Shugaban NNPP Ya Tsage Gaskiya kan Batun Kwankwaso Zai Koma ADC

Shugaban NNPP Ya Tsage Gaskiya kan Batun Kwankwaso Zai Koma ADC

  • Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya fito ya yi magana kan jita-jitar da ake yaɗawa kan Rabiu Musa Kwankwaso
  • Hashimu Dungurawa ya musanta cewa Kwankwaso ya shirya tattara ƴan komatsansa domin komawa jam'iyyar ADC
  • Shugaban na NNPP ya nuna cewa Kwankwaso ba irin mutanen nan ba ne masu yin abubuwa ba tare da tuntuɓar magoya bayansu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya yi magana kan jita-jitar cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai koma ADC.

Hashimu Dungurawa ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai koma ADC.

Shugaban NNPP ya yi magana kan komawar Kwankwaso ADC
Shugaban NNPP ya musanta batun komawar Kwankwaso ADC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta ce Hashimu Dungurawa ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana da manema labarai a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

2027: Shugaban ADC ya fallasa shirin dakile farin jinin jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me aka ce kan jita-jitar komawar Kwankwaso ADC?

Dungurawa ya jaddada cewa Kwankwaso ba shi daga cikin ƴan siyasar da za su yanke hukunci ba tare da cikakken nazari ba.

"Maganar da ake yi cewa Kwankwaso zai koma ADC ko wata jam’iyya ba komai ba ne face hasashe mara tushe daga wasu ƴan siyasa da ke jin tsoron shugaban tafiyar Kwankwasiyya."
"Amma na san Kwankwaso sosai, ba mutum bane wanda yake gaggawar bayyana mataki na gaba da zai ɗauka."
"Me ya sa ƴan siyasar Najeriya ke firgita game da motsin Kwankwaso? Su kwantar da hankalinsu. Lokacin yanke hukunci bai yi ba tukuna. Mu mutane ne masu lissafi, ba ma yanke hukunci sai mun yi cikakken tunani.”
“Kar ku manta, Kwankwaso a halin yanzu shi ne jagoran siyasa na Arewa, kuma kusan dukkan ƴan siyasa musamman a wannan yanki, na kallon sa a matsayin jagora. Don haka, batun cewa zai sauya sheƙa a yanzu ba gaskiya ba ne."

Kara karanta wannan

ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala

- Hashimu Dungurawa

Kwankwaso na shawara da magoya baya

Yayin da yake tsokaci kan wasu da ake cewa mabiyansa ne da ke nuna damuwa da yadda tafiyar siyasarsa, ya ce magoya bayan Kwankwaso ba su nuna shakku a kansa.

"Su ba ainihin magoya baya ba ne. Magoya baya na gaskiya sun san Kwankwaso baya yanke kowanne hukunci ba tare da tuntuɓar su ba, har ma da magoya baya na matakin gunduma."

- Hashimu Dungurawa

Rabiu Musa Kwankwaso ba zai koma ADC ba
Shugaban NNPP ya ce Kwankwaso bai da shirin komawa ADC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Yayin da yake bayani kan jita-jitar cewa an ga Kwankwaso yana ganawa da wasu ƴan siyasa daga wasu jam’iyyu, Dungurawa ya bayyana cewa:

"Shi ɗan siyasa ne mai digirin digirgir (PhD) a harkar siyasa, kuna tsammanin zai ɓoye kansa ko ya ware daga wasu mutane? Ko kaɗan. Zai iya tattaunawa da kowa, hakan ba yana nufin komai ba. Wannan al’ada ce."

APC na zawarcin Kwankwaso daga NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa APC na son jawo Rabiu Musa Kwankwaso zuwa cikinta.

Kara karanta wannan

Moro: Babban sanatan PDP a majalisa ya tsage gaskiya kan shiga hadaka

Hakazalika, Buba Galadima, ya bayyana cewa daga cikin masu zawarcin Kwankwaso har da haɗakar ƴan adawa ta ADC.

Sai dai, ya bayyana cewa Kwankwaso ba zai yi gaggawa wajen barin jam'iyyar NNPP ba wacce ya ke jagora a cikinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng