'Babu Kai, ba Arewa a 2027': Matashi Ya Yi Wa Sanata Kashim Shettima Gata a Bauchi

'Babu Kai, ba Arewa a 2027': Matashi Ya Yi Wa Sanata Kashim Shettima Gata a Bauchi

  • Wani matashi a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ya nuna soyayya da kuma kishi ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima
  • Matashi Kabiru Garba Kobi ya sadaukar da motarsa domin nuna soyayya da goyon baya ga Kashim Shettima yayin da ake tunkarar zaben 2027
  • An yi wa motar ado da hoton Shettima mai taken “Next Level, Jagoran Arewa, in ba kai ba, Arewa 2027” domin karfafa gwiwar shugabancinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Siyasar Najeriya na cigaba da daukar sabon salo musamman saboda ganin an cigaba da tafiya da Kashim Shettima.

Wani matashi a jihar Bauchi ya sadaukar da motarsa musamman saboda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Kashim Shettima na cigaba da samun goyon baya a Arewa
Matashi ya sadaukar da motarsa saboda kaunar Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima, Nuruddeen Yakubu Haske.
Source: Facebook

Matashi ya yi wa Kashim gata a Bauchi

Mai magana da yawun kungiyar 'APC Youth Parliament' a Bauchi, Nuruddeen Yakubu Haske shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa.

Kara karanta wannan

UNIMAID: An faɗi babban dalilin da ya sa Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari

Haske ya ce matashin, Kabiru Garba Kobi wanda shi ne shugaban kungiyar ya yi haka ne saboda soyayya ga Kashim Shettima.

Lamarin ya dauki hankulan mutane duba da irin goyon bayan matasa ga shugabanci mai inganci a Najeriya yayin da ake shirin zaben 2027.

Kobi ya yi babban sadaukarwa ta hanyar miƙa motarsa domin tallafa wa mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima saboda soyayya da kishin Arewa.

Matasa sun nuna goyon baya ga Kashim Shettima
Kungiya ta sadaukar da mota domin goyon bayan Kashim Shettima a Bauchi. Hoto: Legit.
Source: Original

An karfafi matasa kan jagoranci nagari

An yi wa motar ado da babban hoto mai taken: 'Next Level, Jagoran Arewa, in ba kai ba, Arewa 2027' wanda ke nuna tsantsar soyayya ga tsohon gwamnan Borno.

Hakan ya nuna wata sabuwar hanya ta isar da saƙo na goyon baya da amincewa da irin nagartar Sanata Kashim Shettima a matsayin jagoran da ya dace da cigaban yankin Arewa da Najeriya gaba ɗaya.

Haske ya ce:

"Wannan matashi ya zamo abin koyi, domin ya fito fili da goyon bayansa ba tare da fargaba ba.

Kara karanta wannan

Bayan Buhari, Bola Tinubu zai je jihar Kano ta'aziyyar Aminu Dantata

"Ya nuna cewa matasa su ma suna da rawar da za su taka a gina shugabanci na gari a Najeriya musamman a wannan lokaci da ake ciki.
"Lallai wannan lamari na kara jaddada cewa Arewa na da matasa masu hangen nesa da kishin al’umma, kuma irin wannan goyon baya na zahiri zai kasance ginshikin nasara a 2027."

A karshe, Nuruddeen ya yi addu'ar Ubangiji ya dafa masa domin cigaba da daura matasa kan turba mai kyau.

"Allah ya kara masa ɗaukaka da nasara, ya kuma ci gaba da shiryar da matasa kan hanya madaidaiciya."

- Cewar Nuruddeen Haske

An soki masu kiran sauya Shettima da Dogara

Mun ba ku labarin cewa gamayyar kungiyoyin matasa na jam’iyyar APC a Jihar Bauchi sun soki kiran daukar Yakubu Dogara a matsayin mataimaki.

Kungiyoyin sun hada da 'APC Youth Solidarity for Tinubu/Shettima Movement' ƙarƙashin jagorancin Haske No Shaking da 'APC Youth Parliament' ƙarƙashin Alh. Kabiru G. Kobi.

Har ila yau, sun soki ra’ayoyin da wasu ke yadawa na cewa Rt. Hon. Yakubu Dogara ya dace da kujerar mataimakin shugaban ƙasa a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.