'Wannan Son Kai ne," Ana Zargin 'Yan Sanda Sun Tarwatsa Taron Jam'iyyar ADC a Ogun
- Jam’iyyar hadaka ta ADC ta zargi ’yan sanda da tarwatsa gangamin yakin neman zaben da ta shirya a jihar Ogun duk da ta nemi izini
- Shugaban ADC a Ogun, Femi Soluade ya ce 'yan sanda sun karya kujeru, sun kwace kayan sauti da girke tankar yaki a wajen taron
- Yayin da jam'iyyar ADC ta yi Allah-wadai da abin da ta kira son kai na ’yan sanda, ta kuma jaddada cewa babu abin da zai jijjiga ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun - Jam'iyyar ADC a jihar Ogun ta zargi rundunar 'yan sanda da tarwatsa taron yakin neman zabenta a Sagamu da ke jihar.
ADC ta ce ta shirya gangamin yakin neman zaben ne domin shirya wa zaben cike gurbi na kujerun 'yan majalisar tarayya a ranar Asabar.

Kara karanta wannan
PDP ta sacewa magoya bayan Jonathan da Obi guiwa da aka kafa kwamitin karba karba

Source: Twitter
'Yan sanda sun tarwatsa taron ADC
A rahoton da jaridar Punch ta fitar, shugaban ADC na Ogun, Femi Soluade ya bayyana cewa cewa 'yan sanda sun tarwatsa taron ne don amfanin APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Femi Soluade, jam'iyyar ADC bisa jagorancin sakatarenta na kasa kuma tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola sun nemi izinin 'yan sanda kafin hada taron.
Sai dai ya ce duk da neman izinin:
"An tarwatsa wurin taron, an cire mana rumfuna, an karya kujeru, an kwace kayan sauti, kuma an girke tankar yaki a wajen, duk don a hantari dan takararmu, shugabanninmu da masoyanmu."
Femi Soluade ya yi ikirarin cewa shugaban ofishin 'yan sanda na Sagamu, tare da A.C na shiyyar sun tare hanyar Aregbesola da shugaban ADC na Kudu maso Yamma, Rasaq Eyiowuawi da wasu kusoshin jam'iyya a Isale Oke, inda suka ba su umarnin komawa Abeokuta.
Jam'iyyar ADC ta caccaki aikin 'yan sandan
Shugaban jam'iyyar ya ce:
"Sun kawo wani uziri marar amfani, wai Gwamna Dapo Abiodun da mambobinsa na APC sun riga sun kama lungu da sakon yanki, ku ji fa, kamar dai filayen garin sun zama na APC?."
Jaridar Daily Trust ta rahoto jam'iyyar ADC ta yi Allah wadai da abin da ta kira "son kai, kuma abin kunya daga rundunar 'yan sanda," tana mai cewa babu abin da zai razana ta.
"Babu cin wani kalar cin mutunci, karya kujeru, kwace kayayyaki ko girke tankar yaki da zai iya dusashe muryar mutane.
"Muna fadawa 'yan sanda da babbar murya cewa, ku kasance masu biyayya ga dokar kasar kawai, ba wai 'yan siyasa ba. Ko ana muzuru ana shaho, ADC ta nan daram."
- Femi Soluade.

Source: Original
Ogun: APC ta gama yakin neman zabe
Kwamishinan 'yan sandan Ogun, Lanre Ogunlowo, da kakakin 'yan sandan, CSP Omolola Odutola, ba su ce komai game da wannan zargi na ADC ba.

Kara karanta wannan
'Za mu more': An faɗi dalilai da ke nuna Jonathan ne mafi dacewa da bukatun Arewa
A hannu daya kuma, jam'iyyar APC ta kammala yakin neman zabenta yayin da ta shirya shiga zaben cike gurbi na ranar Asabar mai zuwa.
Shugaban APC na kasa, Prof. Nentawe Yilwatda, yayin da yake jawabi a filin jirgin sama na Gateway da ke Sagamu, ya ce jihar Ogun ta APC ce.
"Duk wanda ya zabi wata jam'iyya da ba APC ba, to ya yi asarar kuri'arsa ne kawai."
- Prof. Nentawe Yilwatda.
'Suna son dakile farin jinin ADC' - Mark
A wani labarin, mun ruwaito cewa, muƙaddashin shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa, Sanata David Mark, ya yi zargi kan gwamnatin jam'iyyar APC.
David Mark ya nuna cewa akwai shirin da gwamnatin za ta yi domin ganin ta dusashe tauraruwar ADC wadda ke haskawa a halin yanzu.
Kalaman shugaban ADC din na zuwa ne yayin da aka samu wasu kwararrun lauyoyi da suka shirya kare jam'iyyar a kowace shari'a a faɗin Najeriya
Asali: Legit.ng
