2027: Manyan 'Yan Siyasar Najeriya da Suka Bar PDP, APC, Suka Shiga Kawancen ADC

2027: Manyan 'Yan Siyasar Najeriya da Suka Bar PDP, APC, Suka Shiga Kawancen ADC

  • Siyasar Najeriya na sauyawa yayin da manyan ƴan siyasa ke komawa ADC don kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Baya ga Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, da Nasir El-Rufai, akwai wasu manyan 'yan siyasa sama da 20 da suka shiga ADC
  • A cikin wannan rahoton, Legit Hausa ta yi bayani kan fitattun jagororin siyasar Najeriya da suka shiga ADC da tasirinsu ga jam'iyyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Siyasar Najeriya na fuskantar sauyi mai girma yayin da manyan ’yan siyasa ke barin jam’iyyar APC mai mulki, PDP, da wasu jam’iyyu don shiga kawancen jam’iyyar ADC.

Wannan na daga cikin kudurin jagororin hadakar na kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, inda ya sa ADC ta zama babbar jam’iyyar adawa.

Rahoto ya yi bayanin manyan 'yan siyasar da suka bar APC, PDP suka koma ADC da tasirinsu a jam'iyyar
Atiku Abubakar da manyan 'yan adawa sun zabi ADC matsayin jam'iyyar hadaka. Hoto: @atiku
Source: Twitter

A wannan rahoton Legit Hausa ta kawo jerin manyan 'yan siyasa da suka koma ADC, wanda ya nuna sauyi mai karfi a siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

PDP ta yi babban rashi, tsohon ministan shari'a ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan ’yan siyasar da suka shiga kawancen ADC

1. Atiku Abubakar – Tsohon mataimakin shugaban kasa (PDP)

Takaitaccen bayani: Atiku Abubakar babban jigo ne a siyasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na PDP a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kasance jagora a 'yan siyasar da ke fafutukar kawo sauyi a Najeriya musamman ta fuskar tattalin arziki, tsaro da ci gaban kasa.

Dalilin sauya sheka: Atiku ya ce rashin tsari a cikin PDP da raguwar darajarta ne ya sa ya koma ADC, inda ya bayyana cewa ita ce hanyar “ceto dimokuradiyyar Najeriya.”

Tasiri: Shigar Atiku cikin jagorin hadakar 'yan adawa zai karawa ADC kwarin gwiwa da tasiri a fadin kasar, musamman la'akari da karfinsa a siyasance.

2. Peter Obi – Tsohon dan takarar shugaban kasa, 2023 (LP)

Takaitaccen bayani: Dan takarar shugaban kasa na Labour Party a 2023, Peter Obi ya samu goyon bayan matasa ta hanyar “Obidient” movement, yana mai da hankali kan yaki da cin hanci da kuma gyaran mulki.

Kara karanta wannan

2027: Ƴan siyasa 5 da ake hasashen za su nemi takarar shugaban ƙasa a ADC

Dalilin sauya sheka: Ko da yake Obi bai shiga ADC a hukumance ba, amma dai ya fito a fili yana goyon bayan kawancen, wanda ya haifar da hasashe cewa zai iya barin LP gaba daya kafin 2027.

Tasiri: Goyon bayan Obi da kuma shahararsa a tsakanin matasa ya sa ya zama muhimmin ginshiki ga ADC, wanda zai iya jawo hankalin matasa da masu zabe a 2027.

3. Rotimi Amaechi – Tsohon gwamnan Rivers (APC)

Takaictaccen bayani: Tsohon gwamna na Rivers sau biyu kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya taka muhimmiyar rawa a nasarar APC a 2015.

Dalilin sauya sheka: Amaechi ya bar APC saboda matsalolin tattalin arziki na Najeriya, ciki har da hauhawar farashin kayayyaki da rashin tsaro, kuma ya shiga ADC don gina kawancen adawa.

Tasiri: Tasirinsa a yankin Kudu maso Kudu da kwarewarsa a harkar siyasa suna kara wa ADC karfi a yankin, kuma zai iya taimakawa wajen ganin nasarar jam'iyyar a 2027.

David Mark ya zama shugaban rikon kwarya na jam'iyyar ADC na kasa
Atiku Abubakar, shugaban ADC na kasa, David Mark, Mallam Nasir El-Rufai. Hoto: @atiku_mission
Source: Facebook

4. Nasir El-Rufai – Tsohon gwamnan Kaduna (APC)

Takaitaccen bayani: Tsohon ministan Abuja, kuma tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai ya kasance babban jigo a APC da ya shahara a sha'anin mulki.

Kara karanta wannan

"Ku yi hattara": Malami ya fadi abu 1 da zai iya rusa hadakarsu Atiku kafin 2027

Dalilin sauya sheka: El-Rufai ya ce ya fice daga APC saboda ta sauka da asalin manufar da aka ginata. Ya ce matsalolin shugabanci sun tilasta shi kama gabansa.

Kafin ya shiga kawancen 'yan adawa da ADC, El-Rufai ya fara shiga jam'iyyar SDP, inda daga can ne ya hade kai da Atiku suka kafa kawancen da ya kawo ADC.

Tasiri: Tasirinsa a Arewa-Maso-Yamma da kwarewarsa a mulki sun kara wa ADC karfi da kuma dora yakinin nasararta a 2027.

5. David Mark – Tsohon shugaban majalisar dattawa (PDP)

Takaitaccen bayani: Tsohon soja, tsohon gwamna, David Mark ya taba rike mukamin shugaban majalisar dattawa kuma yanzu shi ne shugaban rikon kwarya na ADC.

Dalilin sauya sheka: Mark ya soki gazawar shugabancin jam'iyyar PDP wanda ya sanya shi ya koma ADC don jagorantar sake fasalinta da hada kan 'yan adawa.

Tasiri: Kasancewarsa kwararre a shugabanci ya sa aka ba shi mukamin shugaban riko na ADC, wanda ake ganin zai kai jam'iyyar ga nasara a 2027.

6. Abubakar Malami – Tsohon ministan shari’a (APC)

Kara karanta wannan

APC: 'Yan siyasar Arewa sun fara neman kujerar Ganduje gadan gadan

Takaitaccen bayani: Malami ya zama ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya taka rawa wajen gyaran doka.

Dalilin sauya sheka: Malami ya bar APC saboda yadda ake tafiyar da matsalolin tattalin arziki da tsaro, kuma ya shiga ADC don karfafa tsarinta na shari’a da siyasa.

Tasiri: Kwarewarsa a shari’a da kuma tarin magoya bayansa za su daidaita tafiyar ADC a wajen tsara dabarun zaben da kuma ba ta nasara a shari'o'in zabe.

7. Emeka Ihedioha – Tsohon gwamnan Imo (PDP)

Takaitaccen bayani: Tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai kuma tsohon gwamnan Imo, Ihedioha ya bar PDP a watan Afrilun 2024.

Dalilin sauya sheka: Ihedioha ya ce ya fice daga PDP saboda matsaloli na cikin gida, sannan ya shiga ADC da fatan za ta hada kan 'yan adawa da magance matsalolin kasar.

Tasiri: Tasirinsa a Kudu-Maso-Gabashin ya sanya shi aminin Peter Obi, ana ganin zai taimaka wajen daukaka darajar ADC da samun nasararta a zabuka masu zuwa a yankin.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fara gargadin ƴaƴanta kan takarar shugaban ƙasa bayan hadaka

8. John Odigie-Oyegun – Tsohon shugaban APC na kasa

Takaitaccen bayani: Shugaban farko na APC kuma tsohon gwamnan Edo, Oyegun ya taka muhimmiyar rawa a nasarar APC a 2015.

Dalilin sauya sheka: Oyegun ya ce ya fice daga APC mai mulki a kasa saboda rashin jin dadin yadda take tafiya. Ya koma ADC don kawo gyare-gyare kasar.

Tasiri: Komawarsa cikin jam'iyyar ADC alama ce ta rashin jin dadin yadda ake gudanar da shugabanci a APC, wanda hakan ke karawa 'yan adawa kwarin gwiwa.

9. Uche Secondus – Tsohon shugaban PDP na kasa

Takaitaccen bayani: Tsohon shugaban PDP na kasa, Secondus ya kasance babban jigon jam’iyyar kuma ya taka rawa wajen tsarinta.

Dalilin sauya sheka: Secondus ya koma ADC, yana mai sukar gazawar PDP wajen kiyaye ka’idodinta da kuma bukatar sabon dandali na siyasa.

Tasiri: Kwarewarsa a shugabanci da kuma sanin makamar tafiyar da jam'iyya yana taimakawa ADC sanin yadda za ta tafiyar da 'ya'yanta.

