2027: Ƴan Siyasa 5 da Ake Hasashen Za Su Nemi Takarar Shugaban Ƙasa a ADC

2027: Ƴan Siyasa 5 da Ake Hasashen Za Su Nemi Takarar Shugaban Ƙasa a ADC

FCT, Abuja - Jam'iyyun adawa a Najeriya sun fara shirye-shirye domin zaben shekarar 2027 da ke tafe domin kwace mulki a hannun Bola Tinubu.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yan adawa na yawan sukar gwamnatin Bola Tinubu saboda rashin tausayawa al'ummar Najeriya.

An yi hasashen yan siyasa da za su nemi takara
Tsohon shugaban ADC ya fadi yan siyasa da za su yi takara a 2027. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi.
Source: Facebook

Jiga-jigan yan siyasa da suka hadu a ADC

Rahoton Punch ya ce an kaddamar da jam'iyyar ADC a matsayin dandalin siyasa a zaben 2027 domin kwace mulkin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai manyan jiga-jigan yan siyasa daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya da suke ganin za su tunkari gwamnatin APC a 2027.

Daga cikin wadanda suka hada kai akwai tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023 karkashin PDP, Atiku Abubakar.

Sannan akwai dan takarar shugaban kasa a LP a zaben 2023, Peter Obi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

APC: 'Yan siyasar Arewa sun fara neman kujerar Ganduje gadan gadan

Sai kuma tsofaffin ministoci, Rotimi Amaechi, Rauf Aregbesola, Abubakar Malami da kuma David Mark da sauransu.

Sai dai ana zargin daga cikin jiga-jigan akwai masu neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC wanda ka iya jawo rigima.

Legit Hausa ta duba muku wadanda ake hasashen za su nemi takara a 2027.

1. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya dade yana neman kujerar shugaban kasa domin samun madafun iko, cewar rahoton TheCable.

Tun bayan kammala wa'adinsa a matsayin mataimakin shugaban kasa a 2007 ya ke neman takara a jam'iyyu daban-daban.

Atiku na daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar haɗaka a APC a 2014 wanda ya ba Muhammadu Buhari damar samun mulki a karon farko.

Tsohon shugaban ADC, Ralph Nwosu ya tabbatar da cewa Atiku na daga cikin masu shirin neman takara a 2027 a jam'iyyar.

Ana hasashen Atiku zai nemi takara a ADC
Atiku Abubakar ya yi magana kan takara a 2027. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

2. Peter Obi

Tsohon gwamnan Anambra ya taba zama ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP wanda suka tsaya da Atiku.

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi ya ziyarci Sheikh Rigachikun a Kaduna, Malam ya masa kyauta

Obi daga bisani ya bar jam'iyyar PDP inda ya sauya sheka zuwa LP da kuma tsayawa takara a zaɓen 2023.

Peter Obi ya ba da mamaki a zaben 2023 domin ya yi abin da ba a taba tsammani ba wanda ya zo na uku a zaɓen da aka gudanar.

Shi ma an ce yana daga cikin wadanda ake sa ran za su nemi takara domin har ya mika bukatar yin wa'adi daya kacal idan ya samu dama.

Peter Obi ya tura bukatar takara ga ADC
Yan siyasar da ake hasashen za su yi takara a 2027. Hoto: Peter Obi.
Source: Twitter

3. Rotimi Amaechi

Tsohon gwamnan Rivers shi ma an ce yana iya neman takarar shugaban kasa a ADC a 2027.

Tsohon minista a gwamnatin Buhari ya yi murabus daga jam'iyyar APC zuwa ADC a makon jiya.

Amaechi na daga cikin yan siyasa da ke goyon bayan a ba dan Kudu dama domin rike madafun iko a wannan karo.

Amaechi ya yi murabus daga APC
Ana hasashen yan siyasa 5 da za su nemi takara a ADC. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Source: Facebook

4. Nasir El-Rufai

Duk da dai babu wata alama daga El-Rufai kan shirin neman shugaban kasa, amma wasu na zargin akwai masu goyon baya ya tsaya.

Jigon ADC, Ralph Nwosu ya ce El-Rufai zai iya kasancewa cikin masu neman takarar shugaban kasa a 2027 karkashin jam'iyyar ADC.

Kara karanta wannan

2027: ADC a Kudancin Najeriya ta fadi matsayarta kan tsayar da Atiku takara

Sai dai wasu masana na ganin cewa El-Rufai ba shi da wani buri na neman takarar shugaban kasa a shekarar 2027 da ke tafe.

Wasu na ganin babban burin El-Rufai shi ne ganin gwamnatin Bola Tinubu a kasa duba da rashin jituwa da ake zargi a tsakaninsu.

El-Rufai yana daga cikin jiga-jigan jam'iyyar ADC
Wasu na hasashen El-Rufai zai nemi takara a ADC. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

5. Rauf Aregbesola

Ralph Nwosu ya ce daga cikin yayan jam'iyyar ADC akwai ma wadanda ke marawa tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya nemi takara.

Aregbesola shi ne wanda aka naɗa mukaddashin sakataren jam'iyyar ADC da aka ƙaddamar domin haɗaka a 2027.

Nadin Aregbesola ya bar baya da kura yayin da wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar da jiga-jiganta ke sukar hakan da cewa ba a bi ka'ida ba wurin zaben shugabanni.

Magoya bayan Aregbesola na son ya yi takara a ADC
Yan siyasa da ake hasashen za su yi takara a ADC. Hoto: Rauf Ogbeni Aregbesola.
Source: Twitter

ADC ta gargadi yayanta kan takara a 2027

Mun ba ku labarin cewa shugaban rikon kwarya na jam’iyyar ADC, Sanata David Mark, ya gargadi masu nuna sha’awar takara tun da wuri.

Wasu ƴan ADC sun nuna damuwa kan yadda wasu ke nuna kwaɗayin takara, inda su ke ganin kamata ya yi a gina jam'iyya.

A kan batun tasirin ADC, masani Salihu Yakasai ya ce jam'iyyar na da damar nasara idan ta hada kai da fitattun ‘yan siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.