2027: Jam'iyyar Haɗaka ADC Ta Tono Tarihin da Ka Iya Hana Tinubu Zama Shugaban Ƙasa
- Jam'iyyar ADC ta nuna damuwa kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke kokarin riguza ƴan adawa a Najeriya
- ADC ta tunawa Bola Tinubu muhimmanci tsarin dimokuraɗiyya, tana mai cewa da Jonathan ya danne adawa, da APC ba ta karɓi mulki a 2015 ba
- Mai magana da yawun ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi ya ce alamu sun nuna gwamnatin APC ta fara tsorata da haɗakar ƴan adawa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jam’iyyar haɗaka watau ADC ta gargadi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta daina ƙoƙarin ruguza jam’iyyun adawa a Najeriya.
ADC ta bayyana cewa shi kansa shugaban ƙasa ya ci moriyar tsari na dimokuraɗiyya a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.

Source: UGC
ADC ta gargaɗi gwamnatin Bola Tinubu
A rahoton da Daily Trust ta wallafa, ADC ta ce da Jonathan ya ruguza adawa tun a mulkinsa, da yanzu ba Tinubu ba ne a kujerar shugabancin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar ADC, abubuwan da wasu daga cikin jami’an gwamnatin Tinubu ke yi kwanan nan na nuna alamar yunkurin kassara adawa, wanda hakan barazana ce ga demokuraɗiyya.
ADC ta bukaci Shugaba Tinubu da ya nuna gogewa a shugabanci na gari ta hanyar takaita irin cin karen da wasu hadimansa ke yi da girmamawa ga ra’ayoyin jama'a.
An tunawa Tinubu abin da Jonathan ya yi
“Dole ne shugaban ƙasa ya tabbatar da cewa shi ɗan dimokuraɗiyya ne na gaske ba na surutu ba.
"Ya kamata ya tunatar da mukarrabansa cewa da gwamnatin Jonathan ta yi irin haka, da APC ba ta karɓi mulki a 2015 ba, kuma shi kansa ba zai zama shugaban ƙasa ba ba a yanzu," in ji ADC.
Hakan dai na cikin wata sanarwa da Mallam Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam’iyyar ADC na rikon kwarya ya fitar a ranar Litinin.
Yadda ADC ta gano makircin gwamnatin APC

Kara karanta wannan
Hanyoyi 7 masu sauƙi da za ka shiga jam'iyyar haɗaka ADC ko wata jam'iyya a Najeriya
Ya zargi cewa an gayyaci wasu tsoffin shugabannin ADC daga yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma zuwa taron sirri da jami’an gwamnatin tarayya.
Bolaji Abdullahi ya ce an kitsa wannan ne don raba kawunana ƴaƴan ADC, ruguza shugabancin haɗaka, da daƙile duk wani shirin ƴan adawa, inji Vanguard.

Source: Twitter
Ya danganta wannan lamarin da tsoron haɗakar shugabannin adawa a Najeriya da jam’iyyar ADC ke jagoranta, wadda ya ce ta girgiza jam’iyyar da ke mulki.
"Yanzu ya bayyana a fili cewa gwamnatin Tinubu, bayan ta rasa amincewar jama’a, ba za ta iya fuskantar haɗakar adawa mai inganci ba.
"Maimakon magance matsalolin ƙasa, sun koma amfani da tsohuwar dabara ta kawo cikas ga abokan hamayya,” in ji sanarwar.
Shafin yanar gizon ADC ya ɗauke sau 3
A wani rahoton, kun ji cewa shafin yanar gizon ADC ya fuskanci matsala sau uku sakamakon yawan masu shiga domin yin rajistar zama sababbin mambobi.
Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT), Ibrahim Mani, ne ya bayyana hakan, ya ce ƴan Najeriya daga sassan Nsjeriya na tururuwar shiga ADC.
Ibrahim Mani ya jaddada kudurin jam’iyyar na gina babban dandalin ’yan adawa a kasar, tare da karbar sababbin mambobi da suka dace da manufofin ADC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
