Zaɓen Cike Gurbi: Albashi da Alawus na Ƴan Siyasar da Suke Shirin Shiga Majalisa
- 'Yan siyasar da aka zaba a zaben cike gurbi za su fara aiki, lamarin ya sake jawo muhawara kan albashi da alawus da suke karba bayan shiga majalisa
- Rahoto ya nuna Sanata na samun fiye da N1m a wata, ciki har da albashi, alawus na dindindin da kuma na wani lokaci wanda ke jawo magana a kasa
- Hakan ya biyo bayan gudanar da zaben cike gurbi a wasu jihohin Najeriya a ranar Asabar 16 ga watan Agustan 2025 domin maye gurbin wasu kujeru a kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - An gudanar da zaben cike gurbi a wasu jihohin Najeriya a ranar Asabar 16 ga watan Agustan 2025 domin maye gurbin wasu kujeru.
Sababbin wadanda da aka zaba a zabukan cike gurbi sun shirya fara aikinsu a majalisar dokoki ta tarayya bayan watanni suna harin mukaman.

Source: Facebook
Zaben cike gurbi: Za a samu sabbabbi 'yan majalisa
An sake fara tattaunawa kan albashi da kuma alawus-alawus da ake bai wa ‘yan majalisar, wanda wasu ke kallo a matsayin nauyi ga tattalin arziki bayan zaben cike gurbi, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya jawo bincike kan albashi da alawus na sanatoci da yan majalisar tarayya bayan zaben da aka gudanar a karshen makon jiya.
Wannan rahoton zai duba yawan albashi da alawus da yan majalisu suke dauka wanda suna daga cikin mafi samun albashi a duniya.
Yawan albashi, alawus na 'yan majalisa a Najeriya
Legit Hausa ta duba tulin albashin da kuma alawus na su yayin da sababbin yan majalisa ke shirin shiga tsarin.
Duk wata, Sanata na karɓar kimanin N1,063,860, wanda ya haɗa da albashi na N168,866.70 da wasu alawus na kullum da ake biya tare da shi.
Alawus na yau da kullum sun haɗa da N126,650 na man fetur da gyaran mota, N42,216.66 na mataimaka da N126,650 na ma’aikatan gida.

Kara karanta wannan
Abubuwan 'tashin hankali' da aka gano a hannun mutane 333 da aka kama a zaben Kano
Sauran kudin da 'yan majalisu ke karba
Haka kuma akwai N50,660 na nishaɗi, N50,660 na wutar lantarki, N25,330 na jaridu, N42,216.66 na sutura, da N8,443.33 na gyaran gida.
Mafi girma a ciki shi ne alawus ɗin mazabu mai darajar N422,166.66 wanda ake biya duk wata tare da albashin yau da kullum.
Wannan ya tabbatar da cewa tsarin biyan su ya haɗa da tsayayyen albashi da kuma wasu kudin da ake biya kai tsaye.

Source: Facebook
Kashe-kashen alawus na yan majalisu a Najeriya
Sai dai akwai bambanci tsakanin alawus na yau da kullum da na lokaci ɗaya, na kullum ana biya duk wata, yayin da wasu ana ba sau ɗaya cikin wa’adi.
Cikin alawus na lokaci ɗaya akwai alawus ɗin kayan daki N6,079,200 da ake biya sau ɗaya, da kuma kuɗin sallama na tsawon aiki N6,079,200, cewar BusinessDay.
Haka kuma, akwai alawus ɗin mota N8,105,600 wanda aka tsara shi a matsayin rance da dole ne a biya kafin barin ofis.
Wannan ya nuna yadda tsarin ya kunshi jerin tanade-tanade na kudi wanda ake ba yan majalisu a Najeriya duk da halin kunci da talakawa ke ciki.
Sababbin ‘yan majalisa da suka fito daga zabukan cike gurbi za su fara karɓar wadannan kuɗaɗe nan da nan bayan shiga ofis, wannan ya sake ta da batun gaskiya da ingancin tsarin majalisa.
Tattaunawa ta sake daukar hankali kan gaskiya, amana da kuma yiwuwar jurewa tsarin albashi mai nauyi, musamman ga tattalin arzikin Najeriya da talakawa ke dogaro da shi.
Mazabun da APC ta lashe a zaɓen cike gurbi
Mun ba ku labarin cewa an gudanar da zabukan cike gurbi a wasu jihohin Najeriya ne domin cike guraben kujerun wasu 'yan majalisu a Najeriya.
An yi zabukan ne domin maye gurbin kujerun da suka zama babu kowa, saboda murabus ko rasuwar wasu daga cikin mambobin majalisar tun bayan zaben 2023 da aka gudanar.
An fitar da sakamakon zabukam inda jam'iyyu da dama suka fatata, yayin da yan adawa suka lashe wasu kujeru, wannan rahoto ya zakulo muku mazabun da jam'iyyar APC ta lashe kan yan adawa a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