Kara karanta wannan

ADC ta shiga Borno da karfinta, tana wawashe yan PDP da APC gabanin 2027

Rauf Aregbesola ya zama sakataren jam'iyyar ADC na kasa a shirin kifar da APC a 2027
Rauf Aregbesola ya zama sakataren jam'iyyar ADC na kasa a shirin kifar da APC a 2027. Hoto: @raufaregbesola
Source: Twitter

10. Rauf Aregbesola – Tsohon gwamnan Osun (APC)

Takaitaccen bayani: Tsohon ministan cikin gida kuma tsohon gwamnan Osun, Aregbesola yanzu shi ne sakataren rikon kwarya na ADC.

Dalilin sauya sheka: Aregbesola ya bar APC saboda rashin jin dadin yadda ta sauya manufofinta da kuma rashin gamsuwa da mulkin da take yi a kasa

Tasiri: Aregbesola yana da karfi a Kudu-Maso-Yamma, kuma matsayinsa a matsayin sakatare na karfafa ayyukan ADC.

11. Aminu Tambuwal – Tsohon gwamnan Sokoto (PDP)

Takaitaccen bayani: Tsohon shugaban majalisar wakilai kuma tsohon gwamnan Sokoto da ya yi wa'adi biyu, Tambuwal ya kasance dan majalisa da ke tasiri a Arewa.

Dalilin sauya sheka: Tambuwal ya koma ADC bayan barin PDP, yana mai cewa akwai bukatar hadin kan 'yan adawa don magance kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Tasiri: Tasirinsa a Arewa-Maso-Yamma da kwarewarsa a harkokin majalisa suna kara wa ADC karfi a shiyyar da ma kasa baki daya.

Kara karanta wannan

Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus

12. Sule Lamido – Tsohon gwamnan Jigawa (PDP)

Takaitaccen bayani: Tsohon ministan harkokin waje kuma tsohon gwamnan Jigawa da ya yi wa'adi biyu, Lamido babban jigo ne a PDP a yankin Arewa.

Dalilin sauya sheka: Duk da cewa Sule Lamido bai shiga ADC a hukumance ba, amma ya ce yana tare da kawancen 'yan adawa, ya ce zai yi aiki tukuru don kawo karshen gwamnatin APC saboda halin da ta jefa al'uma.

Tasiri: Goyawa jam'iyyar ADC baya yana nufin cewa 'yan adawa sun samu daya daga cikin masana sirrin siyasa da cin zabe, ana ganin ADC za ta iya cin zabe a Jigawa da jihohin Arewa saboda tasirinsa.

13. Gabriel Suswam – Tsohon gwamnan Benue (PDP)

Takaitaccen bayani: Tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon dan majalisa, Suswam ya kasance babban jigo ne a PDP a yankin Arewa ta Tsakiya.

Dalilin sauya sheka: Suswam ya shiga ADC don tallafawa yunkurin kawancen 'yan adawa, yana mai sokar rashin karfin tsarin PDP a yanzu.

Kara karanta wannan

Haɗaka: An faɗi ƴan siyasa 7 a ADC da ke neman takara domin karawa da Tinubu

Tasiri: Kasancewarsa tsohon gwamna a Arewa ta Tsakiya, ana ganin zaman Suswam a ADC zai kara karfin jam'iyyar da yiwuwar samun nasararta a shiyyar.

14. Sam Egwu – Tsohon gwamnan Ebonyi (PDP)

Takaitaccen bayani: Sam Egwu wanda ya kasance tsohon ministan ilimi kuma tsohon gwamnan Ebonyi, ya fice daga PDP duk da cewa ya ci zaben dan majalisa a karkashinta.

Dalilin sauya sheka: Egwu ya koma ADC, inda ya ce yanzu neman kawancen da zai magance kalubalen mulki da tattalin arziki na Najeriya.

Tasiri: Kasancewar Egwu yana da tasirinsa a Kudu-Maso-Gabashin, hakan ya kara wa ADC karfi da kuma tasiri a siyasance.

15. Ibrahim Shekarau - Tsohon gwamnan Kano (PDP)

Takaitaccen bayani: Tsohon gwamnan Kano, Shekarau ya kasance babban jigon PDP a Kano, jihar da take da matukar karfi da tasiri a siyasar Najeriya.

An ce Shekarau da kungiyar magoya bayansa sun bar PDP tun da dadewa, inda kuma daga bisani suka shiga kawancen su Atiku.

Dalilin sauya sheka: An ce Ibrahim Shekarau ya sauya sheka ne saboda burinsa na ganin an samu sauyin gwamnati da kuma kawo ci gaba ga al'umma.

