ADC Ta Gano Shirin Gwamnatin Tinubu na Ruguza Hadakar 'Yan Adawa a Jihohi

ADC Ta Gano Shirin Gwamnatin Tinubu na Ruguza Hadakar 'Yan Adawa a Jihohi

  • Jam’iyyar ADC ta ce gwamnatin Bola Tinubu na kokarin rushe hadakar jam’iyyun adawa ta hanyar jan hankalin shugabanninta na jihohi
  • Jam’iyyar ta bayyana cewa ana kiran shugabannin yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma zuwa taron sirri da jami’an gwamnati
  • Rahotanni sun bayyana cewa ADC ta ce wannan yunkuri na nuna shiri ne na kirkirar mulkin jam’iyya daya da hana adawa tasiri a kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da kitsa wani mummunan yunkuri na karya karfin hadakar 'yan adawa da ke kara karbuwa a fadin kasar.

ADC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinta na rikon kwarya kuma mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin, 8 ga Yuli, 2025.

Kara karanta wannan

ADC: Buba Galadima ya fadi dalilin Kwankwaso da NNPP na kin shiga hadaka

ADC ta zargi APC da kokarin rusa 'yan adawa.
ADC ta zargi APC da kokarin rusa 'yan adawa. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Business Day ta wallafa cewa sanarwar ta ce gwamnati ta gayyaci wasu tsofaffin shugabannin jam’iyyar da mambobin kwamitin jihohi a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC ta ce gwamnati na kokarin hana adawa

A cewar jam’iyyar, taron da ake shirin yi ba don batun tsaro ko zaman lafiya ba ne, illa dai yunkurin firgitarwa da jan hankalin shugabanni su janye daga goyon bayan hadaka.

Daily Post ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya ce:

“Mun samu sahihin bayanin sirri cewa makasudin wannan ganawa shi ne a janye wasu daga cikin shugabanninmu daga tafiyar hadaka da muradin rushe sabon tsarin shugabancin jam’iyya,”

An zargi Tinubu da son kafa jam’iyya 1

Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa abin da ke faruwa tamkar kafa mulkin jam’iyya daya ne, inda gwamnati ke amfani da jami’anta wajen takura jam’iyyun adawa.

Jam'iyyar ADC ta ce makasudin hakan shi ne a haifar da rikici a cikinta, a rage karfin sababbin shugabanni da kuma hana ci gaban da take samu a matsayin sabuwar kafar adawa.

Kara karanta wannan

ADC ta yi martani ga fadar shugaban kasa, ta ce ta gama gigita APC

Hankalin Tinubu ya tashi inji ADC

Bolaji ya bayyana cewa nasarar da jam’iyyar ta samu a hadakar da ta kaddamar a ranar 1 da 2 ga Yuli ta sa gwamnatin APC ta shiga tashin hankali.

A cewarsa, gwamnatin Tinubu ba za ta iya jure hadakar adawa mai karfi ba, don haka ta koma yin amfani da tsohuwar dabararta ta rusa jam’iyyun hamayya.

ADC ta bukaci Tinubu ya ja kunnen mukarabbansa kan shiga harkar 'yan adawa
ADC ta bukaci Tinubu ya ja kunnen mukarrabbansa kan shiga harkar 'yan adawa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jam’iyyar ta bukaci shugaban kasa Tinubu da ya ja kunnen mukarrabansa da su daina shiga harkokin da ke barazana ga adawa a kasar.

Rarara ya ce zai kayar da ADC a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa mawakin jam'iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara ya yi tir da kokarin 'yan adawa na yin hadaka a ADC.

Mawakin ya ce ya kamata 'yan adawa su marawa Bola Tinubu baya ne maimakon kafa sabuwar kafar hamayya da shi.

Rarara ya gargadi 'yan adawan da cewa ko shi ma zai gama da su idan ya fito takara a 2027 balle kuma Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng