Bayan Tafiyar Atiku, PDP Ta Bayyana Shirinta na Dawo da Peter Obi cikin Jam'iyyar

Bayan Tafiyar Atiku, PDP Ta Bayyana Shirinta na Dawo da Peter Obi cikin Jam'iyyar

  • PDP ta bayyana cewa tana ƙoƙarin dawo da Peter Obi cikin jam’iyyar domin inganta haɗin kai da tasirinta a zaɓen 2027 mai zuwa
  • Jam'iyyar adawar ta ce Obi babban jari ne wanda zai amfani kowace jam’iyya, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa wajen dawo da shi ba
  • PDP ta ƙara da cewa tana tattaunawa da sauran ‘yan adawa domin ƙarfafa gwiwa, kuma komawar Obi cikinta zai kara mata kwarjini

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam'iyyar PDP ta fito fili ta bayyana cewa tana ƙoƙarin dawo da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, cikin tafiyarta.

Mataimakin sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Ibrahim Abdullahi ya bayyana cewa PDP na son sake hada kai da Obi a harkokin siyasarta.

PDP ta ce tana tattaunawa don dawo da Peter Obi cikin jam'iyyar kafin 2027
Gabanin 2027, PDP ta fara shirin dawo da Peter Obi cikin jam'iyyar. Hoto: @PeterObi, @officialPDPNig
Source: Twitter

"Peter Obi rainonmu ne" - PDP

Kara karanta wannan

'Zai yi wahala Obi ya yi shugaban kasa,' Hadimin Buhari ya yi martani ga Obidients

Da yake jawabi a gidan Talabijin na Arise, Abdullahi ya ce Peter Obi babban jari ne na siyasa wanda zai iya taimakawa PDP na lashe zaɓe idan ya amince ya koma jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Peter Obi rainonmu ne. Muna son mu dawo da shi cikinmu, domin shi babban jari ne da kowace jam’iyyar siyasa za ta so ta mallaka.”

Abdullahi ya jinjina wa nasarorin Obi a zaben 2023, inda ya samu sama da kuri’u miliyan shida duk da cikas da magudin da ya ce an tafka a sassa da dama na kasar.

PDP ta yabawa Obi kan zaben 2023

Ya kara da cewa da ba a gamu da matsalolin zabe ba, da Peter Obi zai samu kuri'u fiye da haka, yana mai cewa:

“Samun kuri’u sama da miliyan shida alama ce da ke nuna cewa Peter Obi ba dan takarar da za a yi watsi da shi ba ne.”

Obi ya fice daga PDP ne a lokacin da ake shirin gudanar da fitar da gwani a 2022, sannan ya koma jam'iyyar LP inda ya tsaya takarar shugaban kasa, ya kuma zo na uku bayan Atiku Abubakar na PDP da Bola Ahmed Tinubu na APC, wanda ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

PDP ta yi babban rashi, tsohon ministan shari'a ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC

Yawan goyon bayan da ya samu daga matasa da mazauna birane ya tabbatar da matsayinsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan 'yan adawa a Najeriya.

Jam'iyyar PDP tace tana da yakinin za ta iya cin zaben 2027 idan ta jawo Peter Obi cikinta
Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na LP a 2023. Hoto: @PeterObi
Source: Facebook

2027: PDP na kokarin dawo da Peter Obi

Abdullahi ya ce ficewar Obi daga PDP ta kasance babban gibi a wancan lokacin, amma hakan bai rage girmansa da karbuwarsa ba a idon ‘ya’yan jam’iyyar.

Ya bayyana cewa PDP ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kokarin dawo da Peter Obi, domin samun sa a kowace jam’iyya babban rabo ne.

A cewarsa, PDP na ci gaba da gudanar da tattaunawa a cikin gida tare da tsara dabarun hadin kai da sauran ‘yan adawa domin fuskantar babban zaben 2027, kuma shirin dawo da Peter Obi wani bangare ne na wannan tsari.

“Idan lokaci ya yi, muna da yakinin za mu iya dawo da shi. Zai kasance babban ƙaruwa ne ga jam’iyyarmu."

- Ibrahim Abdullahi.

Kalli tattaunawar a kasa:

Atiku ya fice daga jam'iyyar PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Atiku Abubakar, ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP bayan shafe dogon lokaci yana gwagwarmaya a cikinta.

Kara karanta wannan

ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala

A wata wasiƙa da ya rubuta kuma ya sanya wa hannu a ranar 14 ga Yuli, 2025, Atiku ya sanar da shugabannin PDP na Jada, jihar Adamawa, game da murabus ɗinsa.

Ficewar Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta ƙoƙarin karfafa jam’iyyar hadaka ta ADC domin haɗa ƙarfi da 'yan adawa kafin zaɓen 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com