'Ta Zama Fanko,' NNPP Ta Dura kan PDP da Ta Soki Mulkin Abba a Kano
- Shugaban jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano, Hashim Dungurawa ya bayyana cewa PDP tana kara dusashewa a jihar
- Ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin ikirarin da babbar jam'iyyar hamayya ke yi na cewa tana farfaɗo wa da ƙarfinta
- A kalaman Dungurawa, lokacin PDP ya wuce a Kano kuma babu abin da ta tsinana wa mutanen da su ka zaɓe ta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Shugaban NNPP a Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce babu wata farfaɗo wa da jam'iyyar hamayya ke yi.
Ya ce iƙirarin da PDP ke yi cewa tana nan da ƙarfinta kawai shaci faɗi ne, kuma babu inda za ta ƙara tasiri a siyasar Kano.

Asali: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa Dungurawa ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan ƴan adawa da ke sukar gwamnatin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan adawa na zarginta da rashin gaskiya da bayyana yadda aka yi amfani da kuɗin da aka ware don ilimi, lafiya da kuma gine-ginen ababen more rayuwa.
Shugaban NNPP ya caccaki jam'iyyar PDP
Politics Nigeria ta ruwaito Dungurawa yana jaddada cewa jam’iyyun adawa sun gaza amfani da damar da suka samu a lokacin da suke mulki.
Ya ce:
“Da fari dai muna gode masu da sun yarda cewa muna nan kuma muna aiki. Amma muna tunatar da su cewa sun shafe shekaru takwas a mulki ba tare da wani abin kirki ba.”
Ya zargi gwamnatin da ta gabata da fifita manyan ayyuka marasa amfani da aka yi don ado kawai, ba tare da sun taba ainihin bukatun al’ummar Kano ba.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Ka dauki gadan karkashin kasa da aka yi a Dangi, misali. Wannan gini babu wani amfani da ya ke dashi. Babu wani cunkoso da ya wajabta irin wannan aiki.
NNPP ta aminta da mulkin Abba a Kano
Dungurawa ya jaddada cewa a karkashin Abba Kabir Yusuf, gwamnatin NNPP ta mayar da hankali kan gina ababen more rayuwa masu amfani da suka dace da bukatun jama'a.
Ya ce:
“Yau da kyar zaka iya samun wata kwazazzabo a kan titunan Kano. Hanyoyinmu sababbi ne, fitilun titi suna aiki yadda ya kamata, hattashingayen hanya na nan daram. Wannan yana nuna cewa masu gaskiya sun karbi mulki a jihar.”
Dungurawa ya kuma kare kokarin gwamnatin jihar wajen biyan bashin fansho da aka gada, inda ya ce sama da N27bn daga cikin N48bn da gwamnatin da ta gabata ta bari aka biya.
Ya ce:
“A cikin shekara biyu kacal, mun biya Naira biliyan 27 na fansho — Naira biliyan 22 a baya, sannan kuma wani karin biliyan 5 da za a biya a watan Disamba. Wannan ya nuna cewa muna da gaskiya da rikon amana a tafiyar da gwamnati.”
PDP ta dura a kan Atiku Abubakar
A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta bayyana cewa ba ta da hannu a cikin sabon kawancen siyasa da wasu daga cikin tsofaffin ƴaƴanta suka shiga.
Jam’iyyar ta kuma bayyana rashin jin daɗinta kan yadda wasu jiga-jiganta suka fita daga cikinta, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga ƴaƴanta da su ci gaba da jajircewa domin sake farfaɗo da martabar jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng