Gwamna Lawal Ya Yi Magana kan Yiwuwar Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar Haɗaka ADC

Gwamna Lawal Ya Yi Magana kan Yiwuwar Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar Haɗaka ADC

  • Gwamna Dauda Lawal ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa yana shirye-shiryen sauya sheƙa daga PDP zuwa APC ko jam'iyyar haɗaka ADC
  • Dauda Lawal ya jaddada cewa yana nan daram a jam'iyyarsa watau PDP kuma ba shi da wani shirin na barinta a halin yanzu
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa yana da kyakkyawar alaƙa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu duk da ba jam'iyyarsu ɗaya ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki ko haɗakar ADC.

Gwamnan ya jaddada cewa babu wani shiri da yake da shi na ficewa daga PDP, ko zuwa jam’iyyar APC ko kuma jam’iyyar ADC, wadda haɗakar ƴan adawa suka shiga.

Kara karanta wannan

Moro: Babban sanatan PDP a majalisa ya tsage gaskiya kan shiga hadaka

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin cewa yana shirin fita daga PDP Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Gwamna Lawal ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayani a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Laraba.

Gwamna Dauda Lawal na shirin barin PDP?

Ya ce labarin sauya shekar tasa da ake ta yaɗawa jita-jita ce kawai amma babu kanshin gaskiya a cikinta.

“Da farko, na ji daɗin yadda ka ce jita-jita ce cewa APC, ADC da sauran jam’iyyun siyasa suna kira na da na shiga jam’iyyarsu."
“Na bayyana a fili cewa ni mamba ne na PDP mai riƙe da katin zama ɗan jam’iyya, kuma har yanzu ina cikin PDP. Babu wani shiri da nake da shi na barin jam’iyyata.
“Don haka abin da kuka ji jita-jita ce kawai, amma har yanzu ina nan a PDP kuma babu inda nake shirin zuwa a halin yanzu.”

- Dauda Lawal.

Gwamnan Zamfara na fuskantar barazana?

Gwamnan ya ƙi amincewa da cewa yana fuskantar barazana daga bangaren adawa a jihar, yana mai cewa ba ya buƙatar komawa APC domin ya samu mafaka daga kowa.

Kara karanta wannan

ADC ta shiga Borno da karfinta, tana wawashe yan PDP da APC gabanin 2027

Ya bayyana cewa dukkan waɗanda ke tsagin adawa a halin yanzu a Zamfara, sune dai ƴan adawa tun zaɓen 2023, amma ba su iya hana shi zama gwamna ba a wancan lokaci.

Gwamna Lawal ya jaddada cewa ba ya jin tsoron manyan ‘yan adawa a jihar, irin su tsofaffin gwamnonin Zamfara, Sani Yerima da Bello Matawalle, yana mai cewa za ya sake doke su a zaɓen 2027.

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.
Gwamna Dauda Lawal ya ce yana da kyakkyawar alaƙa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Dauda Lawal na da alaƙa mai kyau da Tinubu

Ya amince cewa PDP na fama da rikici a cikin gida, amma ya bayyana cewa an riga an fara aiki domin warware matsalolin, kuma nan da wani lokaci za a shawo kansu, rahoton Vanguard.

Game da dangantakarsa da Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Lawal ya ce yana da kyakkyawar alaka da shugaban ƙasa, amma duk da haka suna cikin jam’iyyun adawa da juna.

ADC ta fara zawarcin Gwamna Dauda Lawal

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bayyana cewa ta ci gaba da karɓar masu sauya sheƙa daga jam'iyyu daban daban a jihar Zamfara.

Shugaban ADC, Kabiru Garba ya ce sama da mutum 100 daga jam’iyyu daban-daban ne suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar cikin kwana 10 da suka gabata.

Kabiru Garba ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ADC a shirye take ta karɓi Gwamna Dauda Lawal idan har ya yanke shawarar sauya sheƙa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262