Abu Ya Girma: Jiga Jigai 3 Sun Nemi Ruguza Haɗaƙar Atiku, Obi da Ƴan Haɗaka a ADC

Abu Ya Girma: Jiga Jigai 3 Sun Nemi Ruguza Haɗaƙar Atiku, Obi da Ƴan Haɗaka a ADC

  • Ƴan ADC uku sun maka jam'iyyar a gaban kotu kan naɗa shugaba, sakatare da mai magana da yawun jam'iyyar na rikon kwarya
  • An naɗa David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren ADC na rikon kwarya bayan jagororin adawa sun yi haɗaka a jam'iyyar
  • Sai dai wasu daga cikin mambobin ADC na ganin hakan ya saɓa wa tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyyar na 2018 da aka yi wa garambawul

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC uku sun kai ƙara gaban kotu, suna ƙalubalantar shugabannin rikon ƙwarya da aka naɗa karkashin jagorancin David Mark.

Ƴan jam'iyyar ADC sun garzaya gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda suka nemi a rushe shugabancin rikon kwarya na da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus

David Mark da Rauf Aregbesola.
Mutum 3 sun kai karar shugabannin ADC na rikon kwarya gaban babbar kotun tarayya Hoto: @SenDavidMark, Rauf Aregbesola
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Adeyemi Emmanuel, Ayodeji Victor Tolu, da Haruna Ismaila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da jiga-jigan suka kai ƙara kotu

Sun kalubalanci waɗanda aka nada a matsayin shugabannin rikon kwarya, musamman David Mark, Rauf Aregbesola da Bolaji Abdullahi.

Sun roƙi kotu da ta fayyace ko mika shugabancin jam’iyyar ga wasu da ke shirin ƙulla ƙawancen adawa ya yi daidai ko saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC.

A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1328, masu kara sun ambaci ADC a wacce ake ƙara ta ɗaya, INEC ta biyu, sai kuma tsohon shugaban ADC na ƙasa, Raph Nwosu, na 3.

Sanata David Mark, wanda aka nada a matsayin shugaban ADC na riko, tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola (sakataren riko), sune waɗanda ake ƙara na huɗu da na biyar.

Sai kuma wanda ake ƙara na shida, tsohon Ministan wasanni, Bolaji Abdullahi wanda aka naɗa a matsayin sakataren yaɗa labarai na rikon kwarya a ADC.

Kara karanta wannan

Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya

Jam'iyyar ADC ta fara gamuwa da cikas.
Mutum 3 sun ƙalubalancin shugabancin David Mark na ADC a gaban kotu Hoto: @ADCnCoalation
Source: Twitter

ADC: Abin da masu ƙara suna nema a kotu

Masu ƙarar sun gabatar da tambayoyi na shari’a don kotu ta tantance, ciki har da:

"Ko nadin waɗanda ake ƙara na 4, 5 da na 6 a matsayin shugabannin riko ya sabawa tanadin Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyar ADC na 2018 (da aka gyara)."
"Ko, bisa tanadin Sashe na 9, sakin layi D na kundin tsarin mulkin jam’iyyar ADC na 2018 (da aka gyara), waɗanda ake ƙara na 4, 5 da 6 sun cancanci rike mukaman da aka basu."

Bayan haka, sun buƙaci kotun ta yan hukuncin cewa:

"Nadin shugabannin rikon kwarya a jam’iyyar ADC ya karya doka kuma ya sabawa tsarin mulki, bai halatta ba, don haka a soke shi."
"Nadin waɗanda ake tuguma na 4, 5 da 6 ya saba da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar ADC na 2018 (da aka gyara)."

Har yanzu dai babba rkotun tarayya ba ta sa ranar da za a fara sauraron shari’ar ba, rahoton Daily Vanguard.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 7 masu sauƙi da za ka shiga jam'iyyar haɗaka ADC ko wata jam'iyya a Najeriya

Abin da ka iya rusa tafiyar ADC kafin 2027

A wani rahoton, kun ji cewa ana hasashen akwai abin zai iya tarwatsa haɗakar ƴan adawa a ADC tun kafin babban zaben 2027 da ke tafe.

Atiku Abubakar, Peter Obi da Rotimi Amaechi, sune sahun gaba a jerin waɗanda kom haɗakar ta ba su tikitin takarar shugaban ƙasa.

Babban ƙalubalen ADC shi ne yadda za ta tsaida wanda ya fi cancanta kuma daga wane yanki ya kamata ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262