2027: Sule Lamido Ya Kawo Karshen Jita Jita kan Batun Komawa ADC
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana aniyarsa ta shiga tafiyar siyasa wacce za ta ceto Najeriya
- Sule Lamido ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga irin wannan tafiya a cikin PDP ko a wajenta
- Hakazalika ya nuna cewa ba zai yi wa PDP butulci ba ta hanyar barin ta zuwa wata jam'iyyar siyasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa yana da niyyar goyon bayan kowace irin tafiya ta siyasa, ko dai a cikin jam’iyyar PDP ko a wajenta.
Sule Lamido ya ce zai shiga tafiyar ne matuƙar hakan zai taimaka wajen samar da tsaro da kwanciyar hankali a Najeriya yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Sule Lamido ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Kara karanta wannan
ADC: Atiku da El Rufai sun fara fuskantar abin da ba su yi tsammani ba daga manyan Arewa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sule Lamido ya faɗi shirinsa kan 2027
"Na yi imani da Najeriya. Don haka duk wata tafiya, ko a cikin PDP ko a wajenta, da za ta taimaka wajen ceton Najeriya, ni a shirye nake na yi aiki da ita a 2027."
- Sule Lamido
Sule Lamido, wanda kuma ya taɓa rike muƙamin ministan harkokin waje, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC, yana mai cewa har yanzu yana cikin PDP.
“Har yanzu ina cikin PDP, duk da cewa jam’iyyar na fuskantar matsaloli. Amma ba zan iya watsar da tarihina ba. Ba zan iya fita daga wurina na asali ba na koma wani ƙaramin wuri kamar ADC ba. Wannan ba zai yiwu ba."
- Sule Lamido
Ya jaddada cewa jam'iyyar PDP ce ta ba shi dama ya riƙe manyan muƙamai kamar ministan harkokin waje da kuma gwamnan jihar Jigawa.
“Saboda haka, ba zan iya watsar da tarihina, mutuncina da ƙimata, na ce yau na samu wani sabon abu, na bar PDP. Ba zan taɓa yin haka ba."
- Sule Lamido
Sule Lamido ya magantu kan ƙirƙiro jihohi
Dangane da ƙara yawan jihohi a ƙasar nan, tsohon gwamnan ya ce kodayake buƙatar ƙirƙirar sababbin jihohi abu ne da doka ta tanada, hakan ba zai warware matsalolin da ake fuskanta ba.

Source: Facebook
"Shin ƙirƙirar sababbin jihohi zai magance matsalolinmu, rashin tsaro, talauci, yunwa da rabuwar kai tsakanin Arewa da Kudu? Akwai manyan matsaloli fiye da ƙirƙirar sababbin jihohi."
- Sule Lamido
Game da ziyarar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa kwanan nan, Sule Lamido ya ce tsohon gwamnan na Kano yana da cikakken ƴancin yin hakan.
Sule Lamido na goyon bayan ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya nuna goyon bayansa ga jam'iyyar ADC a zaɓen 2027.
Sule Lamido ya bayyana cewa yana goyon bayan ADC ne saboda ƴan haɗaka suna da niyyar ceto Najeriya.
Sai dai, ya ce duk da goyon bayansa ga haɗaka, ba zai taɓa ficewa daga jam'iyyarsa ta PDP ba wadda ya yi gwamna a ƙarƙashinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
