'Abubuwa 2 Za Su Hana Tinubu Lashe Zabe a 2027,' Modu Sheriff Ya ba da Satar Amsa
- Sanata Ali Modu Sheriff ya ce babu abin da zai hana Shugaba Bola Tinubu zarcewa sai dai idan ya janye ko kuma ba a yi zabe ba
- Ya jaddada cewa sai an inganta hadin gwiwar Najeriya da Kamaru, Chadi da Nijar kafin a iya kawar da Boko Haram gaba ɗaya
- Sheriff ya bayyana cewa shi ne ya kawo Kashim Shettima siyasa kuma ya ce hadakar ADC ba za ta hana Tinubu nasara a 2027 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff ya yi babbar fallasa game da takarar Shugaba Bola Tinubu a babban zaben 2027.
Sanata Ali Modu Sheriff ya bayyana cewa, abubuwa biyu ne kawai za su iya hana Shugaba Tinubu samun tazarce a zaben mai zuwa.

Asali: Facebook
"Abin da zai hana Tinubu tazarce" - Ali Sheriff

Kara karanta wannan
'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'
Tsohon gwamnan ya bayyana ra'ayinsa game da yadda sakamakon zaben 2027 zai iya kasancewa a wata hira da Channels TV a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Modu Sheriff ya yi ikirarin cewa babu wani abu da zai iya hana Tinubu zarcewa, har sai dai idan ba a yi zabe ba ko kuma shi shugaban da kansa ya ce ya janye.
Ya buga kirji da cewa, da irin tsarin shugabancin Bola Ahmed Tinubu, nasararsa a zaben 2027 za ta zama kamar kiftawar ido ne.
"Zan ba ka satar amsa kyauta, abubuwa biyu ne kawai za su iya hana Shugaba Tinubu zarcewa a zaben 2027; na farko, idan ba a gudanar da zabuka a Najeriya ba; na biyu, idan shi da kansa ya ce ya janye daga takara."
- Sanata Ali Modu Sheriff.
Ali Modu Sheriff ya ba da shawara kan tsaro
Sanata Sheriff ya kuma yi magana kan batun tsaron kasa, musamman ma matsalar kungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabashin kasar.

Kara karanta wannan
'Ban da Peter Obi': An yi wa Malami wahayi game da mutum 3 da za su fatata a 2027
Ya bayyana cewa, don kawo karshen kungiyar ta'addancin gaba daya, dole ne a karfafa dangantakar diflomasiyya da tsaro tsakanin Najeriya da kasashen makwabta.
Yayin da ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar kasashe don dakile ayyukan Boko Haram, Sanata Ali Modu Sheriff ya ce:
"Abin da ya kamata a yi shi ne, mu samu kyakkyawar dangantaka da Kamaru, Chadi, da Nijar."

Asali: Facebook
Sheriff ya yi magana kan Shettima da Obi
Sheriff ya kuma tuna da irin tasirinsa a harkar siyasa ga mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, inda ya bayyana cewa shi ne ya fara shigo da Shettima a siyasa.
Tsohon gwamnan jihar Borno ya ce:
"Ni ne na kawo Sanata Kashim Shettima cikin siyasa. Kafin wannan lokacin, shi ma'aikacin banki ne. Yana aiki ne a banki."
Ya kuma bayyana cewa hadakar 'yan adawa a karkashin jam'iyyar ADC ba za ta yi tasiri a 2027 ba, kamar ma ba za ta wanzu ba.
"Bayanan da na samu na nuni da cewa Peter Obi zai iya komawa jam'iyyar PDP a kowanne lokaci, kuma zai tsaya takarar shugaban kasa karkashin PDP."
- Sanata Ali Modu Sheriff.
Kalli tattaunawar a nan kasa:
Yadda jam’iyyun adawa ke shirin kawar da Tinubu a zaben 2027
Duk da cewa Sanata Ali Modu Sheriff ya ce babu abin da zai hana Bola Ahmed Tinubu zarcewa a 2027 sai dai idan ya janye ko ba a yi zabe ba, jam’iyyun adawa na kara hada kai da daukar matakan da za su iya fasa wannan burin.
PDP, NNPP, LP da ma wasu sabbin kungiyoyin siyasa da na hadaka na kokarin samo wata hanya mai karfi da za ta iya kalubalantar gwamnatin APC a zaben mai zuwa.
Tuni ake rade-radin yiwuwar Peter Obi zai yi gaba domin hada karfi da karfe da sauran masu neman sauyi.
Kwankwaso shi ma na kokarin sake kafa sabuwar gabar siyasa da zata jawo matasa da masu karancin gamsuwa da tafiyar Tinubu.

Kara karanta wannan
Bello Yabo: 'Tun da Buhari ya mutu, Tinubu ya ƙwato kuɗin da aka sace a mulkinsa'
A gefe guda, jam’iyyun adawa na kokarin samar da hadin gwiwa karkashin sabbin kungiyoyi kamar ADC ko wasu gungu na siyasa da za su yi aiki da nufin tunkarar APC a matsayin hadin guiwa.
Wannan tsari na iya zama barazana ga tazarcen Tinubu, musamman idan suka samu shugabanci daya da tsari mai karfi.
Duk da karfin da APC ke da shi, ana iya fuskantar fafatawar siyasa mai zafi a 2027 idan jam’iyyun adawa suka shiryawa lokaci.
"Modu Sheriff ya manta da abu 1" - Surajo Caps
A zantawarmu da matashin dan siyasa kuma dan jam'iyyar PDP daga jihar Bauchi, Surajo Caps, ya ce Modu Sheriff ya manta da cewa Allah ne ke yin yadda ya so a lokacin da ya so.
"Ina so na ja hankalin Modu Sheriff da duk masu tunanin cewa babu abin da zai iya hana Shugaba Tinubu zarcewa a 2027, su sani cewa Allah na nan, shi zai iya yin abin da suke tunanin babu mai iya yi.

Kara karanta wannan
Shugaban gwamnoni 19 ya fadi ya fadi abin da 'yan Arewa za su yi kan tazarcen Tinubu
"A matsayinmu na Musulmi, mun yi imanin cewa Allah zai iya cire fari daga baki, kuma ya cire baki daga fari, sannan shi ke ba da mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so.
"Maganar wai ace sai idan Tinubu bai fito takara ba, ko ba a yi zabe ba ne zai hana shi zarcewa ba ta taso ba, shugabannin kasa nawa ne suna kan mulki kuma suka fadi zabe?
"Ai ya kamata Goodluck Jonathan ya zama izina gare su, yana kan mulki marigayi Buhari ya kayar da shi. Kenan, ba wai don kana mulki ne za a ce kana da tabbacin cin zabe ba."
Surajo Caps ya ce su dai suna tare da jam'iyyar ADC inda Atiku Abubakar ke jagorantar hadaka, kuma suna da yakinin cewa za a samu canjin gwamnati a 2027.
Mahaifiyar Ali Modu Sheriff ta rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mahaifiyar tsohon gwamnan Borno kuma jigo a jam'iyyar APC, Ali Modu Sheriff ta riga mu gidan gaskiya.
An ce marigayiya Hajiya Aisa ta rasu ne bayan doguwar jinya a wani asibitin Abuja, kuma ta rasu tana da shekaru 93 a duniya.
Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya aika sakon ta'aziyya ga Sanata Ali Sheriff kan wannan babban rashi da ya yi na mahaifiyarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng