SDP Ta Fice daga Haɗakarsu Atiku, Za Ta Fito da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a 2027
- Jam’iyyar SDP ta karbe rikon NWC daga hannun Shehu Musa Gabam, sakamakon rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar
- Kwamitin NEC ya nada sababbin shugabannin rikon kwarya da za su tafiyar da SDP har zuwa lokacin da za a yi zaben jam'iyyar
- NEC ya kuma sanar da ficewar SDP daga hadakar siyasa da Atiku Abubakar ke jagoranta, inda jam’iyyar ta ce za ta tsaya takara a 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Rikicin cikin gida da ke addabar SDP ya dauki sabon salo ranar Juma’a, yayin wani zaman kwamitin majalisar zartaswar jam’iyyar na kasa (NEC).
A yayin zaman, NEC din ya rushe shugabancin kwamitin da Shehu Gabam ke jagoranta, wanda aka dakatar a baya, saboda rikicin cikin jam’iyyar.

Source: UGC
SDP ta rushe shugabannin jam'iyya na kasa
Wannan mataki ya fito ne a taron gaggawa da NEC din SDP ya gudanar a Abuja, wanda sakataren kudi na kasa na jam’iyyar, Ibrahim Biu, ya jagoranta, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibrahim Biu ya bayyana cewa:
“Daga wannan lokaci, an rusa kwamitin gudanarwa na kasa. Mun naɗa wadannan mutane da za su rike shugabancin jam’iyyarmu mai girma, kuma su ci gaba da tafiyar da ita gaba.”
Sababbin shugabannin rikon kwarya da aka nada sun hada da:
- Adamu Modibo - Shugaban rikon kwarya na kasa
- Abubakar Dogara - Mataimakin shugaba
- Ekpeyong Ambo - Sakataren jam'iyya na kasa
- Joseph Abu - Sakataren shirye-shirye na kasa
- Chief Solsuema Osaro - Mai ba da shawara kan harkokin doka
- Judith Shuaibu - Sakatariyar yada labarai ta kasa
- Ibrahim Biu - Sakataren kudi na kasa
- Eluwa Ifeanyi - Mai magana da yawun matasa na kasa
Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar SDP
Biu ya shaida wa manema labarai cewa:
"Tabbas, abin takaici ne NEC ta dauki wannan mataki mai tsauri bayan shawarwari da dama da aka yi domin warware rikicin da suka ci tura.
“A ‘yan watannin baya, jam’iyyar mu ta fada cikin rikicin shugabanci. Kamar yadda kuka sani, jam’iyyar ta dare gida biyu.
“Wannan ya jawo tashin hankali a jam'iyyar, har ma bangarorin biyu suka yi arangama a hedikwatar SDP, wanda hakan ya sa jami’an tsaro suka shiga tsakani.”
"SDP ba ta cikin hadaka" - Dogara
A wani bangare na taron, kwamitin NEC ya bayyana ficewar SDP daga hadakar su tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da ke karkashin jam’iyyar ADC.

Source: Facebook
TVC News ya rahoto mataimakin sabon shugaban jam’iyyar, Abubakar Dogara, ya fayyace matsayin SDP da cewa:
“Kwanan nan an yi yunkurin hadin gwiwa tsakanin manyan ‘yan siyasa da jam’iyyu domin samar da hadaka, wanda SDP ta shiga tun farko.
"Sai dai daga baya, wakilin SDP a taron ya bayyana wa 'yan hadakar cewa SDP na cikin shirye-shiryen tunkarar zabukan cike gurbi a jihohi 12, kuma ba za ta so ta rasa martabarta ba.
“Don haka, SDP ba ta cikin wannan hadaka. Za mu fito da dan takarar shugaban kasa da mataimaki daga SDP a zaben 2027 mai zuwa.”

Kara karanta wannan
Jam'iyyar PDP ta haƙura da Kano, ta sauya wuri da ranar gudanar da babban taron ƙasa
Kallo taron jam'iyyar a kasa:
'Ba mu tura El-Rufai hadaka ba' - SDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'dan takarar shugaban kasa na SDP a 2023, Adewole Adebayo ya ce jam'iyyarsu ba ta da wakili a haɗakar ƴan adawa.
Adebayo ya yi ikirarin cewa SDP ba ta tura Nasir El-Rufai ya wakilce ta a hadakar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yake jagoranta.
Tun bayan samun saɓani da fadar shugaban kasa da APC, tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya tattara ya koma jam'iyyar SDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

