Haɗakarsu Atiku Ta Kara Karfi, Jam'iyyar ADC Ta Yi Babban Kamu a Jihar Katsina
- Jam'iyyar haɗaka watau ADC na ci gaba da karɓar manyan jiga-jigai daga jam'iyyu daban-daban gabanin zaɓen 2027
- Tsohon shugaban PDP na jihar Katsina, Hon. Salisu Lawal Uli ya tattara kayansa ya koma jam'iyyar adawa ta ADC
- Ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne saboda tangal-tangal din da PDP ke yi tun 2022 ba tare da lalubo matsalar ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Katsina, Hon. Salisu Lawal Uli ya fice daga jam'iyyar tare da komawa ADC da ke ƙarƙashin ƙungiyar haɗaka.
Salisu Uli ya tabbatar da raba gari da PDP ne a wata wasiƙar sauya sheƙa da ya rattaɓa wa hannu mai ɗauke da kwanan watan 2 ga watan Yuli, 2025.

Source: Facebook
Ya bayyana salon shugabancin PDP mai cike da rikici da ruɗani a matsayin dalilin ficewarsa daga jam’iyyar, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Kara karanta wannan
Haɗakar su El Rufa'i ta yi babban kamu a Kaduna, Hon. Isah Ashiru ya gindaya sharadi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban PDP ya koma ADC
Ya zargi jam’iyyar da rashin gaskiya da ƙin ladabtar da masu laifi, yana mai cewa gazawar da take fuskanta alama ce da ke nuna cewa rugujewar PDP gaba ɗaya na gab da faruwa.
Hon. Salisu Uli ya ce:
"Alamu sun fara fitowa tun da wasu daga cikin mambobin jam’iyyar ke ganin kansu a matsayin masu ƙarfin da ba za a iya ladabtar da su ba, duk girman laifin da suka aikata."
Salisu Uli, wanda ya kasance ɗan PDP tun 1998, ya tabbatar wa magoya bayansa cewa zai ci gaba da ƙoƙarin cika burinsa na “ceto Najeriya da jihar Katsina” ƙarƙashin jam’iyyar ADC.
Tsohon shugaban PDP na Ƙatsina ya bayyana haɗakar ADC a matsayin “jam’iyya mai ɗabi’a, akida, da tsari, kuma abin dogaro.”
PDP ta rasa kusoshinta a jihar Katsina
Ficewar Salisu Uli na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da fuskantar rikice-rikice a cikin PDP ta jihar Katsina, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan
Hanyoyi 7 masu sauƙi da za ka shiga jam'iyyar haɗaka ADC ko wata jam'iyya a Najeriya
A baya-bayan nan, wata ƙungiya da ke biyayya ga tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Dr. Mustapha Inuwa, ta fice daga jam’iyyar PDP.

Source: Twitter
Wannan rukunin ya haɗa da ’yan takara da masu neman tsayawa takara 287 daga matakin Majalisar Dokoki, Shugabannin Kananan Hukumomi, da Kansiloli.
Shugaban ƙungiyar masu neman kujerar shugabancin ƙananan hukumomi, Alhaji Yasir Ibrahim, ya ce cin amanar juna da ruɗu a cikin jam’iyyar ne ya tilasta musu ficewa daga PDP.
“PDP ba ta kai matsayin jam’iyyar adawa a jihar Katsina ba a halin yanzu. Don haka muka yanke shawarar shiga cikin hadakar jam’iyyun adawa domin gina adawa,” in ji shi.
Tsohon shugaban kwamitin sulhu ya bar PDP
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kwamitin sulhu na PDP a jihar Gombez AVM Shehu Adamu Fura ya koma ADC.
AVM Shehu ya sanar da ficewarsa daga babbar jam'iyyar adawa watau PDP tare da komawa jam'iyyar haɗaka domin kifar da gwamnatin APC a zaɓen 2027.
Tsohon sojan Saman Najeriya ya bayyana cewa matakin da ya dauka ya biyo bayan tattaunawa da nazari mai zurfi da ya yi game da makomarsa ta siyasa.
Asali: Legit.ng