Kara karanta wannan

Hadaka: Wike ya bar nuƙu nuƙu, ya fadi jam'iyya 1 da za ta iya rikita APC a 2027

Tasiri: Ibrahim Shekarau yana da matukar tasiri ga jam'iyyar hadaka kasancewarsa sananne a Kano, ana ganin kuri'un Kano za su iya canja sakamakon zabe.

Jam'iyyar ADC na ci gaba da samun karbuwa a jihohin Najeriya, ana sa ran za ta iya doke APC a 2027
Jam'iyyar kawance ta ADC na ci gaba da samun karbuwa a jihohin Najeriya. Hoto: @ADCngcoalition
Source: Facebook

Muhimmancin sauya shekar jiga-jigan

Kawancen ADC, wanda aka kafa don kalubalantar APC, yana samun karbuwa a matsayin dandali na adawa da ke sa ran zai kawo babban sauyi a kasar.

Majiyoyi sun nuna cewa an kafa wannan kawancen bayan shawarwarin watanni da aka yi don samar da dandalin da zai iya kwace mulki daga APC tare da gyara matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro, da kalubalen mulki na Najeriya.

Tare da shugaban rikon kwarya David Mark da sakatare Rauf Aregbesola a kan gaba, ADC tana ci gaba da sake fasalin tsarinta don karbar sabavbin mambobi da kuma shirya wa zaben 2027.

Dabarun kawancen ADC suna kama da hadin kan APC a 2013, wanda ya kawar da jam'iyyar PDP daga mulki a 2015.

Duk da haka, kalubalen a ke tunkarar ADC sun hada da zabar dan takarar shugaban kasa da kuma yadda za ta iya lashe zaben 2027.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Abin da ya rusa haɗakar Obasanjo a ADC domin yakar Buhari a 2019

'Yan Najeriya sun yi martani

Mai sharhi, Iliyasu Hadi, ya yi hasashen cewa ADC na iya zama babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya saboda manyan mutanen da suka shige ta.

A zantawarsa da Legit Hausa, Iliyasu Hadi ya ce:

"Muna kan gabar ganin wani babban sauyi a siyasar Najeriya. Duk wasu kusoshin siyasar kasar ka ga suna fita daga jam'iyyunsu zuwa ADC.
"Kar ka manta da yawa daga cikinsu su ne suka kafa APC kuma har ta ci zabe a 2015, kenan, idan suka sake hada wani karfin, za su iya cin zabe a 2027.
"Duk da cewa ita siyasa kasuwar bukata ce, amma tabbas dole ne hantar gwamnatin APC ta kada, dole ne 'yan PDP su karaya, su zama 'yan kallo a adawar kasar."

A zantawar Legit Hausa da Nura Haruna, ya nuna damuwa kan yadda wadanda suka kafa APC ne suka dawo don kafa kawancen kayar da APC.

"Watakan sai ka nutsu ne za ka fahimci siyasar kasar nan. Ka da ka dauka wai har a zuciya talakan ne a ransu, suna yin komai ne don bukatar kansu.

Kara karanta wannan

Aregbesola: Tsohon gwamna ya rikide daga aminin Tinubu ya koma sakataren haɗaka

"Ita fa siyasar nan tamkar kasuwanci ne, wanda ya zuba jari yana fatan samun riba ne. Kaga kuwa, za su iya shiga kowacce irin hadaka domin cimma burinsu.
"Abin da nake tsoro shi ne, bayan sun gama kafa ADC din, to idan ita ma ta bata masu rai, za su sake kafa wani kawancen, ka ga an mayar da hada kawance wata hanya ta yi wa jam'iyyar da ba a so taron dangi, ko da kuwa tana jin-kan talaka."

- Nura Haruna.

'ADC za ta iya doke Tinubu a 2027' - Dagogo

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dr. Farah Dagogo ya ce hadakar ADC na da karfin kayar da APC a 2027 idan aka tabbatar da hadin kai a cikin jam’iyyar.

Tsohon dan majalisar wakilan ya ce shigar Atiku Abubakar cikin hadaka ya nuna cewa ya shirya ceto Najeriya daga matsalolin tattali.

Ya ce gasa tsakanin Atiku, Obi da Amaechi ba zai kawo rikici a ADC ba idan aka yi sahihin zaben fitar da gwani kuma aka yi sulhu bayan zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com