'Mun Yi Allah Wadai': Atiku Ya Fadi 'Gaskiyar' abin da Ya Sa EFCC Ta Tsare Tambuwal
- Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da tsare Aminu Tambuwal, yana zargin EFCC da amfani da karfinta wajen gallaza wa ‘yan adawa
- Ya bayyana cewa gwamnatin APC na amfani da yaki da rashawa a matsayin makamin siyasa kan wadanda ba sa cikin jam’iyyarsu
- Yayin da ya aika sako ga kasashen waje, tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi gargadi kan mayar da Najeriya karkashin jam'iyya daya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da tsare Aminu Waziri Tambuwal da hukumar EFCC ta yi.
Atiku Abubakar ya ce EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Sokoton ne kawai saboda shi mamba ne a jam'iyyar hadakar 'yan adawa.

Source: Twitter
Tambuwal: Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a safiyar ranar Talata, Atiku ya ce wannan na daga cikin shirin gwamnatin Tinubu na cin zarafi da gallazawa 'yan adawa.

Kara karanta wannan
Ana jita jitar rashin lafiyar Tinubu, Sanata ya fadi halin da Shugaban kasa ke ciki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya sanar da cewa:
"Abin da ke faruwa a yanzu ya isa ya zama ishara a gare mu cewa gwamnatin Tinubu na amfani da hukumomin yaki da rashawa wajen gallaza wa 'yan adawa.
"Za mu zama shaida kan yadda a 'yan kwanakin nan wasu ke amfani da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a matsayin makamin cimma burin siyasa."
A cewar jagoran 'yan adawar, hukumar EFCC ta sauka daga turbar da aka dora ta da kuma tubalin da aka gina ta a lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo.
"Yan adawa na fuskantar barazana" - Atiku
Atiku Abubakar ya kuma nuna mamaki kan yadda duk mai kashi a gindinsa ya ke zama mai tsarki da zarar ya shiga jam'iyyar APC, ya hada kai da tsarin siyasar Shugaba Bola Tinubu.
"A yau, duk wanda yake tare da 'yan adawa to yana fuskantar barazanar tuhuma kan rashawa, amma, abin mamaki, da sun hade kai da Shugaba Bola Tinubu, sai a yafe zunubansu gaba daya," inji Wazirin Adamawa.
Ya ce sam ba haka ne ake gina shugabanci ba, kuma ba haka ne ake yaki da cin hanci da rashawa ba. Bal ma, a cewarsa, hakan na kara jawo satar dukiyar jama'a.
Dan takarar shugaban kasar na PDP a 2023 ya ce suna sane da yadda wasu gwamnonin PDP suka koma jam'iyya mai mulki saboda fargabar gamu da EFCC.

Source: Getty Images
"Dole mu yi Allah wadai" - Atiku Abubakar
Atiku ya ce lallai yaki da cin hanci da rashawa wani yaki ne da ke bukatar tallafi daga kowanne dan Najeriya, amma ya ce:
"Dole ne 'yan kasar nan da abokan kasar a kasashen waje su yi Allah wadai da amfani da wannan yaki wajen cimma wata manufa ta siyasa.
"Mun ga yadda a 'yan kwanakin nan aka rika amfani da hukumomin yaki da rashawa wajen tilasta wa shugabannin adawa komawa jam'iyya mai mulki."
Atiku ya ba 'yan Najeriya tabbacin cewa ba za su taba sallama wa irin wannan barazana ba, domin yin hakan tamkar an amince da mulkin mallaka ne na jam'iyya daya.
EFCC ta tsare Aminu Waziri Tambuwal
Tun da fari, mun ruwaito cewa, hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, kan zare Naira biliyan 180 daga banki ba bisa ka’ida ba.
An ji cewa cire kudaden da Tambuwal ya yi ya sabawa dokar yaki da safarar kudi ta 2022, kuma ana zarginsa da aikata hakan lokacin mulkinsa.
Aminu Tambuwal dai ya isa ofishin EFCC da safiyar Litinin, inda jami’an hukumar ke yi masa tambayoyi yayin da ake dakon karin bayani kan lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

