Kwankwaso Ya Cancanta? NNPP Ta Jero irin Mutanen da Ya Kamata Ƴan Najeriya Su Zaɓa a 2027
- Jam'iyyar NNPP reshen Kudu maso Yamma ta bukaci ƴan Najeriya su guji sake aminta da waɗanda suka gaza cika alƙawurran da suka ɗauka
- Shugaban NNPP na yankin, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo ya ce lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su yi watsi da ƴan siyasar da suka ci amanarsu
- Oguntoyinbo ya kuma caccaki jam'iyyar APC mai mulki, yana mai cewa maimakom ceto Najeriya, ta sake jefa al'umma ne a cikin wahala
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jam'iyyar adawa ta NNPP ta shawarci ƴan Najeriya da su saka kowane ɗan siyasa ko jam'iyya a sikelin alkawurran da suka dauka kafin sake zaɓensu a 2027.
NNPP ta gargaɗi mutane kasar nan da su kauracewa zaɓen duk wata jam'iyya ko ɗan siyasar da ya gaza cika alkawurran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.

Kara karanta wannan
"Ku yarda da ni": Obi ya fara lallaɓa ƴan Arewa, yana neman ƙuri'un doke Tinubu a 2027

Source: Twitter
Shugaban NNPP na Kudu maso Yamma, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanne irin mutane ya dace a zaɓa a 2027?
Mista Ajadi ya jaddada muhimmancin tantance alkawurran da jam’iyyu suka yi kafin sake mara masu baya a babban zaɓe na 2027.
Ya bukaci masu kada kuri’a da su yi nazari a kan abin da jam’iyyun suka aiwatar cikin shekaru biyu da suka wuce kafin su yanke shawarar wanda za su zaba.
Babban jigon NNPP ya ƙara da cewa halin da ƙasar nan ke ciki na nuna yadda shugabanni ke karya alkawurra, inda yawancin jama’a ke fuskantar ƙarin wahala.
Jam'iyyar NNPP ta caccaki gwamnatin APC
Ajadi ya caccaki jam’iyya mai mulki ta APC bisa gazawarta wajen cika alkawurran da ta ɗauka lokacin kamfe.
“Duk da cewa APC ta yi alkawarin kyautata rayuwar talakawa, gaskiyar ita ce mutane da dama sun koma bara domin su rayu.” in ji shi.

Kara karanta wannan
Haɗakar su El Rufa'i ta yi babban kamu a Kaduna, Hon. Isah Ashiru ya gindaya sharadi
Ya shawarci jama’a da su yi amfani da basira da hangen nesa wajen tantance abin da jam’iyyu da wakilan da suka aikata kafin su yanke shawarar wanda za su zaba a 2027.
A rahoton Tribune Nigeria, Ajadi ya ce:
“Jam’iyyun siyasa sun yi alkawarin inganta rayuwar ‘yan Najeriya, amma abin da suka yi cikin shekaru biyu da suka wuce shi ne ƙara wa mutane wahala."

Source: Twitter
NNPP ta zargi APC da yaudarar ƴan Najeriya
Ya nuna yadda tsarin “Renewed Hope Agenda” na APC ya ja hankalin jama’a, amma sakamakon haka, rayuwar talakawa ta kara tabarbarewa.
Da NNPP ta ke kuka da matsalolin tattalin arziki, ta bayyana cewa albashin ma'aikata bai zuwa ko ina a karkashin mulkin APC mai-ci.
“APC ta yi ikirarin za ta inganta rayuwar talakawa, amma abin da ta yi shi ne ta ƙara musu raɗaɗi, albashin ma’aikata ba ya iya biya masu buƙatun rayuwa na yau da kullum.”
Kwankwaso na shirin komawa APC?
A baya, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta reshen jihar Kano ta karyata rahoton da ke yawo cewa Rabiu Kwankwaso na shirin sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Kara karanta wannan
Hanyoyi 7 masu sauƙi da za ka shiga jam'iyyar haɗaka ADC ko wata jam'iyya a Najeriya
Shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Kano, Hashimu Dugunrawa, ya ce babu wani shiri da jagoransu ke yi na haɗewa da APC don zama abokin takarar Bola Tinubu.
Dugunrawa ya tunatar da cewa Kwankwaso abokin Shugaba Tinubu ne tun da daɗewa, musamman lokacin da suke gwamnoni daga 1999 zuwa 2003.
Asali: Legit.ng