Tuna Baya: Abin da Ya Rusa Haɗakar Obasanjo a ADC domin Yakar Buhari a 2019
- A shekarar 2018, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya jagoranci kafa hadaka da nufin kawo sauyi a kasa
- Hadakar ta rungumi jam’iyyar ADC a matsayin dandalin siyasa wanda ke kokarin kwace mulki a hannun Muhammadu Buhari
- Bayan watanni uku, CNM ta rabu da ADC saboda rashin fahimta kan hadin gwiwa da CUPP wanda ya jawo rikici da rabuwar kai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Yayin da yan adawa suka rungumi ADC domin kifar da gwamnatin Bola Tinubu, wannan ba shi ne karon farko ba.
A watan Mayun 2018, an kafa kawancen siyasa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kirkiro ta rungumi jam'iyyar ADC.

Source: Twitter
2019: Hadakar da Obasanjo ya shirya domin doke Buhari
Jaridar TheCable ta ce an yi hakan ne domin kalubalantar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar da Obasanjo ya jagoranta 'Coalition of Nigeria Movement (CNM)' ta bayyana ADC a matsayin jam’iyyar adawa ga Buhari.
Daga cikin mahalarta taron sun hada da Obasanjo, Olagunsoye Oyinlola, wanda shi ne mai daukar nauyin kungiyar kuma tsohon gwamnan jihar Osun da wasu ‘yan siyasa.
Obasanjo ya gabatar da CNM a matsayin wata kafa maras bangaranci da za ta “kubutar” da Najeriya daga wahalhalun da gwamnatin Buhari ta jawo.
Ya ce kungiyar ta rungumi ADC ne don samar da sauyin da ake bukata a siyasar Najeriya da shugabanci, cewar Premium Times.
Tsohon shugaban ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ba ta da alaka da “halin baya na PDP” da kuma “mummunan tafiyar APC.”
"Zan fara da taya murna da jinjina ga farfadowar jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, a matsayin jam’iyyar siyasa.
"Tun bayan kafuwar CNM, jam’iyyu 68 sun tuntubi kungiyar kan yadda za a hada kai da aiki tare.
"Shugabannin kungiyar, bayan tantancewa da shawarwari masu zurfi da la’akari da manufofin kungiyar, sun amince da rungumar ADC don kawo sauyi."
- Cewar Obasanjo

Source: Twitter
Tsawon lokaci da hadakar Obasanjo ta dauka
Haka kuma, Oyinlola ya ce shigar su cikin ADC ya nuna godiya ga cigaban siyasar jam’iyyar da zaman lafiyar ta a harkokin siyasar Najeriya.
Tsohon gwamnan ya ce 'yan Najeriya su sa ran karin abubuwa daga kungiyar, yana kiran hadewar da suka yi da ADC a matsayin “mataki na farko.”
Amma hadewar ADC da CNM ba ta yi wani tasiri ba inda ta dore na wata uku kacal.
A watan Agusta 2018, wani bangare na CNM ya fice daga ADC ya kafa sabuwar jam’iyya mai suna New African Democratic Congress (N-ADC).
A watan Yuli 2018, ADC ta shiga kawance da jam’iyyu 36 ciki har da R-APC da PDP don kafa CUPP.
Jam’iyyun sun rattaba hannu kan yarjejeniya domin takarar zaben 2019 karkashin dandalin hadin gwiwa.
Fadar shugaban kasa ta soki masu hadaka
Mun ba ku labarin cewa fadar shugaban kasa ta caccaki masu shirin hadaka domin kwace mulkin Bola Tinubu.
Hadimin Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya ce wasu daga cikin ‘yan ADC na yanzu sun bar APC tun tuni.
Ya zargi Rauf Aregbesola, Hadi Sirika, Abubakar Malami da Rotimi Amaechi da zama marasa biyayya ga APC tun tuni.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


