2027: Gwamnonin PDP 8 Sun Tsayar da Abin da Suke Yi, Sun Nufi Jihar Zamfara
- Gwamnonin jam'iyyar PDP sun shirya gudanar da taro a jihar Zamfara ranar Asabar, 23 ga watan Agusta, 2025 a jihar Zamfara
- Gwamna Dauda Lawal zai karbi bakuncin gwamnonin a yau Juma'a, inda za su halarci liyafar da aka shirya kafin taron da za su yi washe gari
- Ana ran gwamnonin jihohin Bauchi, Taraba, Filato, Bayelsa, Enugu, Adamawa, Osun da Oyo za su yi taro a garin Gusau a ranar Asabar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal zai ya karɓi bakuncin gwamnonin da aka zaɓa a karkashin jam’iyyar PDP domin gudanar da wani muhimmin taro a jihar Zamfara.
Kungiyar gwamnonin PDP ta shirya taron ne a ranar Asabar, 23 ga watan Agusta, 2025 a Jihar Zamfara, daya daga cikin jihohin da ke hannun jam'iyyar hamayya a yau.

Source: Twitter
Gwamnoni PDP 8 za su dura jihar Zamfara
Rahotan Leadership ya bayyana cewa, ana sa ran gwamnonin PDP takwas za su isa Gusau, babban birnin Zamfara da yammacin yau Juma’a, 22 ga watan Agusta, 2025.
Gwamnonin za su hadu da Gwamna Dauda Lawal domin halartar liyafa ta musamman kafin taron da aka tsara zai gudana da safiyar ranar Asabar.
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a Gusau.
Sanarwar ta bayyana cewa, gwamnonin PDP za su tattauna muhimman dabarun siyasa yayin da suke kokarin shawo kan kalubalen rikicin da ake ciki a jam'iyyar a yanzu.
Abubuwan da gwamnonin PDP za su tattauna
“Gwamna Dauda Lawal na mika gaisuwa da maraba ga takwarorinsa, gwamnonin jam’iyyar PDP da za su hallara a Zamfara domin taron kungiyar gwamnonin PDP."
"Za a gudanar da liyafa ta musamman da Gwamna Dauda Lawal ya shirya wa gwamnonin a daren yau, kafin taron sirri da aka tsara yi idan Allah ya kaimu gobe.

Kara karanta wannan
An dauki gwamna 1 a Najeriya, an ba shi lambar yabo ta 'Zabin Jama'a' a kasar Faransa
“Taron zai ba jagororin jam’iyyar damar tattauna batutuwan siyasa masu muhimmanci, tsara matakan hada kan PDP, da kuma yadda za su kawo ci gaba a jihohinsu.
"Za su tattauna kan batutuwan da suka shafi shirin babban taron PDP na kasa da aka shirya a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025.”
- In ji Sulaiman Bala Idris.

Source: Twitter
Gwamnonin da ake sa ran za su isa Zamfara
Gwamnoni takwas da ake sa ran Gwamna Dauda zai karbi bakuncinsu sun hada da Bala Mohammed (Bauchi), Agbu Kefas (Taraba), Caleb Mutfwang (Filato) da Seyi Makinde (Oyo).
Sauran su ne, Ademola Adeleke (Osun), Douye Diri (Bayelsa), Peter Mbah (Enugu), da Ahmadu Fintiri (Adamawa), kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Gwamnonin PDP 2 sun amince da tazarcen Tinubu
A wani labarin, kum ji cewa gwamnonin jam'iyyar PDP guda biyu sun fito karara sun bayyana goyon bayansu ga tazarcen Bola Tinubu a 2027.
Gwamnonin sun tabbatar da cewa za su marawa Shugaba Tinubu domin ya kammala wa'adin mulki na biyu karkashin APC duk da ba jam'iyyarsu ɗaya ba.
Wannan dai na kara nuna yadda jam'iyyar PDP ke fama da rikicin cikin gida, wanda ya hana ta zama lafiya tun bayan zaben 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
