Amaechi: Matsala Ta Tunkaro Tinubu bayan Tsohon Minista Ya Sha Alwashi a Kansa kan 2027
- Jagoran jam'iyyar haɗaka watau ADC a yankin Kudu maso Kudu, Rotimi Amaechi ya yi jawabi ga ɗumbin magoya bayansa a jihar Rivers
- Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ya gaji da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu saboda yadda ta jefa ƴan Najeriya cikin ƙuncin rayuwa da wahala
- Tsohon ministan sufurin ya sha alwashin cewa zai daƙile tazarcen mai girma Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Jagoran jam’iyyar ADC na yankin Kudu maso Kudu kuma tsohon ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, ya sha alwashu kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rt. Hon. Rotimi Amaechi ya sha alwashin kawo ƙarshen burin tazarce na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Rotimi Amaechi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa a filin jirgin sama na Port Harcourt a ranar Laraba, 23 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2027: Amaechi na ƙalubalantar Tinubu
Tsohon ministan sufurin ya nuna matuƙar rashin jin daɗinsa game da yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da harkokin ƙasar nan.
Rotimi Amaechi ya ɗaɗe yana sukar gwamnatin Shugaba Tinubu kan yadda take jan ragamar ƴan Najeriya.
A kwanakin baya, tsohon ministan ya bayyana cewa ya sanar da Shugaba Bola Tinubu cewa ba zai taɓa mara masa baya ko kaɗa masa ƙuri’a ba.
Amaechi ya ce ya tsaya akan wannan matsaya ne saboda ya yi imani cewa Tinubu ba shi da ƙwarewar da ake buƙata don tafiyar da Najeriya.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa kai tsaye ya fito ya gayawa mai girma Bola Tinubu hakan.
Rotimi Amaechi ya zargi gwamnatin da jawo tsanani da ƙuncin rayuwar da ƴan Najeriya ke fuskanta.
"Na gaji da wannan gwamnati. Idan mai kuɗi na kashe Naira miliyan huɗu a wutar lantarki, Allah ne kaɗai ya san yadda ku talakawa kuke rayuwa."
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya buƙaci a shiga ADC
Rotimi Amaechi ya buƙaci mazauna jihar Rivers da su yi rajista da jam’iyyar ADC domin hana maguɗin zaɓe da kuma ƙwato ikon siyasa a jihar.
"Dole mu dakatar da rubuta sakamakon zaɓe a Rivers. Ku tafi ku yi rajista da ADC domin mu sauya tsarin."
- Rotimi Amaechi

Source: Facebook
Amaechi dai ya shiga cikin tafiyar ƴan siyasan da suka haɗu domin kafa haɗaka don kifar da Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Ana hasashen cewa tsohon gwamnan zai jarraba sa'arsa wajen neman takarar shugaban ƙasa a 2027.
A shekarar 2022 ya fafata da Tinubu wajen neman tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC.
Amaechi ya taɓo batun takara da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi magana kan yin takara da Bola Tinubu a 2027.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa akwai yiwuwar zai fito takara da mai girma Bola Tinubu a 2027.
Amaechi ya bayyana cewa yana tunanin tsayawa takara saboda ya san har yanzu yana da gudunmawar da zai iya badawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

