mai bayyana hakan a matsayin "ta'addanci."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gabatar da bukatar neman amincewa don karbo sabbin basussuka na kasashen waje na $4.054bn da €710m ga majalisar kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel