Zabukan Cike Gurbi: Jerin Mazabun da Jam'iyyar APC Ta Lashe
FCT, Abuja - ’Yan Najeriya sun kada kuri’a a mazabu 16 da ke fadin jihohi 13 a zabukan cike gurbi da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Hukumar INEC dai ta gudanar da zabukan cike gurbin ne a ranar Asabar, 17 ga watan Agustan 2025.

Source: Facebook
Meyasa INEC ta yi zabukan cike gurbi?
Jaridar The Guardian ta ce an gudanar da zabukan ne domin cike guraben kujerun 'yan majalisa da suka zama babu kowa, saboda murabus ko rasuwar wasu daga cikin mambobin majalisar dokokin tarayya da na jihohi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zabukan cike gurbin sun shafi mazabu biyu na Sanata a jihohin Anambra da Edo, mazabu biyar na majalisar tarayya a jihohin Edo, Jigawa, Kaduna, Ogun da Oyo.
Hakazalika, zabukan sun shafi mazabu tara na majalisun dokokin jihohi a Adamawa, Anambra, Kaduna, Kano, Kogi, Neja, Taraba da Zamfara.
Jam'iyyar APC ta tumurmusa 'yan adawa
Jam’iyyar APC ta samu nasara a mazabu 12 daga cikin 16 da aka gudanar da zabukan cike gurbin na ranar Asabar.
Ga jerin wuraren da jam'iyyar APC ta samu nasara:
1. Mazabar tarayya ta Remo (jihar Ogun)
Hukumar zabe ta INEC ta bayyana 'yar takarar jam'iyyar APC, Mrs. Adesola Elegbeji, a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi na mazabar tarayya ta Remo a jihar Ogun, cewar rahoton The Punch.

Source: Twitter
Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Kazeem Bello, ya ce Elegbeji ta samu kuri’u 41,237, inda ta doke abokin hamayyarta mafi kusa, Bolarinwa Oluwole na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 14,324.
2. Mazabar Sanatan Edo ta Tsakiya (jihar Edo)
INEC ta bayyana Joseph Ikpea na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Sanata a Edo ta Tsakiya, cewar rahoton TheCable.
Jami'in tattara sakamakon zaben ya bayyana cewa Joseph Ikpea ya samu kuri’u 105,129, inda ya doke Joe Okojie na PDP wanda ya samu kuri’u 15,146.

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa APC ta lashe mafi yawan zabukan cike gurbi da aka yi a Kano da jihohi 12'
3. Mazabar tarayya ta Garki-Babura (jihar Jigawa)
Hukumar INEC ta bayyana Alhaji Mukhtar Rabiu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na mazabar majalisar tarayya ta Garki/Babura a jihar Jigawa.

Source: Facebook
Alhaji Mukhtar Rabiu ya samu kuri'u 38,449, inda ya doke abokin hamayyarsa na PDP, Auwal Isah Manzo, wanda ya samu kuri'u 13,159, rahoton Premium Times ya tabbatar.
4. Mazabar Basawa (jihar Kaduna)
INEC ta bayyana Alhaji Dahiru Umar-Sani na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Basawa a majalisar dokokin jihar Kaduna, cewar rahoton TheCable.
Jami’in tattara sakamakon zaben ya bayyana cewa Alhaji Dahiru Umar-Sani ya samu kuri’u 10,996, inda ya doke abokin hamayyarsa na PDP, Muazu Danyaro, wanda ya samu kuri’u 5,499
5. Mazabar Munya (jihar Neja)
INEC ta bayyana Mathew Dogari Daje, dan takarar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar Neja a mazabar Munya, cewar rahoton The Punch.
Mathew Dogari Daje ya samu kuri’u 12,556, inda ya doke abokin hamayyarsa na PDP, Sabo Sunday Adabyinlo, wanda ya samu kuri’u 5,646.
6. Mazabar Ghari/Tsanyawa (jihar Kano)
Jam'iyyar APC ta lashe zaben mazabar Ghari/Tsanyawa ta majalisar dokokin jihar Kano.
Hukumar INEC ta bayyana dan takarar APC, Yau Garba Gwarmai, a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri'u 31,472, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya doke abokin hamayyarsa na jam'iyyar NNPP, Yusuf Ali Maigado, wanda ya samu kuri'u 27,931.
7. Mazabar Zaria Kewaye (jihar Kaduna)
Jam'iyyar APC samu nasarar lashe zaben cike gurbi na mazabar Zaria Kewaye ta majalisar dokokin jihar Kaduna, cewar rahoton tashar Channels tv.
Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Balarabe Abdullahi, ya bayyana Isa Haruna Ihamo na APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 26,613.
8. Mazabar tarayya ta Ovia (jihar Edo)
INEC ta bayyana Omosede Igbinedion ta APC a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi a mazabar Ovia, cewar rahoton The Cable.
Jami’in tattara sakamakon, Farfesa Clement Ighodalo, ya ce Igbinedion ta samu kuri’u 77,053.
Dan takarar PDP, Johnny Aikpitanyi, ya samu kuri’u 3,838, yayin da dan takarar ADC, Dr. Sandra Asemota, ya samu kuri’u 925.
9. Mazabar tarayya ta Chikun/Kajuru (jihar Kaduna)
INEC ta bayyana Felix Bagudu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Chikun/Kajuru.
Felix Bagudu ya samu kuri’u 34,580, inda ya doke dan takarar PDP wanda ya samu 11,491, cewar rahoton tashar Channels tv.
Wannan shi ne karon farko da APC ta lashe wannan mazabar tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999.
10. Mazabar Ganye (jihar Adamawa)
INEC ta bayyana Misa Musa Jauro na APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar Adamawa a mazabar Ganye, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Tukur Ahmed, ya bayyana cewa Misa Musa Jauro ya samu kuri’u 15,923, inda ya doke dan takarar PDP wanda ya samu kuri’u 15,794.
11. Mazabar Karim Lamido I (jihar Taraba)
INEC ta bayyana Abner Shittu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na majalisar dokokin Taraba a mazabar Karim Lamido I, cewar rahoton Tribune.
Jami’in tattara sakamakon zaben, Dr. Mustapha Sa’ad, ya ce Abner Shittu ya samu kuri’u 5,895, inda ya doke dan takarar PDP, Ali Kanda, wanda ya samu 5,488, rahoton Vanguard ya tabbatar.
12. Mazabar Egume/Dekina (jihar Kogi)
Jam'iyyar APC ta lashe zaben cike gurbi na mazabar Egume/Dekina a majalisar dokokin jihar Kogi da hukumar INEC ta gudanar, cewar rahoton Daily Post.
Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Emmanuel Onoja Eneche, ya bayyana Musa Hassan Yakubu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 55,073.
Dan takarar PDP mai adawa a jihar da kasa, Godwin Meliga, ya samu kuri’u 1,038.
Bola Tinubu ya taya jam'iyyar APC murna
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya taya jam'iyyar APC murna kan nasarar da ta samu a zabukan cike gurbi.
Shugaba Tinubu ya kuma taya sauran 'yan takarar jam'iyyun adawa wadanda suka samu nasara a zabukan murna.
Hakazalika, ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan yadda ta gudanar da zaben cikin lumana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



