Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Fice daga PDP, Ana Zargin Zai Shiga Sabuwar Jam'iyya
- Farfesa Kolapo Olusola-Eleka ya fice daga jam’iyyar PDP a Ekiti bisa zargin jam’iyyar da gazawa wajen zama babban dandalin adawa
- Tsohon mataimakin gwamnan na Ekiti ya aika wasikar murabus dinsa ga shugaban PDP na Okeruku Ward 2, karamar hukumar Ikere
- Olusola-Eleka ya ce PDP ta kauce daga tafarki mai kyau, yayin da wasu majiyoyi ke cewa yana dab da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti – Tsohon mataimakin gwamnan jihar Ekiti, Farfesa Kolapo Olusola-Eleka, ya rubuta takarar murabus daga zama maban jam’iyyar PDP.
A cikin takardar da ya rubuta, ya zargi jam’iyyar da gazawa wajen samar da ingantaccen shugabanci da cikakkiyar adawa a Najeriya.

Source: Twitter
Tsohon mataimakin gwamnan Ekiti ya bar PDP
Olusola-Eleka ya aike da wasikar ne ga shugaban jam’iyyar PDP na mazabar Okeruku Ward 2 da ke Ikere-Ekiti a ƙaramar hukumar Ikere, a cewar rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesan wanda ƙwararre ne a fannin kimiyyar gine-gine, ya kasance mataimakin gwamnan Ekiti tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018 a ƙarƙashin mulkin tsohon gwamna Ayodele Fayose.
A cikin wasiƙar, Olusola ya ce:
“Na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP daga yau. Ina matuƙar godiya ga shugabannin jam’iyyar a dukkan matakai da kuma mambobi da magoya baya da suka tsaya tsayin daka tare da ni a tsawon shekarun nan a jihar Ekiti da wajen ta."
Dalilin tsohon mataimakin gwamna na barin PDP
Jaridar Punch ta rahoto Farfesa Olusola-Eleka ya ci gaba da cewa:
"Jam’iyyar PDP ta ba ni damar hidimtawa jama'ata ta fuskar siyasa, ciki har da zama mataimakin gwamna daga 2014 zuwa 2018 da kuma takarar gwamna a zaɓen 2018.
"Amma bayan dogon tunani da tattaunawa, na fahimci cewa jam’iyyar ta kau daga tafarkin ingantacciyar adawa da jagorancin da ta ke da shi a da.
"Saboda haka, ba zan iya ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar ba a yadda take yanzu. Ina yi mata fatan alheri a gaba.”

Source: Twitter
Murabus din tsofaffin mataimakan gwamnoni
Ko da yake bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, majiyoyi daga cikin tawagarsa na siyasa sun ce akwai yiwuwar ya koma jam’iyyar ADC.
Ba Kolapo ne tsohon mataimakin gwamna da ya fice daga PDP ba, ko a baya bayan nan, tsohon mataimakin gwamnan Imo, Gerald Irona, ya sanar da yin murabus daga PDP saboda rashin gamsuwa da yadda jam'iyyar ke tafiya yanzu.
Jim kadan bayan murabus din Gerald Irona ne muka ruwaito cewa tsohon mataimakin Edo, Philip Shaibu ya fice daga PDP, inda ya koma jam'iyyar APC.
Tsohuwar 'yar takarar PDP ta koma APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Emana Ambrose-Amawhe, wadda ta tsaya takarar mataimakiyar gwamna a Cross River a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023, ta sauya sheƙa zuwa APC.
Ta mika takardar ficewarta daga PDP a ranar 28 ga Maris 2025, wanda ya kawo ƙarshen dangantakarta da jam’iyyar da ta ɗauki shekaru a cikinta.
Shigar ta jam’iyyar APC ta samu tarba ta musamman a liyafar murnar zagayowar ranar haihuwar uwargidan gwamnan jihar Cross River, Eyoanwan Otu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

