INEC: 'Dan Takara da ke Daure a Gidan Yari Ya Lashe Zaben Dan Majalisa a Najeriya

INEC: 'Dan Takara da ke Daure a Gidan Yari Ya Lashe Zaben Dan Majalisa a Najeriya

  • Zaben dan majalisar jihar Enugu mai wakiltar Enugu ta Kudu 1 na daya daga cikin zabukan da INEC ta gudanar ranar 16 ga watan Agusta, 2025
  • Hukumar INEC ta tabbatar da nasarar dan ta takarar jam'iyyar LP, Bright Emeka Ngene a wata sanarwa da ta fitar jiya Talata
  • Mista Ngene ya samu nasara duk da yana zaman gidan yari sakamakon hukuncin daurin shekaru bakwai da aka yanke masa a 2024

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Enugu - Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Bright Emeka Ngene na jam'iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zaben dan Majalisar dokokin Enugu a mazabar Enugu ta Kudu I.

INEC ta bayyana nasarar Ngene a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Sam Olumekun, ya fitar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kotu ta rufe asusun banki 4 da ake zargin na da alaka da tsohon shugaban NNPCL, Kyari

Bright Emeke Ngene.
Hotun Bright Ngene, dan takarar LP da ke zaman gidan yari Hoto: Rebecca Okpara
Source: Facebook

An sake zaben wannan mazaba ne bisa umarnin kotu a ranar 16 ga watan Agusta, 2025, kamar yadda INEC ta wallafa a shafin Facebook jiya Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda kotuna suka soke zaben dan Majalisar

Tun farko, Mista Ngene na LP ya lashe zaben dan Majalisar Enugu ta Kudu a watan Maris, 2023 amma kotun zabe ta soke, ta ba da umarnin shirya sabon zaben cikin kwanaki 90.

'Dan takarar LP ya sake lashe zaben har da wanda kotun daukaka kara ta umarci a canza, amma duk da haka aka kara sokewa.

Zaɓen da aka sake shiryawa a ranar 16 ga Agusta, 2025, a farko kamar ba zai yiwu ba saboda rashin isassun kayan zabe ciki har da takardun rubuta sakamako amma daga bisani INEC ta warware komai.

INEC ta sanar da sakamakon Enugu ta Kudu

A cikin sanarwar da hukumar INEC ta fitar, ta tabbatar da cewa Ngene ya samu mafi yawan ƙuri’u, inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Sam Ngene na PDP.

Kara karanta wannan

Kudin data, kira za su yi sauki, Tinubu ya dakatar da harajin 5% na kamfanonin sadarwa

“An gudanar da zaɓe a mazabu biyu da kotun daukaka kara ta bayar da umarni a jihohin Enugu da Kano. Bayan tashin hankali da ‘yan daba suka jawo a baya, yanzu zaɓen ya kammala.”
A mazabar Enugu ta Kudu 1, an ayyana Ngene Bright Emeka na jam'iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zaɓen," in ji sanarwar.

Ya bayyana cewa za a mika takardun shaidar cin zaɓe ga zababbun ‘yan majalisa a ranar 21 da 22 ga Agusta, 2025.

Zauren Majalisar Dokokin Enugu.
Hoton babbar kofar shiga harabar Majalisa dokokin jihar Enugu Hoto: Rebecca Okpara
Source: Facebook

Me yasa aka daure dan takarar LP a gidan yari?

Tun lokacin da ake takaddama kan zabensa, kotu ta yankewa dan takarar LP, Ngene hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari, cewar rahoton Premium Times.

An fara gurfanar da shi a kotu tun a 2017, tare da wasu mutane biyu, bisa tuhumar wawure Naira miliyan 15 mallakar al’ummar Akwuke da ke karamar hukumar Enugu ta Kudu.

A halin yanzu dai, Ngene na ɗaya daga cikin waɗanda ke zaman ɗaurin shekaru bakwai a gidan gyaran hali na jihar Enugu bayan hukuncin da aka yanke masa a 2024.

APC ta lashe kujerar dan Majalisa a Kano

Kara karanta wannan

Abubuwan 'tashin hankali' da aka gano a hannun mutane 333 da aka kama a zaben Kano

A wani rahoton, kun ji cewa INEC ta bayyana dan takarar jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Ghari/Tsanyawa ta jihar Kano.

Baturen zabe a mazabar, Farfesa Muhammad Waziri ya bayyana cewa Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar APC ya yi nasara da ƙuri’u 31,472.

Ya samu nasarar doke babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar NNPP, Yusuf Ali Maigado, wanda ya samu ƙuri’u 27,931.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262