2027: Malamin Addini Ya Hango Kujerar Gwamnoni 7 da Ke Fuskantar Barazana
- Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya bayyana wasu alamu ga gwamnan jihar Akwa Ibom da wasu gwamnoni guda shida dangane da abin da za su iya fuskanta a zabukan gaba
- Ayodele ya yi wannan furuci ne yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da shirin babban zaben 2027, wanda ake sa ran za a gudanar da shi a watan Fabrairu na shekarar
- Haka zalika, malamin addinin ya shawarci shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da ya zama mai matukar taka-tsantsan da addu’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Asaba, jihar Delta - Primate Ayodele ya yi gargaɗi ga wasu gwamnoni dangane da burinsu na neman wa’adin mulki na biyu.
A wata sanarwa da mai taimaka masa a kafafen yada labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar kuma aka raba wa Legit.ng, malamin ya bayyana cewa komawar wadannan gwamnoni ofis ba tabbas ba ne.

Source: Facebook
Primate Ayodele ya lissafa wasu daga cikin jihohin da abin ya shafa da suka hada da Akwa Ibom, Cross River, Delta, Enugu, Ondo, Zamfara da Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Primate Ayodele ya gargadi gwamnoni 7
Ban da jihar Ondo, sauran jihohin shida za su gudanar da zabe a shekarar 2027.
Malamin addinin ya bayyana cewa gwamnoni daga wadannan jihohin za su fuskanci kalubale wajen cika burinsu na wa’adi na biyu, inda ya ce dole ne su yi addu’a sosai “kuma su yi duk abin da ya dace.”
“Gwamnonin Akwa Ibom, Delta, Enugu, Cross River, Kaduna, Zamfara da Ondo dole ne su yi aiki tukuru don samun wa’adi na biyu. Babu tabbacin komawarsu ofis sai sun yi aiki da addu’a sosai."
"Wannan wata alama ce ta abin da za su iya fuskanta. Dole ne su jajirce sosai domin kada su rasa burinsu na wa’adi na biyu."
- Primate Elijah Babatunde Ayodele
Ayodele ya aika sako ga Akpabio
Haka kuma, Primate Ayodele ya yi gargaɗi ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da ya kasance mai hankali da addu’a sosai domin samun wa’adi na biyu a matsayin shugaban majalisar dattawa.
"Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, dole ne ya zama mai matukar taka-tsantsan da addu’a domin samun wa’adi na biyu. Ina hangen cewa matsayinsa yana cikin barazana; dole ne ya jajirce sosai don kauce wa hakan."
- Primate Elijah Babatunde Ayodele
Haka nan, Ayodele ya bayyana cewa wasu sanata da mambobin majalisar wakilai da suka yi fice ba za su samu damar komawa ba a karo na biyu.
Ya kuma yi gargaɗi ga Sanata Ned Nwoko daga jihar Delta dangane da burinsa na neman kujerar gwamna, yana mai cewa “lokacinsa bai yi ba tukuna.”

Source: Facebook
Ga jerin gwamnonin da Primate Ayodele ya aike wa da sako na gargaɗi:
- Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom
- Gwamna Bassey Otu na jihar Cross River
- Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta
- Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo
- Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara
- Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna
Ayodele ya shawarci Tinubu kan Shettima
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI Spiritual Evangelical, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya ba mai girma Bola Tinubu shawara.
Primate Ayodele ya shawarci Shugaba Tinubu da ka da ya sauya Kashim Shettima daga matsayin mataimakinsa a zaben 2027.
Malamin addinin ya bayyana cewa ko kadan bai kamata shugaban kasan ya sauya Shettima daga matsayin mataimakinsa ba.
Asali: Legit.ng


